Dangina Book 2 Page 27
βοΈπ±π¨βπ©βπ§βπ¦ *DANGINA*π¨βπ©βπ§βπ¦π±βοΈ
*BOOK 2*
*PAGE 27*
Yanzun ke tsakanin ki da Allah hakan da kikayi kina ganin kin kyauta kenan?
Wannan ai tsabar yaudara ne da cin amana, idan bakya son shi mai yasa zaki yarda ki bashi number dinki, ina amfanin k’arya a cikin zaman takewa, ai gara ki fito ki shaida mishi cewa bakya ra’ayin shi a maimakon wannan k’aryar da yaudarar shi da kikeyi da girman ki da komai,
baku kyauta ba gaskiya”
Da yatsar shi manuniya yake nuna Sultana kafin yaci gaba da cewa,
“Kema ashe haka kike?
Wato k’ananan yara daku kunsan yanda zaku had’a kai ku cuci wani, ke kece mai gyara murya kika amshi waya kikayi magana dashi a maimakon Mahaifiyar ta daya buk’ata, kun manta ne da cewa koda shi baya ganin ku Ubangijin al’arshi yana ji da ganin duk abinda kuke aikatawa a sarari ko a cikin duhu?”
Katse shi Meenal tayi da cewa,
(Shehi ko kuma Ustaz)sune sunan da take kiran shi dashi mai makon ta kira shi da (Ya Sheikh ko Ya Naseer da wasu ke kiran shi dashi a gidan,
“Shehi kaga dagani har Sultana fa duka ba laifin mu bane,
Shi dai mutumin nan tun ranar farko na nuna mishi cewa yayi hak’uri bana ra’ayin tarayya a tsakanin mu amma ya nace ya tasani a gaba da rok’o Allah Annabi akan dai in bashi number na,
Ni kuma girman Allah daya had’ani dashi shi yasa na bashi number d’in,
To fisabilillahi tunda ni nasan ba son shi nikeyi ba ina zan yarda in had’ashi da uwata, kawai dan kar yaji ba dad’i a matsayin shi na Babban mutum shi yasa yau na had’ashi da Sultana kaga idan hankalin shi ya dawo jikin shi a hankali ni kuma zan san yanda zan fahimtar dashi ya gane bana ra’ayin shi amma kafin nan ai kasan sai nabi dashi a sannu tunda ban sani ba ko mugu ne kar inyi gaggawa in b’ata mishi rai ya kullaceni a banza dan Wallahi ance wasu mazan da asiri suke shawo kan mata”
“Koma dai menene bai dace ku yaudare shiba, kuma ma kud’in minene naji yana batun zai tura?”
Zaro idonta Meenal tayi wai mutumin nan lab’e ya musu ne da yazo ya titsiyeta a gaban shi yana musu wa’azi da tambayoyi ko ya abun yake ne? Wai dama suma maza sun iya lab’e ashe, to andai fad’i ba nauyi wallahi ustazu da sauraron hirar mataπ
“Kud’i kumaπ³? Wani kud’in?”
“Ke karki mai dani karamin yaro mana bayan duk abunda kuka tattauna naji ko kin manta a loud speaker kika sa wayar ne?
To kud’in da kuke son yin kasafi akan shi nike magana ki kirashi yanzun nan ki fad’a mishi cewa bakya buk’ata, kinji na fad’a miki dan banga dalilin da zaisa ku amsar mishi kudi bayan kince bakya son shiba”
“To amma shehi nifa ban rok’e shi kudin nan ba ra’ayin kanshi ne yasa yace zai tura kud’in, kaga kuma ai dai babu kyau maida hannun agogo baya koh? Wanda kuma yayi niyyar yin aikin alkhairi ai bai dace a dakushe mishi niyyar shiba sai yaga kamar ana mishi bak’in ciki da ladan dake ciki ne”
Ta fada tana tura baki to waima akan me zai wani ce ta kira tace karya turo kud’in bayan ita harta fara kasafin abinda zatayi da su tun kafin su shigo, Akwai friends event da suke so su had’ama Meelat ita da Maryam da sauran friends dinsu a school,
surprise suke so suma Meelat d’in shi suke ta yima shirye shirye ita dasu Moon kunga ko ai dole ta buk’aci kud’ad’e masu d’an tsoka to tana murna ta kamo jibgegen zakara kuma shine shi wannan ustazun zai wani zo ya nemi yi mata karan tsaye,
Kara wayarta yayi alamun shigowar sak’o,
Yana dubawa ko yaga daga bankin da take amfani dashi ne First Bank,
Budewa yayi yaga Alert ne na zunzurutun kud’i har naira dubu d’ari biyu,
Mamaki da tsoron Allah ne suka cika shi ya kasa cewa komai sai mik’a ma Meenal wayar da yayi yana cewa,
“Duba kiga asarar dukiyar da kukaja mishi,
Shin fashi kuka farayi ma maza ne babu wanda yake da labari ko a ina ma kuka samu fasahar aikata hakan?
