Sponsored Links
Dabi'ar Zuciya Hausa NovelHausa Novels

Dabi’ar Zuciya 14

Sponsored Links

Suna cin abincin suna hira,affan din yana bawa samir labarin makaranta,yanayin karatun nasu irin wahalarshi da sauransu,lokaci lokaci hajiya qarama na sanya musu baki,har suka gama,affan ya kira jummai ta debe kwanukan,saiya miqe tsaye yana miqa ya dubi hajiya qarama
“Hajjaju zanje nadan kwanta,baccin jiya da banyi ba duk ya cikamin idanu”
“Ala kiyaye”ta amsa shi,saiya waiwaya ya dubi samir daketa faman goge hannu duk da cewa ya wanke,da yake shi mutum ne da ba kasafai yake cin abinci da cokali ba
“Yaa saraki…..zanje nadan watsa ruwa,idan na sameka to,idan ban sameka ba a gaidamin twin sister na” dan qaramin murmushi ya saki,kana yace
“zata ji” saboda yasan wa yake,da haka yabar musu falon su biyu kadai.

Shuru ne ya ratsa na wadansu sakanni sannan hajiya qarama ta gyara qafarta dake miqe daya kan daya
“Muhammadu” ta kirashi da sunan da ba kasafai ake kiransa dashi ba,samir ko saraki yaso ya shafe na ainihin,saiya daga kai ya dubeta yana amsawa
“Ina waccar maganar da uwarka data taso da ita?,ina fatan dai ta mutu kamar yadda ka gayamin?” Kai ya jinjina a nutse yana duban hajiyan,saita gyada kan nata itama
“Kun kyautawa kanku……abinda yasa nayi kiranka shine,kaga daga ni har mahaifinka kowanne so yake ka fitar da macen aure,bama mu kadai ba,duk wani masoyinka,hatta da yadikko dake azare,kayi qoqari ka zabi yarinya cikin dangi ko wajen dangi,bana so luma bana qaunar na sake jin labarin wai jidda ce zata zaba maka ko ta zabar maka wadda zaka aura,saboda halan bazai haifar mana da daa mai ido ba a tsakanina da ita,idan kuma baka maida kai ka zabi mace ba,to tabbas ni zan zabar maka,don suna nan sun kua guda goma wadanda nasa abincika minsu,kuma kowacce ta isa macen aure” murmushi ne zai subuce masa,amma sai ya sanya tafi hannunsa saman bakinsa,kamar mai shafa kwantaccen gashin daya zagaye habar tasa zuwa qasan hancinsa,a hankali yana duban hajiya har takai qarshe,cikin girmamawa yace
“In sha Allah ba za’a kai haka ba,nan kusa zan kawo miki ita ta gaidaki” wanda shi kansa yasan ya fada ne kawai,saboda a yanzun koda bindiga aka ritsashi ba zaice ga wadda yaji ta kwanta masa ko yake soyayya da ita ba,duk da tarin masoyan da yake dasu,wasu sun bayyana,wasu suna dakon kayansu,hakanan kullum wayewar garin Allah baya rasa samun saqonni daga wajen mata kala daban daban,wasunsu ma baisan su waye ba.

******************

Karfe tara da ashirin na safiya yana tsaye cikin falon,wanda babu kowa,daga shi sai mai aiki dake hada masa breakfast da xaici ya fita,kasancewar yau jawahir bata nan,ta fita tun takwas tana da lactures,haka ma daddy tun bakwai ya fita,suna da wata tafiya shida mai girma gwamna,najwa na ciki tana bacci,mommy ma tana nata dakin,saidai ta leqo tace a hada masa abun karyawar,zata shiga wanka ta fito.

