Sponsored Links
Bakar Ayah Book 2Hausa Novels

Bakar Ayah Book 2 Page 21-22

Sponsored Links

Page 🖤21••22🖤

 

“Me kike faÉ—a haka Hajiya zeenah bana jinki,aure kuma wanne iri?”
“Hmmm yadda na faÉ—amikinnan haka naji nima,yanzu haka na saka ayimin binciken yarinyar da iyayenta,abu daya na sani shine Æ´ar talakawa ce sosai”
“Talakawa kuma,da girmansa kuma ya É—auko Æ´ar talakawa,ga waccar wadda kika É—auko bata fara aikin komai ba,meyasa abu yake nema ya fita a hannunmu ne kai. To shin bakiyi Æ™oÆ™arin hanashi ba kuma?”
“Uhm hakan bazai yiyu ba sam,domin duk abinda nake abbansu baya sakamin hannu,amma wannan karon yatsaya akan idan bai ga wata matsala ba,to zai aurawa Jabeer zabinsa.
Ni inaga mu zuba ido muga shin mai zasuyi kawai,idan an saka bikin kafin JAWAHEER tagama makaranta,to saimu matso da natan,idan kuma sun saka dayawa saimu jira”
“Ai babu wani zancen jira,makarantar banza makarantar wofi,Ki bari muji wanne lokaci suka saka muma sai mu saka daidai dashi.
Batun ita yarinyar kuma,saimu ƙarawa waccar yarinyar kuɗi tayimana dukkan maganinsu kafin ta tafi.
Ya kikaga hakan toh,kinga in ta gama dasu itama ta tafi,shikenan mun huta,makaranta kuwa idan so take,ko Æ™asar wajene ma ai sai ya kaita tayi”
“Eh hakan yayi sosai,bari na zuba musu ido su gama shirin,sai ranar auren yaji mai na yanke”