Kai shima dai duk yanda akayi b’arawo ne inba haka ba taya zaka d’auki kud’i zunzurutu har naira dubu dari biyu ka turama budurwar dako gidan su baka sani ba kawai daga kayi magana da Maman ta,
Ki kiramin shi yanzun nan ya turo da account number din shi ku maida mishi da kud’in shi ki kuma fad’a mishi gaskiyar cewa ba son shi kikeyi ba dan haka gara ya dena wahalda kanshi”
Kan kame wayar tayi tana tura baki, da ido tama Sultana signal akan ta tashi ta fita daga falon,
Dan haka simi simi Sultanar ta tashi Allah yasa dama akwai Hijjabi a gefen ta dan tun d’azun sukaso zuwa gidan su Meelat sai zuwan Salman ya tsaidasu,
Ficewa tayi daga falon tana fita batayi sallama da kowa ba ta shiga motar Meenal ta tuk’a ta fice daga gidan dan hakan shine matakin farko na tsira daga wa’azin Sheikh dan tasan shi kenan kuma sun shiga uku tunda har ya kamasu kirikiri wa’azine zasu sha har su gaji amma in bai gansu a gidan ba sai dai yayi jininin shi kada’i,
“Yanzun nan shehi fisabilillahi da gaske kakeyi lallai sai na kira shi ya turo account number din na maida mishi kud’in? , kyauta fa ya bani ba tareda na rok’a ba taya zan maida kyauta bayan kaima kasan hakan babu kyau”
“Kyauta daban Meenal wannan daban”
“Babu ban banci tunda bamu rok’e shiba”
“Ok kenan dai kina so kice bazaki kirashi ya turo account number din ki maida mishi ba? To in kinci kin san kudin me kika ci?”
“Nidai koma dai menene kayi hakuri dan gaskiya ina jin kunyar yanda zan kirashi ai sai yaga kamar wulakanta shi kawai nake son yi”
“Meenal!….
Bata barshi ya furta komai ba ta mik’e tsaye tana cewa,
“Bari inje in tambayo idan Baba Malam yace in mayar mishi sai in maida”
Tana kaiwa tsakiyar falon ta kwasa da gudu ta fice sai da ta tabbatar ta yi nisa da falon sannan ta tsaya ta waigo sai suka had’a ido yana kallon ta tana kallon shi kafin ta mishi gwalo harda kashe idon ta guda d’ayaπ ta kuma murgud’a mishi baki ta juya da gudu ta fice daga gidan,
Tunda ya fara had’uwa da yarinyar nan abubuwan ta yake bashi matuk’ar mamaki ya lura da cewa kwata kwata Meenal bata da tsoro ko shayin da zata kasa aikata abunda tayi niyya a gaban shi,
Duk yaran gidan ya lura idan yana waje suna kama kansu suna shayin aikata ba dai daiba amma ita,
Ita kam kanta tsaye takeyin abubuwan ta ko a jikin ta kai shifa yama lura da cewa wani abun idan tanayi ganin idon shi yake sawa takeyin su,
Amma yau dai abunda suka aikata ita da Sultana yasa ya fara jin tsoron mata, idan har su da ba wani hankalin kirki suke dashi ba suka iya aikata haka to sauran matan da suka fisu girma wayau da kuma shekaru su kuma ya suke tafiyar da maza kenan?
Dama kenan haka mata suke tafiyar da namijin da basa so musamman idan suka had’u da sakaran namiji, kuga fa wannan shashashan daya tashi ya tura mata zunzurtun kudin daya isa ya cida marayu na tsayin wata d’aya a k’arance,
“Allah ya yafe muku kuma ya shirye ku”
Ya fad’a yana girgiza kai bayan Meenal din ta wuce,
Shifa mamaki yakeyi ma da akace mishi wai likitanci Meenal din ke karantawa, dan shi a haka yanda yake kallon ta gani yake kamar rashin d’aukar abubuwa da mahimmanci da takeyi bazasu barta tayi karatu mai wahala kamar karatun likita ba.