Sai data gama hadawa sannan tadan russuna sanda yake danne danne a wayarsa,yayi kyau cikin wani yadin maza da aka yiwa dinkin zamani,wanda ya dace sosai da jikinsa,fuskarsa kawai zaka kalla kasan yan tafiya da zamani,komai nasa dai dai a muhallinsa
“An gama yallabai” dauke idanunsa yayi daga saman wayar,ya dubeta
“Yauwa……sannu” kai ya gyada taja baya ta soma barin wajen,sai taji yace
“Zo mana” ba tare data jinkirta ba ta dawo inda ta tsaya daxun,yana hada tea din yana motsashi da cokali saboda ya rage zafi ya dubeta
“Me ya faru su baba mai gadi basa samun abinci kullum sau uku a rana?” Shuru tayi kanta a qas,tana nazarin abinda zata fada,bai katse ta ba amma yaci gaba da sauraren amsarta ba tare da ya sake cewa komai ba,sai daya kurba tea din sannan ya sake maimaita tambayar,dai dai sannan mommy ke fitowa,taji tambayar da yake yi din,don haka tace da ita
“Jeki zuwaira” ta fada tana jan kujera daya ta zauna tana dubanshi.

Second kusan uku sannan tace dashi
“Bansan ya zan musu fada su gane ba,nasha gaya musu babban abuj kunya ne ace mun kasa ciyar da ma’aikatanmu…..amma in sha Allah daga yau hakan ba zata sake faruwa va,zanwa tufkar hanci” kansa ya jinjina sannan ya aje cup din hannunsa
“Bai kamata mu dinga qoshi suna kwana da yunwa ba,alhalin mu sujewa aiki,sun sadaukar da lafiyarsu da qarfinsu duk saboda mu…..ki musu magana mommy a gyara please,idan mangyaran bai yuwu ba ni da kaina zanyi maganin abun,i sure daddy bai san da haka ba” kai ta daga tana dubansa
“Tunda nace an gama daga yau, trust me an gama din son” ta fadi da murmushi kan fuskarta,shima saiya saki murmushin.

Sama sama ya qara abincin kana ya miqe,saboda kiran da umar da murtala sukayi masa kan sun iso,ya dubi mummyn
“Zamu wuce mummy……ni suke jira”idanunta saman fuskarsa ta jinjina kai
“Allah ya tsare,sai kun dawo”
“Koda daddy zaiyi qorafin nan……”
“Baka da damuwa da wannan,jeka abinka” ta tareshi tun kafin yakai qarshen maganar,hakan ya masa dadi,tako wanne bangare ya tsaya tana tare dashi,tana kuma bashi goyon baya dari bisa dari akan duk abinda ya yanke,don haka cikin karsashi da jin dadi ya juya ya nufi qofar fita,yayin data rakashi da idanuwanta harya gama ficewar.

Nannauyar ajiyar zuciya ta saki,sannan ta maida idanunta gurbin daya tashi yanzu a kai na wasu sakanni,sannan ta janye idanun nata,taja sauran kayan breakfast din daya gama ta fara hadawa,don itama tana son ta fita taje ta dawo kafin azahar.

**********Daga gefe daya na tsakar gidan nasu dake a share fes take zaune,saman kujera ‘yar tsuguno,tana yiwa wata matashiya da bata wuce sa’arta ba kitso,da qyar take kama kan,don babu yadda zata yine,da lashakka ma bazata mata kitson ba,duba da yadda kanta yayi datti,har wani toka toka yakeyi,saidai a wannan karon ta tayar da neman kudi sosai,kitso take babu ji babu gani,dalilim ciwon qafar mahaifiyarta da a yanzu ya fara daga mata hankali,saboda kullum qara gaba yakeyi,burinta kawai a hada kudin magani da zata kai asibiti,ko yaya ta samu relief na ciwon dake jin jikinta.

Bilal ne daga gefe zaune yake daura qwabja qwabjan takalmansa da yake fita aiki kullum dasu,surutu yaketa mata saidai hankalinta bai wajen gaba daya,nata can tana lissafa adadin abinda ta tara ne,duk da kitson data kama babu dare babu rana tanayi.
“Inama zan samu wanda zai dinga sayen zanena” ta fada cikin zuciyarta,saboda yawan zanan data tara da kayan da bilal ya kawo mata,saidai duk wanda tayi ma maganar dariya yakeyi cikin karkarar,yana ganin zallar haukarta,waye zai wani sayi zane?,yayi me dashi?,mutum daya ne take ganin kamar zai mata hanya ko yasan inda za’a siya din,wani abokin nasuru ne da yace mata ya taba zuwa kano,ya wuce ya wani waje yaga an maqala zanw cikin glass ana siyarwa,tunda ya bata labarin bata manta ba,saita yanke ta tanbayeshi ko za’a dace,saidai kash nasurun yace mata baya nan,amma tana sanya ran dawowarshi cikin satin.