Daga inda yaron drivern yabar su innayi basu motsaba,sai faman aikin neman Jakarta take,amma babu ita babu alamunta,haka ta gaji tabar neman ta fawwalawa Allah.
Alfijir ne yaketo gari ya fara haske,mutane masu rumfa a wajen,musamman ma Æ´an abinci sun fara fitowa.
Wajen wata mai abinci innayi taja Danejo suka nufah,domin samun ruwan Sallah.
Daga ganinta musulma ce,amma kuma batayi kama da bahaushiya ba.
“Amm barka da safiyan Madam,dama ruwan sallah muke nema nida innata ko zaki taimaka mana dashi?”
Kallon bakusan mai kuke ba tayi musu,tareda cigaba da hura wutarta.
Maimaita maganar innayi tayi,wannan karon maimaikon tayi shuru,masifa tafarayi da hausarta wacce bata ishi bakinta ba,gwanda ma ta innayin mai surkin fillanci.
“Ke yarinya bani wajenan idan ke bakida aikinyi,ruwan haka yake a banza kaman kogi,kuÉ—i fah na saka na siyah”
Hannun innayi Danejo taja,alamar tazo su tafi daga wajen.
Hanyar wani layi suka nufa,suna tafiya kaman bazasuyi ba,abin duniya duk ya ishesu.
“Inna Danejo yanzu kenan a in zamu samu Addah Bombee,takardar ma ta faÉ—i banganta ba,gashi bamusan kowa ba a garinnan. Abu É—aya na rike a takardar shine JAAN Estate,bayanshi na manta komai a jiki”
Tafiyah suka har aka fara shiga Sallah a masallatai.
Wani masallaci suka kawo sun shiga Sallah.
Ranadar masallacin innayi ta nufah ta É—ebomusu ruwan a cikin butar da tagani a wajen.
Kawomusu tayi sukayi alwalar suka sha sauran.
Zaninta ta shimfiÉ—amusu sukayi tada sallah. Suna cikinyi mutane suka fara fitowa daga masallacin,kasancewar haske yafara kowa yana kallonsu.
Wani dattijo ne suka fito daga masallacin shida wani matashi suna magana.
Idonsa ne yakai kan su innayi wanda suka sallah a harabar masallacin,tsayawa sukai suna kallonsu har suka gama.
Innayi ce data kuladasu ta taso ta ƙariso wajensu,tsugunnawa tayi har ƙasa ta gaishe da dattijon kafin saurayin.
“Lafiya yarinya na ganku anan,maikuke anan wajen da wannan lokacin,sannna kuma da alama ku baÆ™ine koh”
“Eh baba mu baÆ™ine,munzo neman Æ´ar uwata ne nida innata,saikuma mukayi rashin sa’a wasu suka É—auke mana kuÉ—inmu a mota,shine mukazo nan domin muyi sallah saimu samu inda kuma zamu nufah”
“Innalillahi ana gamuwa da bata gari kam sosai,shin inane ita inda yayarta ki take?”
“Ehh takardar data bamu na address É—in itama ta bata,abu É—ayah na sani a jikin takardar shine JAAN Estate”
“Wai yarinyar taya zamu gane kawai daga suna gidan,inda akwai address É—in anguwarne dai da dasauÆ™i toh”
Jimm Innayi tayi daga inda take tsugunne,tarasa ma yake mata daÉ—i,inda zasu nufah ma shine babban tashin hankalin ta. Daga cikin tunanin tajiyo muryar dattijon
“Tunda kince baki san kowa ba,sannan kuma babu kuÉ—i a wajenku ballantana ku koma,gaki É—iyah mace ita kanta innartaki naga kaman bata gani”
“Ehh baba bata gani sannan kuma bata magana,saidai tanajin abinda ake faÉ—a”
Jijjiga kai yayi cikin halin tausaya musu.
“Idan bazaki damuba akwai gida gefe da masallacinnan,yanada Æ™ofah tawaje da kuma ta cikin gidana,daki daya ne dashi sai banÉ—aki.
Ku shiga keda innartaki ku zauna,zan saka yusufu ya bincikomin inane jaan Estate ɗin sai ya kaiku,tunda shima tuƙin Taxi ɗin yakeyi.
Ku zauna wajen yafi muku yawon da baku san hannun wa zaku faÉ—a ba. Inyaso sai ki dunga É—ebo mana ruwa kina gyara masallaci dakulada shi kafin lokacin,dama maiyin aikin yarone ya tafi makaranta,sauran yara kuma sun zama na zamani”
Tun kafin ya gama bayanin innayi ta tsugunna tafarayi masa godiya kaman zata kifa,saida ya dakatar da ita tukunna.
Wajen inna Danejo ta nufah ta shaida mata abinda mutumin yace,da farko taji jimm kafin ta ɗaga kanta,amma kana ganin fuskarta kasan bataji daɗin yanda suka ƙare ɗin ba.
Dakansa ya Mlm Tijjanin yaraka su gidan,dama na mahaifiyar sa ne data rasu.
A lokacin innayi tashareshi ta shimfiÉ—amusu tabarma a ciki wacce ya aiko yaro ya kawomata,ta gama gyaran kenan aka sake turo musu da É—umame na abin karyawa.

