Bakar Ayah Book 2 Page 5-6
Page 🖤5••6🖤
“Wai luby lafiyah kika tasoni da safennan wai zaki koma gidannan,haba bansanki da wannan,wannan ba girmanki bane mana big elegant woman”
“Kimin shuru Yaseerah eh haka naga dama,komawa zanyi,dama ai bashi ya koreni ba nice dakaina na taho”
“Kutt wannan yajin fah ko sati bakiyi ba shine zaki koma,naga wani lokacin har wata kinayi a gida,ko kai dagaske dan kina tsoron wannan matar ne kada ta mallakemiki miji”
“Kaii wai Yaseerah da wanne zanji ne,dake koda mijina,ko kuma da mommy tada koroni iye,koma mai zai faru kekam ki zuba ido mana kigani,inda tani ce da tuni na kasheta tun kafin ta shigo cikin gidana”
“To meyasa kika fasa hakan”
“Mommy ce ta hanani mana,a cewarta sunyi hakanne domin na kasheta su sakani cikin tarko,idan inaso na kawar da ita saidai na yi amfani da kissa da kuma aiki a boye,wanda ba kowa zai kulada abinda na aikata ba,kaman haÉ—ata da wani ciwo,saka mata wari ko kuma saka wa Jabeer tsanarta,ke yanda nakeji ma koda ban kasheta da asiri ba zan yi hayar Æ´an fashi wanda zasu shigo suyimin daga daga da ita…..”
Tana maganar ne numfashinta yana cikowa saboda tarin baƙin ciki da tsanar amaryar mijinnata da take cinta.
“Kinga ki kwantar da hankalinki haka mana luby,batun kawar da ita wannan dolene,tunda har tayi nasarar shiga rayuwarki,bazamu taba barta ba,yanzu dai mu shiga gidan muga sabon part É—in daza’a kaita,nasan wannan tsohuwartata ce tayi hakan saboda tana tsoron abinda zakiyi mata.”
“Nasan dama shine dalilin,sannan a cikin wajen a kwai part din dayafi girma,yaÉ—an shiga cikin lambun gidan,sannan yana É—an nesa da sauran parts É—in,kaman anyishine domin babbar matar dazata zauna a wajen,wanda nce kenan mamallakiyarsa”
“To yanzu idan mukaje kuma taÉ—auki wannan part É—in fah,ya zamuyi mata kenan”
“Hhhhh har tambaya kike ma mai zanyi mata,kaff gidannan banga mai sakani barta ta zauna a wannan wajen ba,da banyi niyyar zama a wajen ba,amma tunda naga tace anan amaryarsa zata zauna,nima a can zan zauna,kuma wannan part É—in nakeso”
Ƙarisa maganar tayi cikeda shirin abinda zata aiwatar idan ta shiga cikin gidan.
Daidai isowarta ƙofar gidan,wanda take da tabbacin shine gidan da take nema,saboda nan Gps ɗin motarta ya nuna.
Kashe Æ™arar motarta tayi tana kallon get na shiga estate É—in. Ko ba’a faÉ—awa mutum ba daga ganin mashigar zai tabbatar da cewa wajene babba kuma Æ™awatacce sosai.
Ƙara horn ɗin da ake mata da motane yasaka ta ɗauke kanta daga kallon mashigar ta maidashi kan motar dake gabanta.
Farar mota ce mai kyau tashiga taro ta faso kai ta shigo wajen,har Bombee tayi niyyar jan motarta baya domin bata damar shigewa,saikuma taji ana ta jera horn akallah kusan biyar,tun ma kafin ta motsa motar tata.
Komawa tayi ta zauna shuru ta zubawa motar gabannata ido,batareda tasake motsawa ba,jira take taga wanne shafaffe da mai ne yake tunanin zata yimasa abinda yake so ta ƙarfi.