Sai daya gama daura takalman sannan ya miqe yana kakkabe jikinsa
“Na tafi yaya,inajin ma yau zan dan dawo da wuri,zan samowa umma wani abun da zata ci,don yau za’a fara biyanmu kudin aikinmu inji oganmu,mun kusa gama rushe ko ina da ina,aikin ginin kawai za’a fara”
“Toh Allah yasa”
“Amin” ya amsa yana yin gaba da dan hanzari,yana tafe yana dan buga duwatsun da yaci karo dasu,yana ji da takalmin sosai,ji yake babu kamarshi.

Tana gamawa wadda takewa kitson kitso ta kakkabe jikinta,ta wanke hannunta sosai sannan ta sake tattara wajen,gidan habiba takeson zuwa,don tun shekaran jiya take aike kan tazo din amma.bata je ba,don Allah ya sani tun asali ita dama ba maison yawo bace,koda cikin qawayensu duk wadda akayi biki da wahala ka ganta ta koma gidan a kusa.

Sai data leqa dakin umman ta tabbatar bacci takeyi,sannan ta shiga nata dakin,ta dauki hijabinta ta maqala sannan ta fito tana dan jan qofar kara da aka sakayawa sashen nasu sannan tayi gaba.

Tana shirin fita asiya na shigowa da uniform jikinta,duk me hankalin daya kalleta yasa ba daga makaranta ta dawo ba,don fes take a nutse,babu wasu alamu dake nuna gajiya da tarin yunwa irin tadan makaranta tattare da ita,kallon banza data saba yiwa kaltum shi ta watsa mata,ita kam bata ma isheta duba ba,don haka kota gefan da take bata kalla ba tayi gaba abinta,abu dayane data sani shine,ba zata dauki ranini ba,sannan a dake asiyan ba zata dauki komai a jikinta ba.

Ta qofar gidan me gari ta ratsa saboda sai tafi mata sauri,tun daga nesa take hangen wasu maka makam motoci da suke zamewa ‘yan karkara irinsu da basu taba leqa birni ba abun tsoro,saboda haske da walqiyar da suke cikin hasken rana,yara da manya ne tsaitsaye gaban motocin guda uku,da alama suna morewa idanuwansu kallon abunda basu taba gani bane,ta haka ta ratsa ta tsakiyarsu ta wuce,tana tafen itama tana waigen motocin,tare da mamakin wai wadan nan abun hawa ne,kuma sunansu mota kamar sauran motocin da suke gani suke safararsu zuwa qauyensu,bata taba zaton ma akwai samfurin wata aba wai mota irin wannan qirar ba,kwata kwata babu hadi da iein nasu motocin,don idan aka kwatanta wadan nan da nasu,toba shakka sunayen nasu motocin gwangwani ko kuma kace fanko kai tsaye,Allah daya gari banbam,da irin wannan tunanin ta qarasa gidan habiba.

Bata sameta a sassanta ba,a sashen surukarta ta sameta,suna zaune qasan rumfarta mai sanyi suna barar gyada abinsu suna hira,fuskarta wasai take fadin
“Maraba da kaltume,kaltume kinyi tsada kamar kudi?,idan za’a leqomu dinma sai munyita roqo?” Tafadi tana miqa hannunta tana warewa kaltum gefan tabarmar da suke kai,tana murmushi ta zauna,cikin kamewa da kunya ta gaida babar yusufa din,ta amsa mata cikin kulawa da dattako,tana tambayarta ummansu da kuma jikinta,ta amsa mata da sauqi,saita miqa hannu ta debo gyadar da zummar tayasu ɓarar.