Wasa wasa anyi sati guda da dawowar Lubnah sabon sashe.
A iyah wannan lokacin anyi abubuwa da dama,ciki harda tambayo wa aure da aka yiwa Jabeer,take aka saka rana nan da wata uku. Itama hajiya rabi tana jin haka tace a haÉ—a dana Æ´ar ta.
Nan da wata uku kenan za’ayi tare,lokacin da Lubnah taji wanann zancen Æ™aramar hauka ce kawai batayiba,musamman ma zancen Jaleelah wanda bata san dashi ba.
A bangaren Bombee kuwa hakan zai wani dameta ba,tayi sati É—aya kenan a gidan,dan haka lokaci yayi dazata fara nata moving É—in.
A zaune suka a harabar da yamma suna duba bayanan da khamees ya turo ma Bombee É—azu.
Wajen a ƙawace yake da kujeru da kuma rumafah irinna zaman shaƙatawa,da alama dai domin zama a huta akayi shi.
Su ukune a wajen,Hilyaan Bombee saikuma Haidar wanda yake cikin Holding bed É—insa yana wasa a gefensu.
Shuru kakeji dukkansu babu wanda yayi magana,sun maida hankalin su kan document É—in dake gabansu.
“Anty maryam banji kinyi zancen sabin amarennaki ba dazasu zo”
Hilyaan ta faɗa cikin sigar zolayah,kallon rabin ido Bombee tayi mata tareda yin ƙaramin murmushi.
“Wai meyasa Hilyaan kike abu kaman baki san komai ba uhm,dama nasan da zuwan Jawaheer koba daÉ—e da jima,amma kuma itama Waccar É—in nayi tunaninta tun ranar dana ganshi yana duba Sashen dayake kusada shi.
Na gansa kusan sau uku yana shiga wajen shida wasu ma’aikata yana dubawa,sannan kin manta lokacin da Lubnah take da faÉ—an bai kwana a gidannan ba?,na tabbata ba a gidan Su Jawaheer ya kwana ba,saboda kallo daya zakayiwa sha’anin kasan cewar ba soyayya a tsakani,Hajiya zeenah da kawartane suke rawarsu suke kiÉ—ansu.
Da farko nayi zaton a gidan su yarinyar ya kwana,danayi bincike jiya kuma na gano gidansu sunada kamala sosai,to É—ayan biyune yake faruwa……”
“Kutt taya kika shirya waÉ—anann labaran,É—ayan biyun wannene”
“Ko akwai wajen wata daban dayake zuwa idan yana cikin matsala,ko kuma akwai wani waje boyayye dayake zuwa,wanda bayason kowa yasani,a yanda kuma naji labarin a mutuwar matarsa Hafsa an rasashi a gida na wani lokaci kafin ya dawo cikin mawuyacin yanayi.
Tabbas akwai wani abu dayake boyewa wanda babu wanda yasani,harda iyayensa ma”
Tafi Hilyaan tafara yiwa Bombee na alamar jinjina,sanann kuma takara dacewar.
“Gaskiya na jinjina miki,amma inaga wannan binciken da a akan Lubnah da familynta mukayi,ba’a kan Jabeer ba,saboda naga kaman baya cikin target É—inmu koh?”
“Baya cikin target É—inmu a zahiri,amma a boye shine babban target É—inmu.
Kowa dayake cikin wasannan ƙarshen target ɗinsa kan Jabeer yake yin birki.
Hajiya rabi nata shirin shine ƴarta ta aureshi ta haifi ƴaƴa,itama kuma hajiya zeenah shirinta shine ta haɗe companyn hajiyah rabi dana Jabeer saboda JAAN yaƙara power.
Ita kanta Lubnah ba itace ta haÉ—u da Jabeer ba,iyayenta ne wanda suka haÉ—a komai,domin itama ta haifi Æ´aÆ´a a gidannan,dasuka ga bazata haihu ba sai Gen Abdu manga yakeson Mallakar companyn yanzu.
Kuma ina mai tabbatar miki kwanan zai fara moving É—insa akan hakan. Sannan shikansa gidan da kike ganinsa akwai Akwai abinda yake going a cikinsa.
