Bakar Ayah Book 2 Page 1-2
Page 🖤1••2🖤
Tafiyah suke Jabeer yana binsu a baya bataresa saninsu ba har suka kai gida.
Kallon ƙofar ya tsaya yi yana nazarin tsarin gidan daga cikin motar.
Wai dama akwai irin waÉ—annan gidajen a garin abuja?? Kodaga nesa mutum zai gane yanayin rashi da ma’abota gidan suke dashi.
Katangar gidan duk ta zube ta wani wajen saboda rashin ƙarfinta,kuma ya haɗu da yawan ruwan sama dayake kwaranyah a kanta na tsawon lokaci.
Kofar gidan babu wani ishashshen makari,wani langa langane a gefe,da alama dashi ake amfani wajen kare gidan da daddare.
A taiƙacedai gidan na masu ƙaramin ƙarfine sosai.
Numfasawa Jabeer yayi bayan ya gama kallon gidan,inda ba biyota yayi ba yaga tashiga gidan,bazai taba cewa daga nan ta fito ba.
Abinda yafi bashi mamaki shine yanda taƙi karbar taimakonsa,bayan kuma tana rayuwa a gida irin haka.
Fitowa yayi daga cikin motar ya nufi gidan,waigawa yake domin samun wanda zai aikata cikin gidan,idonsa ne ya sauƙa kan wani yaro yana riƙe da kwanon a hannunsa,fuskarsa dama dama da miyar tuwo,da alama tunna jiyane,dan tuwon bayyi kamada wanda aka dafashi sannan ba.
Cikin É—auke kai daga kallon fuskar yaron ya fara magana.
“Uhm mutumina nace zona aikeka mana,shin nanne gidan su Jaleelah koh?”
“Eh nanne gidan su ina anty hafeezah koh?”
“Eh inaga itace,shiga kace ina sallama da mahaifinta idan yana nan”
“Nawa zaka bani to idan na Æ™iramaka shi?”
Mamakin maganar yaron Jabeer yayi,yanzu wannan yaron har yakai bazayyi abuba sai an biyashi?
“Karka damu shiga ka kiramin shi tukunna”
Hanyar gidan yaron ya nufah,bayan wani É—an lokaci sai gashi sun fito tareda wani farin dattijo mai kamala da dattaku.
Gaisawa sukayi cikin mutunta juna,maganar yaronce ta katsesu da cewa wani abu bayan sun gaisa É—in.
“Malam baka bani kuÉ—in ba toh”
Kafin Jabeer yayi magana Dattijon yace.
“Wanne kuÉ—in za’a baka,har yanzu baku bar wannan É—abi’a ba koh,ohhh wai yaro baisan a sakashi abu ba sai an bashi kuÉ—i? Wuce ka tafi gida”
Da sauri yaron ya wuce yana zumbura baki,sai bayan ya tafi tukunna Dattijon ya dawo da kallonsa kan Jabeer.
“Yaro baka faÉ—amin mai yake tafe dakai ba har yanzu”
“Ehh dama yarinyar gidan na buge da mota a can kan titi,nayi mata magana mutafi asibiti a duba taÆ™i amincewa,shine nazo naji shin lafiya dai koh?”
“Jaleelah kenan kake nufi,dan itace ta dawo daga makaranta É—azu,data shigo kuma batace komai ba,babu wanda yasan mai yafaru”
Kasa boye mamakin sa yayi jin wai batace komai ba a gida,kulada hakan da dattijon yayi ne yasashi cewa.
“Yaro karfa ka damu,haka take dama ta saba,kuma tunda har bata nuna ba inaga ba wani abin damuwa bane sosai,kayi tafiyar ka zanje na dubata inna shiga gidan,mungode sosai da kulawarka Allah ya tsare gaba”
Kuɗi Jabeer yafitar ko ƙirgawa bayyi ba ya miƙawa mutumin,tun kafin ya kaishi kusada shi ya ture hannunsa tareda cewa.
“A’ah karma ka É—orawa kanka nauyi akan wannan,kayi tafiyar ka babu komai kaji yaro”
Daga haka ya shige gida yabar Jabeer a tsaye,dama ana samun irin waÉ—annan mutanen har yanzu,basuda shi amma kuma sunada wadatar zuci?