Dakatar da ita baban tayi tana fadin
“A’ah,ajjiye kada ki bata jikinki,ke habi dauketa maza ku wuce bangarenki,idan na gama dambun zan aiko muku dashi,ba sai kin fito ba” cikin ladabi habiba ta miqe tana cewa
“To baba” dole kaltum ta miqe itama tabi bayan habiban suka wuce sashenta.

Daga tsaye kaltum ta qarewa rumfa zuwa dan tsakar gidan habiban kallo,ko ina fes qal kamae yadda suka gada daga mahaifiyarsu,hakan ya yiwa kaltum dadi qwarai
“Gani,lafiya kike nemana?”ta fadi tana duban habiba wadda tayi qiba abinta,koda ba’a gaya maka ba kasan tana cikin kwanciyar hankali da nutsuwa,duk kuma sanda suka daga idanu suka kalleta ita da ummansu,suna samun wani sukuni da farinciki na dacen gidan aure da habiban tayi.

Kama baki tayi tana kallon kaltum
“Kai yaya?,kamar akan qaya kike?,Allah da yau yaya yusufa cewa yayi indai bakizo ba da kansa zaije ya tahomin dake,shikenan saiki yanke zumunci dani?,watanni nawa da aurena amma har yanzu bakizo min sau uku ba?,bilal kawai fa ke leqoni lokaci zuwa lokaci,ko ummanmu taqi zuwa har yanzu,dama ni bana zancan baba,anya kuwa baku daina sona bq?” Tayi maganar kamar zata saki kuka,hakan ya sanya kaltum nema waje ta zauna tana cewa
“Idan ma mun daina sonki aikin samu wasu sabbin masoyan da suka fimu iya kula da habi ta” maganar ta sanya habiba dariya,da alama kaltum din ta sauko kenan daga niyyar komawa cikin gaggawa datayi aniya,habiba bata zauna ba,saita dinga rakitowa kaltum din duk wata cima da take da ita ciki da wajen dakin,gyada ce,rake ne,ragowar tsirenta na jiya,harda kiifi ma da kantu.

Dukkansu kaltum tana sha’awar ci,saboda an jima ba’a hadu ba,saidai ta kasq cin komai a ciki idan ta tuna ummanta,ba zata iya ci ita kadai ba,duk da cewa habiban na yawan yi musu aike irin wannan na kayan taba ka lashe.

Ganin taqi ci habiban tasan halin yar uwar tata sarai,don haka saita samu leda ta juye mata komai,sannu sannu kaltum ta saki jikinta,suka dinga hira sosai da habi,har babar yusufa ta kammala dambun,ta aikowa da habiba nata cikin qatuwar kula da kaltume ta tabbatar tafi qarfinta,sannan kuma ta ciko wata babbar samira tace ta kaltume ce,miqewa kuwa tayi tace gida zata tafi,ita baci zatayi ba,habiba ta kada ta raya taqiya,har sai data hadota da babar yusufa
“Ke kaltume,karbi maza,keda gidan ‘yar uwarki?,banda ma shirme irin naki a mu yanzu ‘yan uwa ne,babu abinda zance da habiba ni sai godiya,don tq zamarmin diyar cikina ba suruka ba,Allah ua bani ‘ya daga sama,babu abinda zan masa sai godiya,na kuma godewa mahaifanku da suka tarbiyyanceta da kyawawan dabi’u” wannan kalaman suka qarawa kaltum qaunar matar,suka kuma sanyaya mata zuciya saboda yabo da ummanta ta samu.

Ko da tazo dawowa a yanzun babu motocin data gani dazu,hakanan babu taron mutanen nan,sai dai daiku da suke zuwa gidan,wasu matsala ce ta kawosu wasu gaisuwa,haka ta wuce zuwa nasu gidan.

Tun kafin ta isa sassan nasu ta jiyo muryar inna,gabanta ya fadi,me kuma ya kawo inna yau gidan nasu?,ta sani da wuya alkhairi ya kawota,ku kumq tazo a qarke qalau da ita,saita fara jan
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” kamar yadda aka koyar dasu a makarantar asuba ga wanda bala’i y asameshi,don ita a wajenta inna bala’i ce cikin rayuwarsu,domin bata kawo musu kowanne alkhairi face sharri,da tana da iko,da tana kuma da hali data shafeta cikin babin zuri’arsu,ta kuma canzawa ummansu mahaifiya da wata ba innar ba.