Zaro ido Hilyaan tayi tareda cewa.
“Ba…..bbban fahimceki ba Anty maryam”
“Meeting É—in dayaje a wancan satin Gen Abdu manga shima yaje wajen,kinsan meyasa?”
“Ahah bansani ba?”
“Saboda shine nabiyu mai kaso mafi yawa na share companyn,a kowanne lokaci zai iyah Æ™arbe shi daga hannun Jabeer”
“To abin da É—aure kai,saboda taya Zasu bar wani yayi kusa da mai company a yawa share?”
“Ba a mutum É—aya ya siya share É—in ba,ya mallakesune da sunayen mutane a Æ™allah Gudan goma,kuma shima kansa Juyashi ake yakeyin aikin, babban kifin yana duhu,shiyake juya komai.
Alhj Abdullahi ƙafafa yake yana tunanin shine da babban share na companyn,saidai ba haka bane.
Wannan ne dalilin dayasa matarsa take Nata aikin da daddare batareda kowa ya sani ba a boye,da alama mijinta take tayawa yaƙi.
Tohhh kinga anan wajen shin wanene Target É—inmu idan muna son ruguza kowanne?”
“Jabeer!!!!”
“Done Plan yayi solving toh”
“Amma taya zamu solving a kansa,shi baida laifin ballantana mu kamashi”
“Akwai hanyoyin saka mutum a cikin tafin hannunka,basai da Laifi ba kokuma Soyayya”
“To taya zak…….”
“Wait and see Hilyaan,lokacin zai faÉ—amiki koma menene”
Suna shirin tattarewa yamma tayi motar Jabeer tashigo harabar wajen baƙa siɗik da ita ƙirar daraja.
A hankali yake tuƙin irinna ƙasaita har ta kaita wajen parking inda sauran motocin suke.
BuÉ—ewa yayi ya fito tareda nufar hanyar sashensa,maganar Lubnah ya jiyo wacce taji muryasa tafito daga sashenta,shi duk yayi zaton ma bata gidan tunda taji labarin auren dazayyi.
English wear ne a jikinta tasha ado sosai,tundaga nesa take fuÉ—emasa baki kamar gobar auguda,saidai daga yanda take dariyar zatakasan cewar bahar zuciyarta bane.
Takowa take cikin tafiyar mai son jan hankalin wanda ake yiwa.
“Honey ina kuma zakaje,tun É—azu fah nake jiranka,kuma saika wuce batareda kaga ya nake ba koh”
Tayi maganar cikin karayar zuciya,dan ita gabaÉ—aya a tunanin ta sashen Bombee zai shiga daya nufi wajen.
A yanda tayi abun kwata kwata bayyi mata kyauba,shikansa Jabeer sakin baki yayi yana kallonta, “Mata iyayenmu” yafaÉ—a a ransa.
Kasa rike dariyarta Hilyaan tayi,ganin tafiyar da Lubnah takeyi,aikuwa tunda babu wanda ya É—auremata baki tasaki dariya.
A tare Jabeer da Lubnah suka juya inda Su Bombee suke zaune,danshi sai yanzu ma yagansu.
Idonsa akan Bombee ya sauƙa,wadda fatarta take sheƙin yamma,ga kayan sun amshi jikinta sosai.
Gajeran kallo ta aika masa na dan mintuna tareda murmushi,kana kuma ta maida kanta kan system .
Kansa É—aurewa yayi,yarasa shin murmushin dawa take,dashi take data kalleshi kokuma da abinda Lubnah tayi ko ga mai aikinta.
“Kuttt yaushe har kina matsayin Æ´ar aiki kika samu damar yin dariyah a inda nake,yau saikin faÉ—amin dawa kike,barganin kina aiki a Æ™arÆ™ashinta kuma tare kuka zo,ko uwarta ce bazan É—au raini daga gareta ba ballantana ke”
Hilyaan ce ta kalli Bombee wacce bata É—ago ba,amma kuma fuskarta ya nuna Ranta tafasa yake,dan ita kanta Hilyaan sai tayi shakkar fuskartata.
Takowa Lubnah tayi zuwa inda suke.
