Dabi’ar Zuciya 43
43
Tsahon wasu mintuna yana duqe gaban daddyn bayan ya gaidashi ba tare daya maido masa amsar gaisuwarsa ba,kamar bazai amsa din ba,har sai daya gama kurbe baqin ruwan shayinsa sannan ya dubeshi
“Sai yanzu ka damu dani daka ganni?,sai yanzu ka damu kasan lafiyata?”
Ƙas yayi da kansa,don baisan da wanne yare zai wanke kansa ba,iya yinsa dukka yayi ya sameshi a waya amma abun yaci tura,baisan me yasa hakan ba
“Duk dai tsiya baka da mahaifi sama dani,kuma ba’a cazawa tuwo suna ko?”
“Tuba nake” ya fada cikin ladabtacciyar murya,yana zaune har daddyn ya qarashi fadansa yadda ransa yayi masa,duk da qoqarin dakatar dashi da mummy keta yi,saiya hada harda itama cikin fadan.
Sai daya tabbatar ya gama sannan ya sake gaidashin,ya amsa sama sama,sai ya miqe ya lalubi kujera ya zauna bayan ya aje masa file din hannunsa a gabansa
“Wannan file din dukka lissafinmu na qarshen shekara ne da dukka bayanan komai da komai,zaka sanya hannu ne asanya cikin documents na kamfani”.
Baiko daga kai ya duba file din ba,yana zuba wani ruwan tea din a kofi yace
“Ka dauka ka baiwa fawwaz ya duba ya sanya hannu”
Banbarakwai yaji lamarin,ta yaya fawwaz zai shiga cikin lamari irin wannan?,ta yaya babban sirri irin wannan zaice a baiwa fawwaz din ya saka hannu?,bayan abune daya shafi daddyn?,share dinsu ne shi dashi,me ya shafi fawwaz banda yayi aiki a biyasa kowanne wata kamar kowanne ma’aikaci,ya zaci zaiji mummy tace wani abu,amma baiji tace komai ba,saiya dauke idanunsa daga kan file din zuwa fuskar daddyn
“Amma kamar ba hurumin fawwaz bane,wannan abune daya shafi masu share a kamfani”
“Kudin waye?” Daddyn ya fada kansa tsaye yana duban qwayar idanun samir
“Naka ne,Allah ya huci zuciyarka” saiya miqe ya qarasa inda ya ajjiye file din ya dauke
“A huta lafiya” ya fada yana nufar qofa
“Son,yau da wuri haka?,abincin fa?”
“Zanci a waje mummy”
“Jirani,ko wani abun sassauqa a hada maka ka tafi dashi” ta fada tana miqewa da hanzari.
Hannu tasa ta amshi packaging da tasa aka yiwa samir din tana miqa masa
“Kaga bance komai ba kan batun bawa fawwaz file ya saka hannu ba ko?” Tayi tambayar tana miqa masa,yasa hannu ya karba ba tare da yace komai ba,tasan kuma zaiyi wuya yace din,don ta karanci fushinsa da bacin ransa fiye da kowa
“Kayi haquri son,daddynka ya fara zargar goya maka baya akan komai,banason wannan rashin jituwar dake tsakaninku taci gaba da dorewa,gudun kada takai har kan ‘ya’yanka,shi yasa na yanke shawarar yin shuru kan wasu abubuwan,badon inason hakan ba,sai don babu yadda zanyi” kai kawai ya gyada mata yana lumshe ido,tare da qoqarin hadiye bacin ransa,saiya juya zai soma barin wajen,tayi hanzarin sake tsaidashi,tana ganin wannan wata dama ce gareta daya kamata tayi amfani da ita.
“Son” ta sake kiransa,saiya dakata ya kuma waiwayo,takawa tayi zuwa inda yake tsayen da kanta,fuskarta na nuna russuna da kuma alhini.