Bayan kaman a ƙalla minti biyar,wanda zuwa sannan lubna tayi horn yafi sau a ƙirga,jan tsuka tayi tareda bugar sitiyarin motar da hannunta,idanuwanta har sunyi ja dan baƙinciki.
“Wai wannne É—an***** ya taremin hanyar shiga ne,waye mai kuma yake taÆ™ama dashi”
“Inaga saidai É—an gidann mana,abin da rainin hankali kam a ciki,amma bari naje na duba”
“Ahah yi zamanki basai kinje ba,daga gani baÉ—an gidan bane,domin bansan mai irin Æ™irar motar nan ba”
“Ahh a yanda suke kam ko jiya zasu iya order sabuwar mota,kokuma Abdulkareem ne kai ya dawo?”
“Ba Abdulkareem ba inma Abdullahi ne dakansa bazan É—auki wannan rashin mutuncin ba,yaushe har lagona ya karye suke wannan wasan dani”
A zuciye lubna tafito daga motarta ta tunkari inda Bombee take zaune a cikin tata motar.”
Kwantar da sit ɗin drivern tayi tareda yin miƙa,lokacin da taga lubna ta tunkaro inda take,dama jira take daga wanene a cikin motar da har zai mata waɗannan horn ɗin kaman ya samu dabba akan hanya.
“Ohh dama kece mai yimin horn É—in mrs Jabeer? Banyi tsammanin haÉ—uwar mu yanzu ba,wow very interesting and nice meet”
Bombee tafaÉ—a cikeda nishaÉ—i kana ta karisa maganar da hamma.
Ƙwanƙwasa glass ɗin kusada ita taji lubna tayi,nan ma saida tayi shan ƙamshi na ɗan wani lokacin kafin kafin ta sauƙe glass na motar.
In ana magana takaici ranar Lubnah ta shaƙa,da taga macece ma cikin motar,kuma dan iya shege a kwance ma take batada niyyar tada motar,wato ƙalau motar ma take da gangan taƙi tayar da ita ta matsa mata.
“Wacece keee!?”
Lubnah ta faɗa tanayiwa Bombee kallon ƙasa da sama,wacce idon yake rufe kaman bada ita take ba,inda bata buɗe mata glass ba sai tayi tsammanin bacci take,ji take kaman ta saka hannuwanta ta cakumo wuyanta tacikin motar.
“Mai kike taÆ™ama dashi da har ina miki magana kina ji iyee,waye ubanki cikin garinnan,koma menene alaÆ™arki da gidannan bai dameni ba,amma ki sani ko Æ´an gidan nafi Æ™arfin su rainamin hankali ballantana kuma keh”
A kasalance Bombee ta buɗe idonta tajuyo ta kalli Lubnah,a yanayin data juyo cikeda jan magana,sai ya ƙara fito da ainihin Kyawunta.
Gaban Lubnah ne ya buga datayi arba da fuskarta,sai taga kaman ta taba ganin mai kama da ita,amma ina ga kamace,ta faÉ—a a ranta.
“Ku mutane kunada damuwa,dole saini Æ´ar wanice kafin zanyi abinda naga dama,akwai wanda aka hanashi motsi yanda yake sone,to meyasa sai Æ´an wanene zasuyi yanda sukeso,sha kuruminki ni ba Æ´ar kowa bace,amma tunda kikayimin horn fiyeda É—aya kafin na matsamiki,to a lokacin na yanke hukuncin sai kinyi minti talatin kina tsaye kafin ki shiga gidannan,in kinga na matsa a wajennan to lokacin dana yanka ne ya cika,ko kuma mota mai haÆ™ora kika É—auko ta dauÆ™e motata,amma idan biyunnan wani bai faruba,tsayuwar banza kikeyi a wajenann,dan abinda kike bazai sakani sanja ra’ayina ba,gwanda ma ki koma motarki ki zauna”
Bombee tana kaiwa nan ta bayaninta ta maida glass É—in motarta ta rufe.
