Sponsored Links
Hausa NovelsSoldiers Family

Soldiers Family 1-2

Sponsored Links

S

(Romantic novel)

*By Dr Yasmeen Ahmed*

Autar alheri ✍️

Fitaccen lbr metafeda Sabon kaccen na ban mmki da Al,ajabi bandariya dakuma tsagaran jijidakai cin Amana da ha,inci duk acikin *SOLDIERS FAMILY*

Dan Allah Kar wacca tadameni da yadda salon lbr na zekasance ba ruwanku Idan yayi Miki kikaranta Idan bemikiba shikenan 🀷

Page 1&2

Zamfara State

Acikin kauyen shinkafi.

__”mama mama kina inanewai haka aa? Wata dattijuwace kitafaman Kiran mama..daga zauren gidan aka amsa Mata cikin wata siririyar murya me shegen dad’i dagaji kasan mamallakiyar muryar yarinyace k’arama fad’ar takeyi eggo Ina zuwa barana k’arasawa babyta kitso…”Aiko Idan nasameki zaurennan zakisani mama jirankifa nakeyi shine bazakizoba shekin gama shirme?

Tasowa yarinyar tayi tana tura Baki gaba kallo d’aya zaka Mata kasan cewa kyakkyawar yarinyace ta gaske ba farabace tass Amma baza,akirata bak’aba sedai zamu iya kirantada chocolate yarinya ce wadda bazata wuce shekaru 13 ba aduniya Amma Allah yayimata sihirtaccen kyau me d’aukar hankali….karasa shigowa gidan tayi tana fad’ar Wai ke eggo idanba takura mutin kikayiba hankalinki baya kwamciya.

“Eh baya kwanciya rasa kunya karb’i nidai maza kije kid’obomun ruwa Kuma saura kitsaya aikin naki ahanya.

Batareda tacewa eggo komaiba tad’auki Dan k’aramun bokitin k’arfe tafita tana turo bakinta gaba irinna tab’a rarrin yarannan…tafe take ahanya ita kad’ai tana duban k’asa domin Idan birnin sin mama zataje to kanta ak’asa yake cikin nutsuwa take tafiyarta Idan kaganta kaga na tsatsiyar yarinya sabanin hakan kuwa katab’ata tantagaiyar rashin kunya….seda tayi tafiya menisa tabar inda harabar mutane suke kana wani katoto maciji (🐍) Wanda fad’in girmansa ma bazeyuba binta yarink’ayi abaya kamar Wanda aka aiko Sam mama Batasan dashiba tadaiji anabinta abaya Amma Koda Bata juyaba aranta tasan bamemata hakan se aminanta..

Takai inda zata dibiruwan sekawai wata yarinya tajiyo Aiko tayi Ido 4 da macijinnan wata razananniyar k’ara tasaki tareda jefarda tulunta tana fad’ar maciji maciji…cikin sauri saura yaran duk suka juya suna kallan abunda take nunawa ciki kuwa hadda nama Amma wayam basuka komaiba…juyawa sukayi suna kallonta danneman K’arin bayani Amma sesukaga tasuma cikin sauri way’anda keda Dan girma acikinsu suka dibi ruwa suka zuba Mata bayan ta farfad’o wasu daga ciki suka d’auketa izuwa cikin gari Dan sukaita gidansu domin tinaninsu gamo tayi kowa yawatse akabar mama kawai

Duk’awa tayi tad’ibi ruwanta tataso kenan wannan wasgegen macijin yak’ara dawowa juyiwarda zatayi taganshi agabanta Yana bud’ar Baki abum mmki memakon mama ta tsorata kawai seta saki wani lallausan murmushi daya Kara bayyanarda kyawunta setace “hum dama nayi tinanin Kaine bibibo to y kk kagadai katsorata Yar mutaneko tafad’a cikin shagwab’a tana turo baki ga dukkan alamu wannan Dabi,artace.