Dukka nutsuwarta ta tattaro tana dubansa,irin duban da zai gaya masa cewa dukka zancan da zata furta na gaske ne,shima ita yake kallo,da alamu kuma ya tattara mata dukkan hankalinsa ita yake sauraro
“Akwai abu guda daya da mahaifinka yake ra’ayi da kuma buri,wanda aikatashi zai zama silar warwarewa,dama dawowar dukkan wata fahimta da jituwa a tsakaninku” shuru ta danyi kafin taci gaba
“Mahaifinka bashi da burin daya wuce ka auri jauhar ‘yar abokinsa,me zai hana ka sadaukar da wannan farincikin zuwa gareshi?,ina da tabbacin hakan zai sake kawo qauna da jituwa tsakaninku…..amma kaje kayi tunani,burin kowanne da ya samu qauna da kulawa ta mahaifinsa,kana da wannan damar”
Zaman irin na dirshan tayi gaban professor,irin xaman da idan tayi shi yasan tabbas akwai babbar magana da takeson yi dashi,idanunta cikin nasa,cikin wani laushi ta soma magana dashi
“Ko kusa ko alama bana jin dadin irin wannan mu’amalar dake gudana tsakaninka da samir,raina baya min dadi sam,ko babu komai kusan nice a tsakaninku,kuma samir tamkar dan dana haifa nake jinsa,kaga kuwa ko meye zaya sameshi hakan bazai taba yimin dadi ba”
Sosai yake kallonta,yake kuma yaba kyan hali dana zuciya irin nata,tsahon shekarun ko sau daya bai taba ganin ra kwarewa samir baya ba,komai wuya kome dadi tana a gefansa,saiya zauna sosai ya gyara zamansa
“Babu abinda yake hadani da danki illa taurin kai da kafiya,da kuma ganin ko meye ta yankema rayuwarshi nashi shine dai dai,kome na yanke a rayuwarsa yana kallons a matsayin opposition na ra’ayinsa,ni kuma bazan zauna yana yankamin da gindayamin dukka sharudda da yaso ya kuma ga dama ba,don bashi ya haifeni ba,nine na haifeshi” shuru tayi bayan ta sauke ajiyar zuciya ta dago ta kalli professor
“Babu abinda yake zama cikasa hankali da kamalar dan adam irin aure,koda kuwa nutsuwarsa ake da buqata,tofa la shakka aure shike gyara mutum….inajin option daya kuma hope daya muke dashi akan samir….shine aure,aure ya kamata kayi masa”
Hannuwansa ya wara kafin ya maida bayansa ya jinginar a jikin kujera
“Ya isa ya yiwa kansa aure ai,ni meye nawa a ciki?” Kai ta jinjina wani abu na taso mata tana danneshi,tana tuna wani abu daua faru shekarun baya da suka shude,wata magana shigen wannan data taba faruwa,ba shakka duk inda take tunanin nasararta bata kai ba tama shallake nan,saidai a yanzu kuma ba irin wannan amsar take buqata daga bakin daddyn ba,tana so ne ya shiga lamarin tsundum fiye da kowa.
Kanta take kada masa kafin ta sake cewa
“A’ah,daddy wannan sam ba kalmar data dace ta fito daga bakinka bace,kanason ka sake jawomin sabuwar tsana daga mutane ire iren hajiya qarama?,wannan aikinka ne,dole ka sanya hannu,koda kuwa shine abu na qarshe da zaka yiwa danka,ba’a sakarwa yaro garma” saita dakata tana karantar yanayin fuskarsa na wasu sakanni kafin yace
“Kin fiya damuwa da lamuran samir da yawa…..”
“Wa nake dashi sama dashi?” Ta tari numfashinsa fuskarta dauke da murmushi,sai yayi shuru ya zuba mata idanu,tana sake burgeshi,tare da sake jinjina mata,yana ji a ransa lallai ta cika macen qwarai,duk da har yanzu yana jin wani emptiness can qasan zuciyarsa,wanda har yau wannan gurbin ya gaza cikuwa.
