Arubuce Ta Ke 40
Page 40
Kuka sosai ta sakarwa ummun,da qyar ta samu ta shawo kanta,cikin hikima da dabara irin ta manya ta dinga lallabata,har sai data gamsu ta kuma ji alamun sakewa da tayi sannan ta fara tambayar ta inda wayarta take,sam ta ma manta da wani batun wayarta,sai a sannan ta tuna tun randa suka iso da nujood ta gama game da ita tace ta saka mata a bedside drawer dinta.
Kusan awa guda suka shafe da ummu a waya,har alhaji ma ya karba,Aafiya da rafi’ah da suka shigo suma dukkansu suka karba,sai da kudin ummu ya qare tsaf kiran ya yanke da kansa.
Maganganun da sukayi da ummu yasa ta samu sassauci,sai walwalarta kadan ta dawo,ta sauko daga saman gadon da wayar riqe a hannunta da niyyar kaiwa latifa.
Tana shirin bude kofar dakin aka turo qofar,sai ta danja da baya tana kallonshi yana shigowa dakin,sanye yake da wani yadi mai taushi,a ido kawai zaka fahimci bashi da kauri,saboda kana iya hangen fara qal din vest din dake jikinsa.
Baya ta sake ja tana rakubewa,gabanta kuma yana faduwa,har ya qaraso cikin dakin,ya taka a hankali ya qarasa gaban madubinta ya tsaya
“Ina kwana?” Ta gaidashi tana dan russunawa,sai ya maida dubansa a kanta,gaba daya a darare take, baisan me yasa ba,amma ya gama karantar dabi’unta tsaf na rashin sakewa da jama’a,da alama tana da wuyar sabo,shikam tako ta ina baiga ta inda wannan hadin zai zama me alfanu ba,saidai ya sani cewa,abinda babba ya hango,yaro ko ya hau dala da gauron dutse bazai hangoshi ba
“Lafiya lau,ya kwanan baqunta?” Ya fadi yana gyara daurin agogonsa,bata san ya zatace ba sai tayi shuru kawai ta sadda kanta,ita kawai Allah Allah take ya fita mata a daki,kada latifa tazo ta gansu su biyu.
Sai daya gama gyara agogon sannan ya maida kallonsa a kanta
“Shikenan babu wani abu da kuke buqata?” Kai ta gyada masa da sauri,sai ya jinjina kai,ya sanya hannu a aljihunsa ya fidda kudi ya ajjiye mata,don dabi’arsa ce,haka yakewa hafsan,koda suna da komai baya taba fita ya barta hannu babu komai.
Ido ta bude sosai ta zarosu waje tana kallon kudin,har ya kusa fita daga dakin sannan ta ankara,da hanzari tace
“Don Allah ka dauke,kada latifa ta gani,ni banaso” qaramin murmushi ne ya subuce masa duk da bai shiryawa hakan ba,ya waiwayo yana kallonta da manyan idanunsa
“Ba zata komai ba koda ta gani din,daga yanzu duk abinda na baki babu wanda zai miki fada don kin karba,right?” Jikinta a sanyaye ta gyada kanta,don dai ita ta sani ummu na fada sosai gasu basma ma idan wani ya musu kyauta suka karba,tana kallonsa har ya fice daga dakin,sai ta matsa kusa da kudin tana kallonsu ba tare data taba ba.
Ja baya tayi kadan jin an sake buda qofar an shigo,latifa ce,idanunta nakan fuskar widad din
“Kun gama wayar ne?” Kai ta gyada mata
“Eh tun dazu,kinga kudi wai ya bani” ta fada a shagwabe cike da sakarci tana dubanta
“Kuma Allah bani na roqshi ba” ta sake fada qwalla na cika mata idanu,dariya kufcewa latifa,ta yarda widad bayan quruciya ma harda sangarta irin ta goyon kaka ke damunta,qarasawa tayi inda take tsaye ta kama hannunta ta riqe
“Don ya baki kudi ba komai bane,mijinki ne kinji, komai zai baki hakanan kome zaiyi miki ba haramun bane kin gane?”, Kai ta gyada kawai bawai don ta fahimci me take nufi ba
“Kuma ya akayi ya fita baki masa rakiya ba?”