Gaba kad’an wannan macijin datakirada bibibo yayi kamun yarikid’a daga kanshi zuwa wuyanshi yakoma na mutane yayinda jikinshi yakena macizai…shima murmushi yayi Mata kamun yace tuba dakeyi uwar gijiyata… murmushi tak’arayi kamun ta,ajiye ruwanta tareda zama kusadashi tanadan kwantowa jikinshi tace bibibo nagaji dayawa Kuma yau banyiwa babyta kitsoba eggo tatasuni…. murmushi bibibo yak’arayi kamun yace to shikenan kiyi hak’uri uwar gijiyata barana kaiki gidan ko?””eh Amma Ina k’anwata ne? Gatanan tana kallanki juya kiga juyawar tayi aiko tayi Ido 4 da wata shirgegiyar damisa (tigerπŸ…) tana huci..tashi mama tayi aguje tayi wurin damisar kamun tak’arasa tazama Yar kyakkyawar budurwa me shigar Igbo ajikinta mama nazuwa tafad’a jikinta tana fad’ar shine kikadena zuwa guna ko? Itama murmushi tayi kamun tace yi hak’uri maamar memartabane ya,aikeni shiyasa Amma yanzu ainadawo…sake tura Baki tayi gaba kamun tayi wata maganar k’anwarta tace eggo fa nacanna jiranki kiyi sauri muje…to tace tareda juyawa wurin bibibo d’inta…itako k’anwarta tayi hakanne dantasan yanzu zata fara musu rigimarta data Saba…tana zuwa kamun tak’arasa wurinshi yabuso Mata wani abun afuska Aiko Bata bud’e Ido ko, inaba se zauren gidansu…dauk’ar bokinta naruwa tayi tak’arasa cikin gidan dashi inda tasamu eggo nata zabga masifa kamar taci Babu…itadai mama tana ajiye ruwan tawuce dakinsu bayan minti 5 dashigarta tafito dashirinta na isilamiya tareda yiwa eggo sallama tatafi..!

Tofa πŸ€” wayannan dabbobin dake tareda wannan yarinyar miye hadintadasu?

Abu Dhabit (Dubai)

Wasu manyan motocine ke tafe cikin azababben gudu suna doka jiniya wani katon stet suka nufa Wanda fad’in girmansa ma b’ata bakine akallah wannan stet d’in yayi girma wani Dan k’aramun gari kaitsaye wani babban gert suka nufa bayan sunyi tafiya me Nisan acikin stet d’in suna kaiwa Gert d’in yawangale kanshi mitocin suka nausa ciki Perkin sukayi a perkin space kana duk suka shiga fitowa kyawawan samarine yayan larabawa masu shegen kyau da d’aukar hankali dukkansu suna cikin shigar kakin soja nak’asar Dubai abun gwanin Sha,awa kasa lisafa yawansu nayi domin suna neman k’urewa lissafina dukkansu k’ofar dazata sadasu da babban perlon gidan suka dosa suna shiga suka fara fad’ar habibbty habibbty habibbty dukkansu abunda kefitiwa daga bakinsu kenan..suna cikin kiranta wata dattijuwar tsohuwa ce tafito daga wani bedroom dakenan cikin perlon tana fad’ar lalemarhabuk lale,lale dukkansu K’arasawa sukayi wurinta d’aya bayan d’aya haka suka rinka hugging d’inta tareda manna Mata kissing agoshi seda duk sukayi Mata hakan kamun dukkansu Kuma sukama hanyar barin part d’in gaba d’aya itako tabi jikokin nata da kallon k’auna…suna fitowa kowanne part d’insu yanufa domin gaisarda iyayenshi Kuma suyi wanka rarrabuwa sukayi wasu biyu sushiga part d’aya wasu Kuma ukku keshiga part d’aya wasu Kuma mutin d’aya keshi hakan suka rik’ayi…ganin hakan yasa nagane cewa dukkansu ba y’ay’an mutin d’aya bane domin kowannan su bangaren iyayenshi yakebi.