“KifaÉ—amin dawa kike a wajennan dahar kika samu damar dariyah,ko wacce kike zaune dominta bata isa ballantana ke”
Yanda Lubnah take maganar ne da izzah yabawa Hilyaan haushi,É—aure fuska tayi ta tashi zata mayar mata martani(abin sojoji ya motsa).
Tun kafin ta miƙe taji shugabar tata tayi magana.
“Don’t,ke yanzu in kare marar sarka a wuya yayi miki haushi saiki juya ki rama?”
ÆŠan murmushi Hilyaan tayi bayan ta watsawa Lubnah kallon baki kaiba.
Hakanne yasake ƙuleta ta hassala zata fara faɗa.
Buga tebur ɗin Bombee tayi tareda miƙewa suna kallon kallo a itah.
“Lubnah kowa kike ya isheki haka,da akayi kason haÆ™uri kaÉ—an aka bani,to tun É—azu zakika zageni kika ÆŠebeshi,karki bari ki shiga list É—ina tun lokacin shigarki bayyi ba,hakan bazayyi miki daÉ—in.
Kije can ga mai riÆ™e da igiyarki yana jiranki,idan kika tasarmin yaro daga bacci wlh bazakiyi baccin daren yau ba. Idan kina musu try me please”
Yanda take bata saƙon kausashe nan da nan yakai inda takeda muradin yaje.
Jabeer ne yayi gyaran muryah bayan gama jawabin Bombee É—in.
Tunda suka fara ƴar tsamar yana tsaye ya haɗe hannu yana kallon su,haka kawai yaji yanada buƙatar yasan wacece amaryar da mahaifiyar sa tayi masa,idan yanada buƙatar hakan dole sai ya matsa jikinta yasan ya take.
Beside tunda zai haÉ—a mata huÉ—u,dolene ya dunga tsayawa yana ganin mu’amalar dake tsakaninsu. Duk da yasan dana ba kyau zatayi ba koda yace zayyi koÆ™arin gyarawa.
ÆŠan jijjiga kai yayi bayan ya kalli inda yaron yake kwance,babu abinda yake tsaye a ransa kaman zancen yaron,ko ya akayi ta samu yaron tabbas yanaso ya sani dole.
Ba su Bombee ne suka bar inda suka zaune ba har sai wajen magriba tukunna,zuwa lokacin sun gama tsara yanda komai zai tafi..
Misalin wajen ƙarfe tara khamees yaƙirata,ɗauka tayi batace komai,komai ya faɗamata daga ɗaya bangaren ta tashi da sauri ta zauna.
“Me kake cewa? Inna da innayi sun gudu daga gida sunzo nemana? Ohh shittt ya akayi ma ban Æ™ira Muruje naji ya suke ba…..tsawon wanne lokaci….”
“Sati É—aya,shin kana ganin suna cikin garinnan kuwa?”
“Ehh to in suna cikin garin yaci ace ai sunzo wajenki koh,tunda kince kin bawa inna Address É—inki”
“Hmm ba lallai sunada address É—in ba,in babu damuwa inaso ka É—an nemo min clue na inda suke, kasan basu taba fitowa ba sai wanann karon,kada a samu matsala”
“Ohk shikenan kada ki damu,inshaaallah baza’a samu matsala ba”
Jefah wayar tayi akan gado tareda zama ta dafe kai na É—an wasu mintuna,da taga hakan bazai mata ba ta barbaza gashin kanta tareda jan gwauron numfashi.
“Why innayi mainene haka yasakaku baro gida ku biyu meye dalili ,wa yace kuzo nemana,inada dalilina na barin inna a can,meyasa zaki kawo ta nan? …..to inna laari fah taya innayi zata gudu lokaci guda ta………….akwai abinda yake faruwa,É—ayan biyu.
Tabbas innayi taga abinda Inna laari take,ko taji zata kashe Innnata ko kuma zata kasheta itah.
Shiyasa suka gudo nan kenan?”
Ta daÉ—e ita kaÉ—ai tana maganganu kafin ta tashi tanufi bayi..
Ruwa ta watsa a jikinta saboda zafin da ake,da alamar hadarine yake haÉ—uwa.
Kayan Patrol tasaka baƙaƙe misalin Wajen sha ɗaya zata fita.