“Daddy,duk da samir ya haura shekara talatin….amma ni har yanzu kallon yaro.nake masa,kamar yadda kowa ya sani,yaro baya taba girma a wajen iyayensa koda kuwa furfura gareshi,matuqar suna raye,har abada kallon yaro suke masa…..yaronmu Allah ya masa baiwar arziqi da daukaka,ba za’a rasa tarin ‘yammatan dake son shiga rayuwarsa ba,wanda da yawansu wala’alla ba don Allah suke sonsa ba,so abinda na hango anan shine……ka zaba masa mata ka aurar dashi,matar da kasan ta dace dashi,yar asali kamarsa,yar gidan arixiqi,ga misali jauhar……har yanzu ita da iyayenta suna nan akan bakan son bawa diyarsu samir din” kai daddy yake jinjinawa,ba shakka tayi zurfin tunani da kuma hange,kuma maganarta na bisa turba,mahaifin jauhar kusan abokinsa ne na kusa,tare suke gudanar da duk wata harka ta siyasarsu,hakanan mahaifiyarta akwai qawance mai qarfi kuma dadadde tsakaninta ta da mummyn?,to me yayi saura?
“Na yarda dake,nasan zaki iya komai,na baki wuqa da nama akan lamarin” qasaitaccen murmushi ya subucema mummyn,tuni ta soma hango nasara ruwa ruwa,saita gyada kai cikin salo tace
“Na gode qwarai da gaske mijina da wannan babban matsayi daka bani”murmushi kawai ya mata yana ji a ransa inama inama?……..
Wadan nan kalaman na mommy sune sukayi ma samir qawanya,suka dinga kai kawo a kwanyarsa,har zuwa sanda yakai office.
Ringing din da wayarsa keta faman yi sai yakejin kamar ana yamutsa kwanyarsa ne,bashi da mafita illa ya daga wayar,saiya miqa hannu ya dauka ya kuma kara a kunnensa.
Sallama yayi cikin muryarsa da tayi sanyi,daga can daya bangaren aka saki ajiyar zuciya sannan aka amsa.
Cikin nutsuwa aka fara gaidashi,ya amsa yana Allah Allah yaji saqo ko dalilin da yasa aka kirashin
“Mubina ce,kira nayi dama nayi maka godiya kan dawainiyar da kuka yimin” sam bai gane wace ba,a yanzu kuma qwaqwalwarsa babu wani space da xai iya tuna wace ita
“Ok yayi kyau” kawai ya amsa,yana qoqarin ajjiye wayar,kamar ta karanci hakan saitayi hanzarin cewa
“Kamar baka gane wace ba,mubina da kuka kai clinic kai da abokinka da daddare”
“Oh….ok,sannu,ya kike?” wannan tambayar da yayi mata ji tayi kamar ya mata wata babbar kyauta,saita gyara kwanciyarta dadi na ratsata
“Alhmdlh,nama samu sauqi”
“Ma sha Allah,haka akeso” ya fada yana fitiwa daga motar,sannan ya dora da cewa
“A gaida mutanen gidan” ya katse wayar yana sanyata a aljihunsa.
Sama sama ya gaisa da ma’aikatan yakai kanshi office dinsa,iska me zafi ya furzar sanda yake zama saman kujerarsa,tsahon wasu sakanni yana qoqarin saisaita tunanukan da suka cuse masa kwanya,kafin ya dauki wayar tafi da gidanka yayi kira daga can reception kan shaidawa fawwaz yana nemansa,yaci gaba da juyawa saman kujerarsa a hankali a hankali.
Minti goma aka shaida masa isowar fawwaz,aka bashi izinin shigowa.
Kan idanunsa qofar ta bude,fawwaz din ya shigo,yana takawa dai dai idanunsa saman fuskar samir,kamar yadda Shima Samir din shi yake kallo,da wani irin kallo dake nuna zallar kwarjini qasaita da kuma isarsa.
Tsaye yayi gaban table din samir din,a hankali saraki ya janyo file din gabansa ya turashi gaban fawwaz,idanuwansa tsakiyar na fawwaz din yace masa
“Ka saka hannu on behalf of daddy,but…..karka fita dashi out of company,kayi singing a nan ka dawo dashi” daga haka ya tura kujerarsa baya yamiqe a hankali ya murda qofar toilet ya shiga,saboda lokacin sallar walha yayi,yana kuma saka ran zuwan amiru,akwai abubuwa da yawa da yakeso su tattauna.