Sosai ta tamkae fuskarta,ya aro duk wani bacin ran duniya ta azawa fuskar tata sanda take sallama a tsakar gidan nasu,innar ce kuwa,tana zauna akan kujera ‘yar tsuguno,yayin da ummansu ke saman tabarma,da alama ma zuwan innar ne ya tasheta daga baccin data tafi ta barta tana yi.

“Har kin dawo kenan?”umman ta tambaya tana duban fuskarta,kai kawai ta gyada mata,ta isa gefan umman ta ajjiye kwano da ledar hannunta,sannan cikin cushewa ta soma gaida inna
“Lafiya lau”ta amsa mata,amma idanunta kacokam na kan kayan da kaltume din ta ajjiye
“Nazo akace kina gidan habiba,itama shegiyar da bata neman kowa sai uwarta da yan uwanta…..wannan din meye kikq shigo dashi?,me aka same acan din?,Allah yasa ana qulla abun arziqi itama bata fada irin gidan da uwarta ke ciki ba”innar ta fada wuyanta kamar zai tsinke ya isa ga kwanon,tuni kaltum tasa hannunta ya dafe kayan,don bata jin innar ko mayyace zata bata kayan nan,saidai kallo daya umman tayi mata ta janye hannunta daga kai,don babu yadda zatayi
“Dauka kikai mata”unma ta umarceta,kamar zata sanya hannu aka ta zunduma ihu haka taji,ta jefi innar da harara,saidai ina batasan tanayi ba,zuba surutu take idanuwanta kan kwanon dai,haka ta miqe ta dangware mata komai tayi wucewarta daki abinta,inda tasan zata zo ta taras da ita wallahi ta gwammace tabar abincin bata karbo ba.

Rub da ciki tayi saman shimfidarta,tana jiyo yadda innar keta zuba surutu taga dambu,ga nama harda kifi,tana jin sanda ta saki guda
“Kai lallai ba shakka,habiba Allah ya tseratar dake,ai nima na leqa mu gaisa” maganar tata tadan cunkushe daga qarshe,wala’alla dambun ta cika bakinta dashi.

Tsaki kaltum taja kamar zata tsinke harshenta,ta juyar da fuskarta ta daina kallon qofar dakin wai ko zata rage jin kalaman zalama da tsantsar kwadayi daga bakin innar
“Kema kiyi kiyi ki tattara ki qara gaba,har yanzu shuru,shi yaron da yace adaga masa qafa gashi wata nawa basu sake magana ba,sai kace wadda ta ɓincino baqin jinin ubanta,don dai wannan baqin jinin bana uwa bane,saboda ni kaf yarana babu wanda ke wuce shekara goma babu baiko,itama donta biyewa son raine tazo tq haifeku a wanna qangin” kalaman da suka sanya kaltum miqewa sa sauri ta tura qofar dakin nata ta rufe abinta,sannan ta dawo ta kwanta.

Bata qara miqewa ba sai da taji ummansu na kiranta,ta miqe a hankali taja dankwalinta ta daura,sannan ta fito,ta samu innar ta gama kasafta komai ta dauki nata,dubanta umman tayi
“Ki dauka abincin kici” fuskarta a hade tsaf tace
“Na qoshi,ki qara mata kawai” sarai umman ta fahimci magana ta fada a fakaice,amma batason cewa komai kada innar ta samu wata mafakar,tana son su rabu lafiya,ko banza yau dai ga innar tata a gidanta.