Wata jijjiga Lubnah tayi,tama rasa mai yake mata daɗi,wai wannan yarinyar ce take mata magana haka,tukunna ma wajen wa tazo a cikin estate ɗin,yanayinta ne yasa tayi tunanin wataƙila baƙuwar Lylah ce,sai kuma wata zuciyar tace ta ƙira securtyn gidan.
Allah sarki bawan Allah,chiep securityn yana É—agawa lubna tafara balbaleshi da masifah,ta inda take shiga bata nan take fitaba.
“Uban me kukeyi,menene ma aikinku a gidannan,maza kazo da kanka ka gani,wata banza ta hanani shigowa ciki,da saka motarta a bakin Æ™ofa,kuzo kuyimin waje da ita”
“Ranki ya daÉ—e kiyi haÆ™uri bari muduba CCTV camera,inaga kuma wajen wani tazo a cikin gidan,kada muyi mata magana yazama matsala”
“Matsala… Ina ruwana da wajen wa taxo tunda ta nuna min ta isa dan tasamu shiga wajennan sai tasan matsayinta yanzunnan,ku zaba shin fitar da ita daga baÆ™in Æ™ofar nan ko kuma Aikinku?”
Ai tun kafin Lubnah tasake cewa wani abun yayi saurin cewa.
“Aikina na É—auka Hajiya,gani nan zuwa dakaina yanzunnan basai anjima ba”
Kashe wayar tayi tana jiran isowar tasu kaman yanda suka faÉ—a.
Yaseerah ce ta fito itama daga motar tazo inda lubna ke tsaye tana jijjiga kaman an jona mata wutar lantarki.
“Ƙawass mai yafarune,waye a cikin motar ko baci tayi?”
Duk maganar datake Lubnah bata kulata ba,har sannan tana sama,ƙarar fitowar motar securityn ta jiyo,saidai suma bayadda zasuyi su fito,dan Bombee ta tare hanyar fitowar daga waje.
Sagern Hudu ne ya fito daga motar,wanda shine shugaban security na estate ɗin gaba dayah,wajen motar Bombee ya nufah tareda ƙwanƙwasa mata ƙofah.
Zugewa tayi tareda haÉ—e fuska tace,
“Wai menene kuka dameni,idan kukayi haÆ™uri ma minti talatin na cika zan matsar da motata,basai kun takurawa rayuwata ba”
Kallon mamaki ya bita dashi tareda cewa.
“Kee wacece ke,shin tukunna ma mai kikazoyi gidanann,danni ban taba ganin mai kamarki ba a wajennan”
“Kai kai wai duk gidannan haka kuke ne,kowa inzai buÉ—i baki wacece ke,dole saini watace zanyi haka,kenan ban isa É—aukar mataki ba idan akayimin wani abun?”
Tsawa Lubnah ta dakawa sagern hudu daga inda take tsaye,
“Lallabata ma kakeyi,yanzunnan kuyi waje da itah,ko tsoronta kukeji kai”
Sagern hudu yanajin maganar Lubnah ya ƙara ƙaimi tareda ficcina ƙananun idanunsu.
“Kinga madam koma me kike takama dashi ki fito daga motar nan yanzunnan,a matsar da motar”
“A kuda kuke so na matsar da mota meyasa kuma zan fito?”
“Ahhh wannan kuma madam daga baya kenan,dole zaki fito ki faÉ—amana menene dalilinki na zuwa nan wajen”
Shuru Bombee tayi bata bashi amsa ba,daidai lokacin da ta ƙayyade suna cika taga hannun sagern hudu yana shirin cakumo kirjinta,cikin zafin hannu ta riƙe a hannunsa tareda yimasa kallo mai ɗauke da alamar tambaya.
Idonsa tagani yana kallon kan ƙirjinta,tashi daya ta gane ba iyah niyyar fitowa yake da ita daga motar ba,harda wani mungun nufinnasa ma.