Suko tunda sun san abunda suka aikata kuma a yanda ta lura tsaf Shehin nan yana iya kai zancen nan gaban Malam dan haka kawai ya bud’e mata aiki, dan haka daga gidan su Meelat Tudun wada suka wuce a ranar babu wanda suka sallama sai da dare yayi nema da Mommy Hauwa taga shiru basu dawo ba ta kira Meenal din dan taji ko a gidan su Meelat zasu kwana shine Meenal din ke shaida mata cewa sun koma Tudun wada zatayi magana da Fauxieyerh ta had’o kayan Sultana gobe ta biyosu dashi can gidan,
Hatta Malam a waya ta kirashi ta shaida mishi cewa suna Tudun wada,
Baiyi fad’aba duk da cewa bai so hakan ba sai ma cewa da yayi ta gaishe mishi da Hajiya,
Shiko Salman a ranar ma sai da ya k’ara komawa gidan Malam din da dare sai kuma ya samu labarin bata gida,
Har gidan su Meelat yaje aka shaida mishi cewa basa nan,
Kwana biyu ya jera yana jelan zuwa gida Hajiya amma Meenal bata bashi daman da zai gana da ita ba daga karshe ma masu gadin ta fad’ama cewa duk ranar da yazo karsu k’ara bud’e mishi gate suce mishi bata nan,
Abun duniya duk yabi ya dame shi dan haka ya yanke hukuncin gara ya sami Uwar gida da maganar kawai,
Baiyi k’asa a gwuiwa ba haka yaje mata da zance a wani zuwa da yayi gidan Hajiya masu gadin suka hana shi shiga,
Dan haka bayan ya koma gida ne ya iske Uwar gida da malam Sulaiman a falon na Malam Sulaiman,
Bayan sun gama gaisawa ne Malam Sulaiman din ke tambayan shi ya aikin gyaran gidan Sarki wanda ya siya a Kaduna yake tafiya,
Shi kuma ya shaida musu da cewa komai ya kammala yanzun gida masu shi kawai yake jira su shiga cikin su,
Ya dade a zaune ganin bashi da niyyar tafiya ne hakan yasa Baban nashi tambayan shi da cewa,
“Salmanu lafiya kuwa ko akwai wani abu ne?”
Kanshi a duk’e ya amsa da cewa,
“Eh to dama dai wani magana ne nake so in fad’a muku”
Yakai karshen zancen yana sosa keya irin yanda maza keyi in suna jin kunya,
“To bismillah yi bayanin ka muna sauraron ka ai”
“Uh uhm uhmm dama… Dama… dama ina so ince muku na samu matar da nike son,
Umm nike son aure… Aure ne, to. To. Tooo shine dama.. Dama nace bari infad’a muku saboda ina son a shige gaba wajen yimin tambaya”
Ya kai karshen zancen da kyar yana jin zufa yana d’an karyo mishi dan bai san yanda suma zasu kalli zancen ba,
“Ah to masha Allah, shine tun d’azun ka kasa magana sai faman kame kame kakeyi”
Cewar uwar gida cike da farin ciki mad’aukaki a fuskarta,
“Bakiji d’an naki yau har da in ina ya fara ba”
Shima Malam Sulaiman ya furta yana ma Salman din dariyar in inan daya dungayi akan maganar da batafi wasu yan takaitattun harafi ba,
“A ina ka samo matar? Ina nufin yar wani gari ne kuma su waye iyayen ta?”
Malam Sulaiman ya tambaya.
Duk’ar da kanshi k’asa yayi sosai ba tareda ya iya kallon d’aya daga ciki su biyun ba ya amsa da cewa,
“Ameenatu Meenal nike so, har cikin zuciyata nike son kasancewa da ita a matsayin matar aurena dan Allah kusa baki ku nema min auren ta”
“Wai naji kamar ka kira sunan Meenal ko tsufane yasa banji sunan da kyau ba Baban su?”
Uwar gida ta fad’i hakan tana kallon malam Sulaiman wanda shima Salman din yake kallo cike da mamaki mad’aukaki,
“Ah ah ya kuma zaki maido tambayar ki kaina bayan ga wanda yayi maganar nan zaune a gaban ki,
Nima dai ban fahimci mai yace ba,
Kai wata Ameenatu Meenal din kake magana ne wai,
Ina fatan dai ba matar da d’an uwan ka ya saka kake so bakoh? dan nidai nasan ita kad’aice Ameenatun da muke kira da Meenal kaf a cikin Dangi?”
Malam Sulaiman ya tambaya yana jiran amsar da Salman d’in zai bashi,
“Ana magana dakai kayi ma mutane banza,
Ko bakaji tambayar da akayi maka bane?” Cewar uwar gida.