Washe baki innar tayi
“Aina qoshi ‘yar nan,kedai Allah yasa kema ki dace kamar habi” batace mata ci kanki ba bare ta amsa mata,saita gyara zama,sanda ummansu ta miqe ta dauki buta don zuwa bandaki
“Nace ba……zuwa nayi ki bani aron dubu da dari biyar,wallahi jiya jiya ado da indo suka aikomin da kudi,zan siya kiwo,to saura cikon dubu da dari biyar,babarki tace min kina tara kudin magani,ko su zaki aramin,koma dai ki bani kyauta,tunda kukan jima baku yiwa kowa alkhairi ba,na tambaya babarki ko akwai sauran na gudunmawar bikin habiba ta bani,to ashe babu duk kun qurmushe” mamaki ya cika zuciyar kaltum,ta soma bin innar da wani kallo.na mamaki,tana ji har cikin zuciyarta,data dauki abunta ta baiwa innar ta mora,gwara su fadi
“Ina zuwa” kaltum din tace da ita tana miqewa,saita sake washe baki,murna sosai ta cikata
“Allah dai yayi miki albarka,kare ma yana da ranarsa gaskiyar bahaushe” ta fada innae tana gyara zama.

Inda take ajjiye kudin ta soma bankadawa ta debe kudin,ta dauresu sosai bakin habar zaninta,sannan taja hijabinta daya cire dazu ta mayar jikinta,ta saka slipper dinta ta fito.

“Yauwa miqosu nan,sauri nake nayi na koma,na baro gidan babu kowa” tsaiwa tayi saman kanta ya dubeta,saita kwance kudin ta dagasu sama
“Kin gansu nan?,to wallahi sisi a ciki ba zakici ba,saboda gumina ne bana wani ba,aimu marasa amfanine a wajenki,to a tafi a hakan har duniya ta nade,kuma gidan habiba indai kika sake kika je,yasin saina sakar miki karnukan gidan mati dake hanyar” saita sura da mugun sauri tayi waje,saboda taji ummansu daketa doka mata gyaran murya tana gaggawar fitowa,da alamu taji komai a kunnenta.

 

Hanya kawai ta miqa ta dinga shawagi abinta,ta dade bakin rafinsu zaune,abinda bata taba yi ba,saidai wajen yayi mata sosai,batasan haka wajen yake da dadi ba sai ranar,saitaga zai dace da wajen zamanta idan zatayi zane,taga abubuwa da yawa da zata iya zanawa tana zaune daga wajen.

Anan ta shimfida dankwalinta tayi sallar azahar,batason komawa gida a yanzun,saboda wata nutsuwa da wajen ya saukar mata,sai data qara awa guda sannan ta miqe,ta yanke tabi ta wata hanya,duk da batasan ainihin inda zata maidata ba,amma tana da tabbacin xata kaita gida.

Ga mamakinta saita bulla da ita layin gidan yaya muzammilu,gidan da aqalla ta kusa shekara uku rabonta da zuwansa,ta laluba kudinta taji suna jikinta,zuciyarta ta bata shawarar ta kaiwa matarsa lariya ajiya,don haka ta kutsa kai gidan da sallama.

Kadaran kadaham ta karbeta,suka gaisa,bata zauna ba ta kwance kudin tace
“Babar haruna,ajiyemin zakiyi,zan dawo na karba nan da kwana uku” jikinta na rawa ta karba,kudin sunzo mata akan gaba,dama su take nema
“To kaltume,Allah ya kaimu” daga haka sukayi sallama ta juya gida.

Koda ta shiga bata samu inna ba,sai ummansu dake zaune,suna hada idanu umman ta kauda kanta taci gaba da abinda take,tasan ummanta sarai,ta santa ciki da bai,tasan yadda zata saukar da ita,don haka saita zame takalmanta ta isa gabanta ta duqa
“Don girman Allah,don manzan Allah ummanmu kiyi haquri idan kinji haushi,wallahi ummanmu bazan iya bata bane” shuru ne ya ratsa kamar umman ba zatayi magana ba,sai kuma tace
“Idan ba zaki iya bata ba kuma saiki gaya mata maganganu kamar sa’arki?,idam farincikina kike nema to bai samu ba,tunda daga qarshe akaina koma meye ya qare”
“Kiyi haquri ummanmu,kinyafemin” shuru ta sakeyi,kafin daga bisani ta fidda wata ajiyar zuciya
“Allah ya shiryamin ke kulsum” don ta fahimci kaltum din ba zata taba sauyawa ba,saidai addu’ar
“Amin” ta amsa murmush na subuce mata na ganin nasarar data samu ta sauke umman nasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button