Yatsun hannunsa guda biyu na ƙarshe ta rike ta malƙwasa,nan da nan yabada ƙarar ƙass ta ƙaryasu.
Ƙarar azaba ya saka tareda fizge hannunsa yaja gefe yana kallonta cikeda mamakin karfin dayaji ta saka masa.
Key tayiwa motar ta bata diri,hanyar get É—in ta nufah inda sauran securityn suke tsaye,nufarsu tayi da niyyar bi takansu ta shiga gidan.
Da farko basuyi tunanin zata cigaba da tafiya ba duk da sun tsayah….amma ganin tsakaninsu baifi taki É—aya ba,kuma bata da niyyar tsayawa yasaka su bajewa da gudu,É—aya kam har yatsansa t taka na Æ™afah.
Tsalle yafara ya ihu tareda bin motar tata da kallo,wanda har ta bace a cikin gidan.
Saida ta ƙule tukunna sagern hudu ya juyar da kallonsa ga Lubnah,wacce itama tatsayah tana kallon abinda Bombee tayi.
Hannunsa yasake É—unlewa tareda cewa.
“Hajiya kiyi haÆ™uri bari mushiga cikin muga wajen wa tazo,karki damu yanzu zamu koreta”
Bai tsaya jin abinda zatace ba yashiga motarsu suka shiga cikim gidan.
Itama Lubnah ganin cizon yatsa bazai kaita ya sakata shiga tata motar itada yaseerah suka bi bayansu.
A bangaren Bombee kuwa hankali kwance take tafiyah akan titin dake cikin estate din,har ta isa ga bakin part É—in su Hajiya zeenah,dan shine a farko daga an shigo da kuma na su Lylah daga ciki kaÉ—an.
Parking motarta tayi a wajen da taga wasu motoci,wayarta tafitar tareda dannna sunan Hilyaan.
Ringing biyu da daga tareda yimata sallama daga É—aya bangaren.
“Kinga babu bata lokaci sonake na kwantar da yaronnan,ya gaji da kwanciyar mota ga bayanin daÉ—i,ki fito ki nunamin part É—in dazan zauna,ko kimin kwantance idan wani abu kike,zan wuce daga nan”
“Lahh anty maryam harkin shigo wai,kina ina kenan a cikin gidan?”
“Uhmm ina bakin wani part wanda shine na farko idan aka shigo ciki”
“Ohh part É—in Hajiya zeenah kenan,muna ciki ai barina sanar mata da isowarki,mijinnaki ma yana wajenta yanzu ya shigo gaishe da ita”
“Kinga ni Hilyaan bana son wannan maganganun wanda naga kin koya tun zuwanki wajennan,inma wani abun suka baki kika sauya ni bai dameni ba,kawai ki fito ki nunamin masauÆ™ina inason na huta,badan hotel É—in dana sauka ana event a wajen ba maizai fitar dani da safennan kamar na ciwa wani bashi?”
“Sorry sorry Ogah ganinan fitowa yanzu nan karki damu”
Bayan kashe wayar Bombee a ƙalla tayi tsuka sunfi uku,ƙarar motoci taji sun faka a kusada ita,sa alama mutanen ta ne na bakin get suka iso.
Tana kallonsu dukkansu suka fito daga motar,shikam sagern hudu har sharce yake,saboda azabar data haushi na gurÉ—iyar yatsunsa guda biyu.
Fitowa itama tayi daga cikin motar tana kallon Lubnah wacce take tsaye tana zabga mata harara kaman zata cinyeta da ido.
“Ohh wato ke baÆ™uwar matar nan ce,no wonder kikejin haushina duk da bansanki ba mana”
Lubnah tafaÉ—a tareda yin murmushin gefen baki .