“Assalamualaikum ammy ammy cikin wasu ukku dasuka shiga wani part d’in suke Kiran manarsu tana zaune a perlo tana kallansu se murmushi kawai data keyi k’arasowa sukayi wurinta tareda manna Mata kiss agoshi suka rungumeta sosai ajikinsu kamun sud’ago suna kallanta cikin harshen larabci d’aya daga cikinsu yace ammy ammiki wanka? Kaita girgizamai alamar eh anyi Mata..kamun yayi magana d’ayan yace abuncifa ammyna? Shima murmushi tayi tareda girgiza Kai alamar Bata ciba..dayan wada keda matuk’ar kamada wanda yayi maga daga farko yace dama kusan baci zatayiba semun dawo dukkansu sukayi murmushi kamun biyu suka shiga dakinsu danyin wanka sushirya sufito seda suka gama suka fito bayan sun zauna tareda ammy d’ayanma yatashi shima yayo kana suka nufi dining table domin suyi dinner..

 

*London*

Kwance yake abakin swimming pool yalumshe idanuwanshi kyakkyawan saurayine ajin karko Wanda kallo d’aya zaka masa kasan cewa shid’in yakai duk inda akeso namuji yakai yanada kyakkyawar Kira irinta karfafan maza dogoneshi daga yadda yake akwance zaka fahimci hakan yanada kwarjini duba da yadda yahad’e Rai kamar besan minene dariyaba Dan k’aramun bakinshi med’auda pink lips se motsawa yakeyi kamar me magana cankuma yamika hannu tareda d’auko wayarshi yashiga contact d’inshi tareda Kiran wata nomber yak’ara akunne…d’ayan bangaren Wanda yakira Yana d’auka yace hello my sweet bro inawuni yafad’a da larabci….shiru yayi kamar beji meyaceba seda yak’ara yin magana kamun yayi Dan k’aramun tsaki cikin cool voice d’inshi yace Al,Husain Ina ammyna? Dan murmushi captain Husain yayi kamun yakalli ammy dake zaune suhaif nabata abunci yace ammy tana lpy qalau my sweet bro abunci Yaya suhaif kebata…later I will call you video call I love see my mom Yana gama fad’ar hakan k’itt yakashe wayar…. murmushi captain Husain yayi kamun yadubi Yan uwanshi suma duk sukayi murmushi suname cigabada cin abuncinsu.

Shiko bayan ya yanke wayar shiru yayi Yana tinanin har yoshe zasuyita zama da mahaifiyarsu acikin wannan halin Miya kamata sunyi? Ina dadynsu yake Yana Raye koya mutu? Duk shikadai keyiwa kanshi wannan tambayar dabamai bashi amsarta..se yanzu abud’e idanuwanshi dasuyi jajir sabida kuncinda yatsincin kanshi aciki Amma dudda hakan behana ainihin sahihin kyawun idanun nashi fitaba domin idonshi kamarna mage hakan suke sedai manyane sosai Kuma alumshe suke bawai me laifiba kime gaskiya yawatsawasu se hantar cikinshi ta kad’a…. mik’ewa yayi tareda fara tafiya cikin tak’ama da kuzari tafiya yakeyi irinta karfafan maza masuji da kansu kaitsaye wani k’ofar yashiga segashi yafad’o wani kyakkyawan bedroom wayoyinshi kawai ya,ajiye tareda nufar cikin bathroom wanka yayi yafito d’aureda towel akugunshi wannan mird’ad’d’iyar k’irar tashi duk awaje ga sking d’inshi se shek’i yake shiryawa yayi agurguje cikin kayanahi na jojojin London tareda fitowa harabar gidan yanufi inda motocinshi suke kaitsaye…tinkamun yakai wurin wasu sojojin suka taso dagu2 suka bud’e Mai yashiga suma shiga sukayi kamun atada motocin cikin azababben gudu sukabar gidan mota kusan 7 ahakan suka fita ukku gaba ukku baya d’aya wadda yake ciki a tsakiya..

Happy sallah all my lovely fansπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒIna fatar kunsha ruwa ply Allah yakarb’i ibadunmu Baki d’aya 🀲

 

 

Autar alheri ✍️

πŸš€ *SOLDIERS FAMILY*πŸš€

(Romantic novel)

*By Dr Yasmeen Ahmed*

Autar alheri ✍️

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button