Da kyar Salman din ya bude baki ya amsa musu da cewa
“Eh ita nike nufi Aminatun Baba Malam kuma ai aurena da ita bai haramta ba tunda shi yaya bata mishi ba ni tayi min ina son ta zan aureta in zauna da ita”
“Da kata Malam”
Uwar gida ta fad’a a fusace tana d’aga mishi hannu alamun dakatarwa,
“Kai baka da hankali dama ashe ban sani ba?
Matar da d’an uwan ka ya aura ya sakice kake tunanin zamu sa baki a aura maka ita?
Saboda ka mai damu mahaukata,
To baka isa ba kayi kad’an dan haka karma ka sake in k’arajin maganar nan ta fito daga bakin ka koda wasa balle kuma har zancen ya fita ya zaga cikin dangi,
Kajini da kyau na kashe zancen nan bakai ba auren Meenal in auren kake so ka duba a cikin Dangi ko a waje zamu aura maka ko wacece”
Tana gama fad’in hakan ta mik’e fuuuu ta fice bata k’ara sauren mai zaice ba,
Hannuwan shi ya hada alamun roko da jan gwuiwa ya k’ara gaban Malam Sulaiman,
“Abba dan Allah kasa baki wallahi ina son ta please π ”
“Salman kana magana ne akan abunda kasan bazai yuwuba dan nidai bazan iya tunkarar kowa da maganar nan ba, zaifi kyau idan kaima kaji zance Mahaifiyar ka ka hakura ka nemo wata can daban ba Meenal ba mu kuma zamu tsaya muga mun aura maka ita”
Shima tashi yayi ya shige ciki yabar din shi kad’ai a falon sai uwar zufan tashin hankali yake had’awa, akwai matsala fa gaskiya dan bayajin zaiyi saurin sarewa dole zaici gaba da gwada sa’an shi har su saurare shi in kuma basu saurare shiba shida kanshi zaije ya gabatar da kanshi a gaban Malam.
Tunda Meenal da Sultana suka koma gidan Hajiya sai ya zamana zuwa unguwar Malamai ya musu wahala dan hankalin Meenal yana kan surprise din da suke son hadama Meelat dan haka ko a tudun wadan ma ba zama sukeyi sosai ba,
Kuma tun dawowar su ko sau d’aya meenal tak’i yarda ta tsaya suyi magana da Hajiya akan AK dan da zarar Hajiya ta d’auko zancen ita kuma zata tsareta da cewa ai ita Hajiyar tayi alkawarin cewa wannan karan bazata yarda ayi mata aure irin wanda aka mata a baya ba dan haka su kyaleta ita ba yanzun zatayi aure ba, ko dan Hajiya taga AK jikan ta shi yasa take so ta matsa mata,
To ai itama jikar Hajiyar ne bai kamata kuma ta nuna banbanci ba,
Ita dai Hajiya ta kyaleta ne kawai amma tuni ta riga ta yanke hukunci suna gama hidimar bikin nan na Musty ita da kanta zata nemi Adamu akan maganar dan babu ruwan ta da Malam Almu.
Misalin k’arfe 3 na rana ya iso garin na ZARIA,
Yana mai d’aukin dawowa dan yayi tozali da muradin zuciyar shi, bai shaida ma kowa cewa yana hanya ba dan yasan idan tasan zaizo ba abun mamaki bane ta gudu ta koma Unguwar Malamai,
Sai dai dole murnar shi ta koma ciki a sanda ya iso gidan Hajiya ke shaida mishi cewa ai basa gida sun daiyi mata sallama akan zasuje Makaranta,
Sabon wanka yayi bayan da yaci abincin da Hajiya ta shirya mishi kananun kaya ya sanya,
Kai jama’a wallahi AK bayaji indai wajen iya d’aukar wanka ne koba dan Allah ba idan yayi wani wankan dole ka tsaya ka kalle shi,wankan na yau k’ananun kaya ne bak’ak’e ya sanya dogon wandon crazy jeans sai vest daya sanya a ciki mai fad’i dan sam bata kama jikin shiba ya d’auko wata jacket itama bak’a crazy wacce duk akabi jikinta aka Yayyan ka ta saboda tsabar iya shege tun daga gangar jikin rigar har hannayen duka Anbi an yayyanka sai tsintsiyar hannun ne kawai wajen inda aka makala botura sune ba’a yanka wajen ba,
Bandana bak’i ya d’aura akai haka ma a tsintsiyar hannun shi guda wanda ya nad’e hannun rigar zuwa sama suma sai ya sanya agogo da wasu yan hannu na gayu wanda maza ke sawa,
Takalmin kafar shi ko irin π’ boot din nan ne mai tarin igiyoyi shima baki, bak’in glass ya sanya ya toshe idanuwan shi dasu bayan ya gama yima jiki shi wankan turare ya fito daga Sashen,
A farfajiyar gidan suka had’e da hajiya wacce ta fito itama wajen Dada Turai kakar billyn ya sa’eed take son zuwa,
Harta gifta shi ta dawo daga baya tana tafa hannu wa,
“Kai Abdul me nike shirin gani haka wannan shigar da kayi kuma irin ta d’iyan anna ina kake shirin zuwa ni Aminatu?