“Amma kaman banice dajin haushinki ba,ina fah kece kika dau da zafi daga farko,kuma har yanzu ma kinanan dajin haushinnawa,shin bakya ganin kallon da idanuwanki suke yiminne madam luban,ko aikamin kallon suke batareda izininki ba kai……..ohhh kuma akan kawai na hanaki shigowa ciki sai lokacin dana shata sun cika,abin burgewar kuma saida suka cika kika shigo É—in,common Æ™aramar dokata kin kasa karyawa inaga babba kuma…….chchchchchc am feel sorry for you”
Bombee tafaÉ—a cikeda sigar zolayah,harda wani cuna baki kaman na kifi,hakan datayi ne lokacin É—aya mutum zai dauka innocent ce.
“Sannunki da isowa”
Hilyaan tafaÉ—a fuskarta É—auke da fara’a lokacin da suka iso wajen da take itada khamees.
Daga kai Bombee tayi wa Hilyaan kafin ta kalli khamees cikin kame fuska,kaman ba ita ke zolayar Lubnah yanzu ba.
“Barka da isowa yakk ya hanya”
Khamees ya faÉ—a cikin girmamawa,murmushi Bombee tayi masa tareda cewa.
“Hanya normal ne kasan dawar,ykk hope komai ya tafi normal koh?”
“Yeah komai kalau,amma nayi mamakin isowarki da safe haka”
Wani rolling manyan idanuwanta tayi,wanda hakan yasake bawa ƙwayar idanuwant show up,kafin tace.
“Jiya na shigo garin,so na tsayane a hotel badan hayaniyar dasuke yahanani sakewa ba,da bazan shigo yanzu na sai yamma”
Hajiya zeenah ce dake tsaye tayi magana cikin dan É—aga murya yanda kowa zaijita a wajen,harda su Bombee da suke magana itada mutanenta.
“Toh amaryarce ta shigo da wuri haka,hala a gari kika kwana amma?”
Tsayawa tayi da maganar da suke da khamees ta ƙarisa inda Hajiya zeenah ke tsaye itada su Madeenah,harda Jabeer wanda ke tsaye a gefe kaɗan yana waya,saidai duk abinda ake akan idonsa a wajen.
Doguwar rigace baka a jikinta har ƙasa irin Butique ɗinnan,tasaka belt a tsakiyar rigar,wanda ya fitoda anihin shafe ɗinta,dama gata doguwar mace,mayafi tayafa akan rigar shima baƙi.
“Eh na iso ina fatan dai hakan bai zama muku matsala ba ina,irin na al’ada haka nan”
Bombee ta faÉ—a da É—an murmushi kaÉ—an sannan kuma tana nunawa da hannunta.
Cikin dariyah irinta wayancewa Hajiya zeenah tace.
“Ahhh ehh babu komai,bari a rakaki an gyara komai ki huta kafinnan saiki shiryah kizo mu gaisa”
Daga kai Bombee tayi tareda kallom Hilyaan.
“Mu tafi koh kina tsaye”
Kallon Jabeer tayi juyawar datayi,idanuwansu ne ya sarqe da juna wanda shima kallon wajen dayayi kenan,wani kallon ƙasƙanci yayi mata yana bin kayan jikinta da kallo kaman yaga karya. Hakan ya batawa Bombee rai,amma sosai ba dam dama tayi tunanin hakan. Kallon kayi kaɗan tabishi dashi tareda juya idonta zata wuce,kamar irin takalli abinda bata buƙatarsa a rayuwarta tayi masa kallon kuskure.
Har suka shiga mota suka nufi sashen da ainihin part É—in Jabeer yake Lubnah bata motsaba,yau taga wani abu waishi tashin hankali.
Sai bayan sun bar wajen taja wani mungun dogon numfashi tayi baya zata fadi.
Yaseerah ce tayi saurin riƙeta ganin tana shirin yin suman tsaye.
“Kambuuuuu menake ji kuma nake Yaseerah ni Lubnah,anya kuwa ban mutu ba ina raye??”