*_SANNU SANNU KWANA NESA_*
Ta farat daya kamar a mafarki ta soma tsintar sauye sauye kala daban daban daga rayuwarta,sauyin da iyaka kaifin tunani da basirarta basu taba kawo mata su ba.
Cikin watanni qalilan saiga kaltume ta soma sauyawa,tun daga suna daya koma kulsum ahmad zuwa yanayin fatarta,murjewar jikinta da kuma gashinta da ayanzu take kallonsa kamar ba nata ba,kamar na kanti ne aka aro aka dora mata,tun daga ranar da jawahir ta turketa ta sakata ta tsefeshi,ta wanke mata shi tas,sannan ta kwasheta zuwa wanki da gyaran gashi,saiga tsahon cukurkudadden gashinta yana neman ninka tsahonsa na asali,abinda ya sanyata ita kanta a zallar mamaki.
Tsaye najwa tayi a kanta kan duk wani amfani data siyo saboda ita,tace sam ba zata yarda ta fito daga gidan professor rashid ba a dinga ganinta a haka ana rainata ba,hakan kamar ci baya ne da koma baya ga sunan gidansu,saboda sunan ba boyayyen suna bane,duk kuwa da cewa da sunan mahaifinta take amfani,amma dole wataran a gane daga inda ta fito.
Sannu a hankali zama da gogayya tasa ta soma sauya abubuwa da yawa,rayuwarta ta fara sauyawa zuwa daga kattume zuwa wata kulsum,’yar makaranta,mai ilimi,ba kaltumen qauyen dinya ba.
Daga gefe guda kuma hazaqarta tsafa da rashin quiya saiya sanya ta zama kusan kome na gidan ana sanyata ciki,ko kadan bata taba kawowa ranta komai ba,hakan ma dadi yake mata,a qalla ta zama busy sosai,tunda ta fuskanci babu xancan zuwa ko komawarta gida,saita watsar da komai ta fuskanci gobenta,ta fara kwasar gardin ilimi,takan mata kwata kwata da cewa wai aure ne tsakaninta da samir,don ba wani haduwa sukeyi dashi ba sosai,mutum ne me yawan aiki da sabgogi,wanda mafi yawanci yana fita ne da safe,dawowarsa kuwa sai bayan sallar magarib.
Ta fannin daddy kuwa yana daukarta ne kamar jawahir,musamman saboda shaquwar dake tsakaninta da jawahir din,saiya sanya kome zatayi tana sanyo kaltum din a ciki,duk kuwa da irin kallon banza kyara da kuma hantara da take samu daga najwa,hakan baisa ta sare ba,dole take dauke kai daga dukkan wasu halayya da dabi’u na najwan,wanda ta sani,inda ta sameta a matsayin kattume ne a qauye,bata isa tayi mata irin wadan nan abubuwan ba,koma meye tana daukarsa da sauqi,saboda bata taba sanya iyayenta a ciki ba.
Sannu a hankali rayuwar taci gaba da jujjuyawa,cikin watanni ta gama ss one ta tafi ss two,babu jimawa kuma aka fara batun zana qualifying.
Batasan yadda abun yake ba,don haka hankalinta ya dugunzuma,tayita fargaba,tana tsoron kada ta fadi ta jawa samir din daya tsaya da aljihunsa yana biya mata kudin makaranta da dukka sauran buqatunta,zataji kunya matuqa idan hakan ta faru,ba kuma zata yafewa kanta ba.
Sanda take gayawa jawahir haka dariya ta dingayi mata
“Babu fa komai kaltum,ba wata jarabawa bace ta tashin hankali ba, infact ma idan bakici ba za’a biya miki ne shikenan an wuce wajen” kai ta kada
“A’ah,nifa nafison na ciyo da kaina,hakan nasan dole zaifi faranta masa akan abiyamin,xaifi kuma yarda da cewa ba asarar kudinsa yake yi ba”
“Kaltum….wannan idan kika tafi University sai kuma yaya kenan?”