Karo sukayi da Hilyaan tazo dama madarar Haidar,saboda kada ya dameta da kuka.
“Anty maryam lfy ina zakije haka da Darenan ana shirin yin ruwa?”
“Wani wajen zanje,yanayin a haka yafi daÉ—i ai,bakiji ance Duhun Damina itace sa’ar barawo ba,to hadda irinmuma masu bincike.
Waje tafita tabar Hilyaan a tsaye kaman gunki,dan ita yanzu ta daina bata mamaki ma sai tsoro.
Kai tsaye sashen su Lylah ta nufah,kaman yanda tayi tsammani kuwa akwai hasken fitila a store É—in wajen.
“Yaune 18 ga wata,baki saba ranar da kika saka ba rannan kenan?”
Daidai kaiwa kunnenta taji ana magana.
“Ga takardun yabani,ka tabbatar ka musanya takardun project É—insa da waÉ—annan,karka taba bari a samu matsala,kaine secatrynsa nasan ya yarda dakai sosai bazai zargi kaine ba.
Na zabi haÉ—uwa dakaine anan saboda Karka a ganni a wajen na haÉ—u dakai,ka fahimta dai koh?”
“Ehh na fahimfa Hajiya,amma wannan abun fah hadda mijinki da duk companyn zai shafa,domin zai fita ne daga hannunsu ya koma wani wajen daban”
“Ina ruwana toh,nidai tunda zai biyani maÆ™udan kuÉ—aÉ—e ko gidannan ya karba mana ina ruwan ni.
Ina ganin kuÉ—aÉ—en a hannuna zanyi fiyattt na bar Æ™asar shikenan”
“Uhm zan fita ni yanzu,idan nayi mintuna goma da tafiya saika bar wajen,saboda kar in case wani ya ganmu”
Tana gama faɗin hakan siƙaf siƙar ta maida lullubin kanta ta fita.
Saida Bombee tajira tabar wajen kafin ta shiga cikin store É—in inda mutumin yake tsaye.
“Madam akwai wani abune bayan……”
Tun kafin ya gama maganar Bombee ta kifah masa naushi a fuska,faÉ—uwa yayi yana dafe ta inda takai masa hari.
“Bani takardun Yanzunnan”
Tafaɗa tana miƙa masa hannu.
“Wacece ke?”
“Shine yafimaka amfanin ka sani a yanxu,zaka miÆ™omin takardun ko saina cewa wannan ya aikata abinda na sakashi”
Takarisa maganar tana nuna masa matarsa da ƴarsa an sata wuƙa a wuyansu suna bacci a gida.
Zaro ido yayi jiki yana karkarwa ya miƙa mata file ɗin.
“Yawwa yaron kirki,yanzu kaje gida ka kwanta da iyalanka sannan kuma kace mata kayi yadda tace,idan kuma tasake saka ka wani aiki ka tabbatar saina sani tukunna.
Kuma daga koda wasa naji kayi wani abun dazai cutar da companynnan saina saka fetur kuna bacci na Æ™oneku. Dafatan ka jini sosai”
“Ehh…. Aradu na jiki,in so kike ma zan faÉ—amiki duk abinda nasani yanzu da kuma wanda yake sakamu,nidai kiyimin lamuni nabar garinma”
“Babu inda zakaje kana nan,batun wanda yake sakaku kuma nasan waye yake shi basai ka bata yawun bakinka ba”
Hanyar side ɗinsu ta nufah,zuwa lokacin har an fara yayyafah mai ƙarfi.
A ledar data zo ta ita ta saka takardun sannan tafara gudu gudu sauri sauri zuwa sashensu.
Kasancewar da ɗan tazara kafin ta isa har ta jiƙe zaraff,daidai shigowarta harabar wajen ta cire baƙar hular da take kanta,jiƙeƙƙen gashin kanta ya kwanta a fuskarta da ƙafaɗarta..
Hannayenta ta ware a cikin ruwan yana bin ko ina a jikinta,komai ta tuna ita kaÉ—ai tafara murmushi idanuwanta suna rufe.
“Hmmm fashi kika iyo mana a cikin gida na ganki da kaya irinna barayi?”
Cikin sanyi yayi maganar a kusan kunnenta,dayaga har ya zo kusada ita batasan yana wajenba,ta tafi duniyar tunani.