“Mu jera tare?” Ta tambayi latifa tana fidda idanu,saita jinjina mata kai
“Eh mana,bakiga ummu na raka alhaji ba?” Shuru ta danyi tana tunowa,ta gyada kai a hankali
“To daga yau kema haka zaki dinga yi masa kinji ko?” Fuska ta noqe,itadai wannan ai iskanci ne,batason irin wadan nan maganganun,haka dai ta gyadawa latifan kai,sannan ta sakata a gaba suka wuce kitchen.
A ranar latifa ta fara gwada mata yadda zatayi wasu abubuwa cikin kitchen,kamar tsaftaceshi da inda zata dinga ajjiye komai a muhallinsa cikin kitchen din,yadda zata wanke kwanuka da sauransu.
Da yammaci tana falonta a zaune bayan sun gama komai ta dinga jin hayaniyar yara,sai tayi mamaki don bata dauka akwai yara a gidan ba,daga nan ta yaye labulen falon nata,sai ta hangi su mimi suna wasa,tana son fita amma ita komai na gidan d’ari d’ari takeyi dashi,don haka taci gaba da kallonsu ta nan,har suka gama wasansu suka bar wajen.
Tun qarfe shida ta gama lafta shinkafarta da miya,ta zubata cikin food flask,bata damu da jimawar da zaiyi kafin ya dawo ba,ko kuma gumin abincin da zai iya komawa cikin flask din ba.
Fuskarta ta dauraye kawai,ta cire zanin jikinta ta nemo mahadin rigar ta saka,sannan ta tasa su mimi a gaba suka wuce sashen widad,tayi hakanne saboda ta hanashi dadewa acan,kada ya shiga yaje ya zauna,ko abinda ya faru jiya ya maimaita kansa,cikin ranta tana jin ko a jiyan ma kirsa ce kawai irin tata,ta sani cewa mace duk qanqantarta kaidi ne da ita,kada tazo tana tufka ta baya tana warware.
Kan widad na saman cinyar latifa tana kitsa mata kalba tana warewa saboda santsin gashinta,sa’annan kuma ba wani kama mata takeyi da kyau ba,tana mata ne shigen yadda ummu ke mata idan tanason tayi baccin rana,latifan na bata labarun ban dariya,wanda ya sake sanyawa zuciyarta ta kuma saki.
Koda tayi sallama hannu bibbiyu latifa ta karbeta,widad kuwa kamar ko yaushe binta tayi da kallo kafin ta zamo ta gaisheta kamar yadda take gaida dukan wanda ya girmeta,hakan kuma sai ya yiwa hafsat dadi,ta sake jin lallai itace a sama,ta dinga bin falon da kallo a fakaice,kafin ta koma satar kallon widad din,bata da matsala da komai,tana kuma jin komai zai tafi dai dai,damuwarta daya irin kyawun da yarinyar take dashi,tana tsoron kada wannan ya zama mabudin nasarar jan hankalin abbas…
“Inaaaa,bazan bari ba” ta tabbatarwa kanta da kanta cikin zuciyarta,zatayi dukkan mai yuwuwa ta hana wannan kyan tasiri a fuska da idanunsa.
Kusan da latifa suke hirar,ita widad ta maida hankalinta gasu mimi,kasancewarta mai son qananun yara,duka sai suka ja hankalinta,tana ta duban fuskar nawwara da taga tana mata kama da fuskarshi
“Ke dawa kike kama?” Ta tambayi yarinyar tana dan murmushi,mimi tayi wuf tace
“Da daddynmu mana,ni kuma da mommy na,wai shine su anty bara suke cewa ta fini kyau,wai daddy yafi mommy kyau” daga idanunta widad tayi ta dubi fuskar hafsat dake magana da latifa,eh itama taga wannan duk da qarancin shekarunta,amma dai tasan kyau
“Eh wallahi,ya fita kyau” widad ta fada hankalinta kwance cikin yanayi na quruciya.
Rigime mata mimi tayi ta soma qwalawa uwar kira
“Mommy,kinji anty ma tace daddy yafiki kyau,kuma nawwara ta fini kyau?” Dariya latifa tadan saki tana kama baki,widad din tayi wauta,amma da alama ma ita a wajenta ba komai bane,yayin da hafsat ta kafe widad da idanu,wani abu mai kama da bacin rai yana motsa mata qasan ranta,sai kuma ta buge da murmushin yaqe
“Tsokanarki takeyi,kuma ni nafi daddynku kyau,saidai ya nunamin manyan ido kawai” cikin murna mimi ta waiwaya tana duban widad
“To kinji ko?” Dariya ta saki tana jawota jikinta
“Wasa nake miki,kema kina kama da daddyn naki ai” kau da idanunta hafsat tayi daga kansu, zuciyarta na raya mata wani abu.