Wannan ai kirama kai tsiya ne wallahi ka rasa suturar sawa sai wannan shegiyar riga ko ina a yayyage kamar wani sabon mahaukaci, fisabilillahi wa zai kalleka in bacin wannan tabon sallan dake goshin kaba ai sai ace k’atoton Anne ne kai wallahi,
Ji takalmin da kasa ka tamke k’afa wannan kafin ka cire kace zakayi alwallah an liman ya idar da sallah tuni,
Ni ko ina ce kwanaki naga duk ka zubar da wannan shigar naka na banza ka koma shigar hausawa sak,
To yau kuma watan iya shege ne ya tsaya daga dawowan ka ka shiga ka cire suturar mutane kawai kayo shiga irin ta annan legos ka fito a haka zaka fita gari kana yawo a dunga nuna ka da baki ana cewa ai jikan prof ne,”
“Hajiya Birthday din friend dina zani fa taya zan je wajen da kananun kaya?
Nidai kiyi hakuri sai na dawo”
“Muhammadur Rasoulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam yanzun a haka kake son in shige maka gaba a baka auren jikata kana Wannan shigar anya kuwa Abdul Khareem”
Bai saurare ta ba ya shige motar shi yabarta a wajen tana faman surutai daga karshe fasa fita tayi ta wuce wajen jummai kai karan AK din.
Shiko tun a hanya ya kira Sultana ya tambayeta suna ina ne ita kuma ta shaida mishi inda suke,
Makarantar ba bak’on shi bane dan haka baisha wahalar gano inda suke ba,
A can wani cafeteria suke ita da su Maryam da alamar sun gama tattauna wa ne suka isa wajen dan cin abinci,
A kujerar da suke zaune ita da wani abokin su ne tana k’ara jaddada mishi abubuwan da take buk’ata,
Sultana ce ta fara hango shi dan haka sai tayi ma su Maryam signal akan subar wajen, zare jikin su sukayi suka koma can gefe ita kuma tana duk’e ne sai faman list na abubuwa take rubutawa,
Yana K’arasowa da Sallama yaja kujera guda d’aya a gefe ya ajiye a gefen ta ya zauna yana binta da mayen kallo,
Muryar shi da kuma kamshin turaren shi data shaqa ne yasa ta d’ago kai babu shiri,
Idanuwan sune suka fad’a cikin na juna sai ko ya wani d’age mata girar shi guda d’aya,
K’asa sosai ta amsa sallamar ta maida kanta k’asa sai dai kuma ta gagara ci gaba da rubutun saboda yanda idanuwan shi ke yawo a jikin ta,
Gayen dake zaune a gefe ne bayan ya amsa sallamar AK din yake tambayar shi da cewa,
“Malam lafiya? Ko akwai wani abun da zamu taimaka maka dashi ne?”
Wani irin kallo AK ya jefe mishi kafin a dake da jefa mishi tambaya da cewa,
“Waye Kai?”
“Ah ah ya zaka zo waje ka samu sannan ka kama tambaya na waye ni, ai sai dai ni in tambaye ka ko waye kai daka zo ka zauna a inda muke ba tareda izini ba”
“Oh haka ne fa, na zauna ban tambayi izini ba koh?
Koda yake ai babu buk’atar masoyi ya tambayi masoyiyar shi izinin zama a inda take, koba haka ba Soulmate?”
Bata dago ba ta amsa da cewa,
“Ina ganin ai mun kammala lissafin komai na buk’ata zaka iya tafiya yanzun dan muma wuce wa zamuyi”
Ta fadi hakan tana mik’a ma gayen takardar data gama rubutu a ciki yanzun,
Shima baija zancen da tsaho ba ya amshi paper din ya mik’e ya isa can inda su Maryam suke, ya rage daga ita sai AK a zaune a wajen.
“Soulmate ba gaisuwa ko baki farin ciki da zuwana bane? Kinga niko tunda na iso na kasa jure rashin ganin ki shi yasa na biyoki nan.
*UMMIEE ce*βπΌ