“Wanne irin mutuwa Lubnah,kina raye da ranki sarai,ki kalli kallon da Hajiya zeenah take miki ma,dan haka ki saita kanki karki nuna mata karyewarki nan da nam”
ÆŠaga ido tayi ta kalli Hajiya zeenah wacce take yi mata kallon kaÉ—an ma kika gani daga aikina. Kafin ta juyah itada yaranta suka koma ciki.
“Yaseerah muje part É—in da waccar matar ta nufah,taci nasara ta farko idan taci ta biyu zataga gadon baccina,dan haka yanzunnan ki wuce dani part É—in basai anjima ba”
“Hmmm Lubnah kibari ba yanzu ba,saboda bakida wani makami a hannunki yanzu dazaki tunkareta,dan naga babu alamar tsoro a fuskarta,amma idan kika samo Jabeer a hannunki zuwa goben,shida kansa zai sakata tafita a ciki tunda zamansa takeyi”
Dahaka Yaseerah ta samu da ƙyar ta lallaba Lubnah ta yarda da shawarta suka bar wajen suma.
Shima dama Jabeer tun haÉ—uwar da sukayi a hanya shida Bombee da zata wuce yashiga motarsa ya bar gidan,cikeda sabon wani tashin hankalin dayasan zai dawo ya sameshi ko ina yaje.
A zaune take ta tattara hankalin ta gabaɗaya wajen bawa haneef break fast ɗinsa,kasancewar daƙayar yakesha saida dabara tukunna.
Mai aikinta ce ta shigo falon da rawar jikinta fara gaisheta.
“Ahh indo kece da sanyin safiyah haka,wata sabon gani kenan,ban Æ™iraki ba kikazo da wur”
“Uhm Hajiya Lylah dama wani abune yake zagawa a cikin gidan,shine nace barinazo na shaida miki nasan baki sani ba”
“Mai ya faru haka da safennan, ince dai ba wata satar mai aiki tasake yiba?”
“Ahah ko É—aya ba wannan bane,dama amaryar da Hajiya zeenah ta aurawa Yallabai ce ta zo gidan yanzu da safennan,naji ma har tana maganar wai a hotel ta kwana jiya kafin ta iso gidan”
“Mee amarya da safe,hotel dai,yau itada wa suka zo haka har suka kwana a hotel,tana amaryar da aka É—aura aure kwana uku da suka wuce?”
“To kowama haka yace,kuma abin mamakin ma bata gaisheda Hajiya ba,shikansa yallabai bata kulashi ba,kuma naji Sagern hudu yana cewa wai ta takawa yaransa yatsan kafa da mota a shigowa”
Shuru Lylah tayi tana jin abinda indo take faÉ—a har takai ayah kafim ta sheqe da dariya tana cewa.
“Hhhhhhh kice Hajiya zeenah ta É—ebo ruwan dafa kanta,wannan shi ake Æ™ira da an gudu ba’a tsira ba kenan.
Kinga bar wannan zancen bana nan bane,bari na je sashen Iyah sayyada na sanar mata,cigaba da kulamin da Haneef kafin na dawo.
Tana gama faÉ—in haka da rawar jiki ta nufi sashen Sayyada-tateen,cikeda zumuÉ—in yafa mata wannan labari dataji,wanda tasan idan taji ba Æ™aramin daru za’a yi a gidan ba,dan akwai ta dasan mata masu al’ada da kuma tarbiyya,idan taji irin wacce Hajiya zeenah takawomusu cikin zuri’ah,za’a kwashi Æ´an kallo.
_*SADI-SAKHNA CEH*_
____****🖤🖤****_____
🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤
🖤 _BOOK 2_ 🖤
Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]
Anshiga Sashen na KuÉ—i,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka É—au hakkina bisa kanka tamm!!!
Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin
https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31
Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.
3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150
Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU
Mutanen niger kuma zaku biyah kuÉ—inku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150
______________****_______________