Yau dinma kai tsaye sassan hafsat din ya fara isa,bai taras da kowa a falon ba,don haka ya sanya kai bedroom dinta,yana taka lallausan sabon carfet din daya sauya mata dab da bikin nan,amma har datti ya fara cikashi laushinsa ya ragu ainun.
Dakin yaran ya fara budewa,komai a hargitse a zaune da duwawunshi,ash and baby pink ne color din dakin,amma pink din har ya dauki hanyar zama ash din shima,ya taka a hankali yana tattare kayan sawarsu dake watse a qasan dakin,sun cakude waje daya,ba zaka banbance wankakke da wanda baida wanki ko kuma guga ba,ya kwashe gaba daya,ya buda laundry basket dinsu da niyyar zubawa,sai ya sameshi a cike fam da kaya.
Ransa ya sosu,baiga amfanin yaron da ya aje saboda ya dinga musu wanki ba,bayan duk wata sai ya ajjiye kudinsa,to kudin ake bashi a banza ko kuwa,ya daga kayan da niyyar zubasu a haka yaci karo da undies din hafsat din,harda brassieres.
Kishinsa ne ya motsa,ransa ya sake baci fiye da dazu,sai ya watsar da kayan yaran gefe daya,ya soma birkito kwandon,nan ya dinga cin karo da undies dinta,ya dinga tarasu a gefe,har ya gama kwashesu tsaf,sannan ya zuba kayansu mimi din,ya buda toilet dinsu ya leqa,dole ya dawo baya da sauri,saboda abun babu kyan gani,mutum ne shi me masifar tsantsami,idan kanaso kaga fadansa to yaga qazanta.
Dogon tsaki yaja kamar zai tsinke harshensa,yana dai tunanin me aikin da bayaso daga qarshe daqyar idan ba ita zai sa a daukowa hafsat din ba,ya gaji da ganin wannan qazantar gaba daya,to amma kuma hakan kamar daure mata qarqashi ne,kada ta sake sangarcewa ta miqe qafa,tun a baya yaqi a kawota dinne saboda gudun ta sake tabarbarewa,amma a yanzu dukka alamu suna nuna daukotan ya kusa zame masa wajibi.
Dakin ya janyo musu ya wuce nata dakin,shima dai kamar dakin yaran,shikam natan harda tsami tsamin kayan wanki,bai saka kai da yawa ba ya dawo da baya yana ambaton sunan Allah,sai kawai ya juya ya fice daga sashen gaba daya.
Duk da ransa babu dadi haka ya daure ya nufi sashen widad din,tunda dai itama matarsa ce kamar hafsat din,tana kuma da haqqi a kansa kamar ita.
Sanda yayi sallama a falon yayi dai dai da sanda widad ke maimaitawa mimi karatun makarantar bokonta,yarinyar kuwa nata kamawa tana amsawa cikin jin dadi,don baqon abune a wajenta,mamarta bata taba tsayawa ko sau daya ta duba assignment dinta ko ta bibiyi karatunta ba,abbas din keyi mata assignment idan yana gari,idan baya nan kuma haka zata koma da litattafan ta, aunties dinsu sunsha rubuto letter suce ta kawo gida,hafsat ke karba,tana gama karantawa take yagawa,ta rubuta reply da cewa ayi haquri,mamanta ba mazauniya bace amma za’a gyara,har sun gaji da rubutun sun qyaleta,saboda suna ganin kudin ubanta ke tafiya,su basu da asara.
Rige rigen zuwa yi masa sannu da zuwa sukeyi,widad ta bisu da kallo tana jin damuwarta da kewarta na raguwa,dan zaman awannin da sukayi dasu sun debe mata kewa matuqa.
Tunda ya shigo din take bibiyar dukka motsinsa da idanuwanta,tana son taga shin ko zai kalli sassan da widad din ke zaune?,ko kuma zai saci kallonta ko sau daya ne?.
*Arewabooks: Huguma*
KI KULANI miss xoxo
DAUDAR GORA Billynabdul
RUMBUN K’AYA hafsat rano
IDON NERA Mamuhghee
A RUBUCE TAKE huguma
_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_
_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070
*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261
*Al’ummar nijerπ³πͺπ³πͺπ³πͺ zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63
*Thanks for choosing us*π₯π₯π₯π₯π₯π₯[3/2, 10:44 AM] +234 802 297 0646: *H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)