Murmushi ne ya subuce mata,ta riqe matashin kujerar da suke kai sosai
“Wayyo Allah na,ranar bazan iya bacci ba”
“A gidan ubanwa zata University din?,badai a gidan nan ba,taimakon ma da akayi mata aka fiddata daga duhun jahilci da kantar qauyanci ai ya isa,amma muje University itama taje?,babu wannan maganar,gwara ma ki shiga hankalinki ki daina kwadaita mata abinda bazai yiwu ba,ko ta fidda miji dai dai ita tayi aure,ko kuma ungulu ta koma gidanta na tsamiya” najwa dake nutse cikin daya daga cikin lausasan kujerun falon riqe da remote na tv ta fada,tana gyara zaman gilashin fuskarta.
Sosai bacin rai ya bayyana kan fuskar jawahir,yayin da kaltum tayi qas da kanta,dadin hira da jawahir yasa ta manta gaban waye take magana,ta kuma so manta ita din wace,wanda kullum takewa kanta tilawar daga inda ta fito,kada ta sauya hanya kota manta asalin nata,abunda ba zata taba iya yafewa kanta ba kenan idan ta bari hakan ta faru.
Miqewa kawai jawahir tayi ta kama hannun kaltum tana cewa
“Muje ciki saimu qarasa hirarmu”
“Cikinki xaki maidata ba daki ba,banza local kawai” najwa ta fada,ko waiwayowa ta dubeta jawahir batayi ba suka shige ta gabanta.
“Karki damu da maganar ya najwa pls katum” murmushin qarfin hali tayi,duk don ta kauda bacin ran data gani saman fuskar jawahir
“Kin manta hali da dabi’arta ba baqona bane?, don’t bother,babu komai fa” murmushin turancin da kaltum din ta jefo ta saki,tana ganin qoqarinta matuqa da gaske, gifted ce irin wadda ta jima bataga kamarta ba,bata taba tunanin zatayi catching up har haka ba,duk da cewa sanda ta gayawa ya saraki tana da hope sosai a kanta,sai gashi ta tabbatar mata da hakan
“Bari na duba ko bibi ta gama tuwon nan na karbo”
“Baza dai ki manta ba” tasan me take magana a kai,sai tayi murmushi
“Gado ai sai dan gado,kowa yabar gida gida ya barshi” kai ta jinjina ta bita da murmushi harta fice,saita zauna gefan gado tana wani nazari,itakam ba zata iya tuna lokaci na qarshe da mummy ta kaisu sukaga nata dangin ba,duk wannan tarin alkhairin nata bata ce ga wani nata na kusa da yake amfana ba,tana tsananin mamakin hakan,tayi mata magana tayi qorafi da mita har kamar bakinta yayi ciwo,takan ce musu garinne yayi nisa,tanason kuma ta shirya sosai kafin suje,sanda suna qanana wai basa daukan dogon lokaci basu je ba,najwa tace ita takan tuna sanda suke zuwa din,amma ba sosai ba sabida abun ya danyi nisa,yanzu ne dai da abubuwa sukayi yawa a cewar mummyn zuwan ya gagara,ta rasa gane wane irin shiri ne wannan,amma takan baiwa faruwar hakan uzurin cewa don dai mahaifi da mahaifiyarta sun rasu ne.
Da sallama ta shiga dakin biban,saita amsa mata tana qoqarin boye takardar dake hannunta,a lokaci guda kuma tana yunqurin goge hawayen daya jiqa mata fuska.
Sosai jikin kaltume yayi sanyi fiye da ko yaushe,wannan kusan shine karo na uku data taba riskar bibi a irin wannan yanayin,saidai kullum amsa daya take bata
“Yar uwarta data rasu take tunawa”
“Kin biyo sahun tuwonki ko?” Bibin ta fada tana dora murmushi kan fuskarta,kai ta daga mata a sanyaye
“Muje na baki,nima jira nakeyi nayi sallar magariba tukunna kafin naci” ta fada tana sake goge fuskarta da habar zaninta tana yin gaba.
Har ta kusa fita saita dakata,ta waiwayo tana duban kaltume
“Kada ki sake ki shaidawa kowa yanayin da kike shigowa kina samuna a ciki har karo na uku,yin hakan zai iya zamewa rayuwarki hadari” bibi ta fada muryarta nayin rauni,tana kuma girgixawa kaltum kai alamun tabbatarwa