Zabura tayi zata matsa sulu ya É—ebe ta,dan bata tsammaci kallon É—an adam a wanann lokacin ba,hakan ma kuma kusada ita,bataji motsin zuwansa ba saboda ruwan da ake.
Saurin riƙota yayi ya ranƙwafah bata kai ƙasa ba..
Kallon fuskarta yake wadda hasken ƙwoyayen wutar wajen suka haske.
Yayinda itama shiÉ—in take kallo da nata zararrun idanuwan.
“Sakeni”
Tafaɗa a kausashe,bayyi mata musu ba kuwa ya saketan,jin tana shirin Kiss ta ƙasa yasaka ta jawo rigarsa suka faɗi tare cikin ruwan.
Tashi sukayi tana riƙeda hannunta wanda ya bugu,kallon hannun yake yanda tariƙe gwiwar wajen,kuma shima yaji ƙarar da hannun yayi.
“Am sorry barina gani”
“Kaga me,saikace kana magana da Æ™aramar yarinya,ai duk laifin ka ne,menene na zuwa kusada ni kayi magana”
“Dannaxo kusada ke nayi magana sainace kiji tsoro,ke mekike a tsakar dare da baÆ™aÆ™en kaya?”
“Ina ruwanka da abinda nake zaman ka nake komai,saika barin in kaji ance an sace wani abu ko yanka wani gobe,saika tuhumeni”
Hannunta takama da ɗayan taja saida yayi ƙara,jijjiga shi tayi tareda miƙewa tsaye.
Duk abinda take Jabeer yana kallonta,yanda tagyara buguwar tashi É—aya yasa ya share tantamarsa,tabbas ta taba aiki a wani wajen masu horon.
“Baki faÉ—amin sunanki ba miss sannan kuma idan bazaki damu ba inason mu haÉ—u akwai tambayoyin dazan miki,sannan haka kike a kowanne lokacin bakya shakkar nuna sassan jikinki a gaban mutane,hmmm ba mamaki naga hadda sakamakon hakan kikeda shi.
Juyowa tayi cikin ƙosawa,takowa tayi har zuwa inda yake.
Gabaɗaya kayan jikinta sun lafe kana ganin komai nata a fili,sakamakon ruwan daya jiƙa ta jarabb,wata tafiyar girgiza take da gangan wacce batayiba ɗazu.
Tsugunnawa tayi a inda yake zaune bai tashi ba.
“Mutum yagani ya Æ™yasa ma bai da ikon tabawa horone,ohh dama karkatacciyar bishiyar kuka ka É—aukeni mai daÉ—in hawa ga kowa,wai ……..to tun dare bayyimaka ba ka sanja wannan karatun gamedani.
Ni bishiyar giginya ce,sai jarumine zai iya kaiwa Æ™arshe bai faÉ—o ba. Batun É—ana kuma kama dauke kanka daga gareshi,in ma bincike kake ka gano ubansa ba samu zakayi ba,nice nan mai shi ba wani ba”
Bata bari Jabeer yaƙara cewa wani abu ba ta kama hanyar sashenta,har tayi nisa ta juyo ta kalleshi,zuwa yanzu an fara taƙaita ruwan.
“Husbyy in magana kake so dani zanzo gareka,kawai Æ™ira na zakayi zaka ganni,zan turo maka numberta byeee”

 

_*SADI-SAKHNA CEH*_

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK 2_ 🖤

 

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

 

Anshiga Sashen na KuÉ—i,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka É—au hakkina bisa kanka tamm!!!

Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin

https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31

Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150

Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU

Mutanen niger kuma zaku biyah kuÉ—inku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150

______________****_______________

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button