Kallon sama yayi ganin rana tayi shirin faɗuwa,gari yafara duhu,yasan zuwa yanzu wataƙila Hajiya zeenah sun dawo.
Wani idan su Hajiya zeenah sun dawo yanzu,toh fah lubna zataji labarin auren da aka É—aura masa,kuma yasan da gangan Hajiya zeenah zatayi abinda zata san da É—aurin auren.
Wai yazayyi kenan bai faÉ—amata ba saidai taji a wani wajen,yasan tashin hankalin dazai tarar ba kaÉ—an bane.
Saurin dafe kansa yayi,zuwa É—azu daga haÉ—uwa da waccar yarinyar har ya manta da damuwar dayake ciki,ya shanye lokacinsa a nan wajen.
Hanyar inda ya ajiye motarsa ya nufah da sauri,yana bata wuta kuwa yanufi gida,a ransa yana addu’ar Allah yasa Hajiya zeenah basu dawo ba tukunna.
Tun kafin ya isa sashen Hajiya zeenah ya hango mutane a wajen,wanda hakan yabashi tabbacin ta dawo kenan.
“Tafaru ta Æ™are….”
YafaÉ—a cikin kasalalliyar muryah,fita yayi a motar ya nufi sashennata,yasan dole amryar da akayi masan tana sashinta yanzu,tunda baici ace an gama gyara ainihin sashennasa zuwa yanzu.To ma shi baiga wani dalilin komawa wannan sashen ba,kawai dai rigimar Hajiya ce.
Da Maleekah ya haÉ—u a falon ta É—auko faranti a hannunta zata shiga É—akin Hajiyan.
“Ke zo na tambayeki”
Cikeda tsoro da kalleshi,fuskarnan a tamm da ita babu alamar fara’ah.
“Yaushe Mommah ta dawo,tana ina kuma?”
“Uhm batafi minti talatin da isowa bama,tana daÆ™inta itada amaryar”
“Amarya,kowa yasan da zancen amaryar kenan?”
“Eh mommah tana shigowa ta tara dukkan ma’aikata ta shaida musu cewar kayi sabon Aure yau,kuma dama tana nemanka idan ka dawo”
Dafe kansa yayi ta gefen dama,jin É—anyen aikin da mahaifiyar tasa ta aikata masa a karo na babu adadi,ko shakka babu yasan da gangan tayi hakan saboda lubna ta sani.
Bai sake kallon inda Maleekah take ba ya wuce É—akin Hajiya zeenah,itama binsa tayi a baya,dan dama can zata nufah.
A can ƙasan maƙogaronsa yayi salllama kansa yana kallon ƙasa,kana ganin haka kasan yana cikin yanayi marar daɗi.
A É—aya daga cikin kujerun É—akin ya zauna,yaga alamar wata farar mata a zaune gefen Hajiya zeenah suna magana,amma ko kallonta bayyi ba,dan yasan itace matar da aka aura masan.
“Ahh Jabeer kaida nace ka kira su Madeenah ka shaida musu zuwana sai yanxu ka shigo”
“Nasamu wani É—an Æ™aramin hatsari ne a hanya”
“Ohh to Allah ya tsare na gaba,shin an gyara sashennaka ne ko kuwa har yanzu”
“An gyara saidai bansan ko sun gama ba,amma naga wancan É—inma danake ciki akwai parta empty a ciki”
“Nasan da haka,akwai dalilin daya saka na zabi wancan É—inne,kuma nasan kaima kasan dalilin. Yanzu dai ba wannan ba,mun taho da baÆ™i,wannan itace……..”
“Please dan Allah mommah kibar wannan bayanin,inkin faÉ—ama ba ganewa zanyi ba,inade part ne,za’a gyara taje da zauna kaman yanda kike buÆ™ata,daga nan kuma fah saime takeda buÆ™ata”
Cikeda bacin rai da ƙosawa yayi maganar,shuru Hajiya zeenah tayi,dan ita kanta tasan takai ɗannata bango,amma shima bazai gane bane,kullum cikin fargaba take da matarsa,gani take da dai da rana dayah idan ta zauna tayi shuru lubna zata cutar mata da ɗa.
“To naji,dare yafara nasan ka gaji,kaje ka huta sannan ka sanarwa matarka cewar yanzu ba ita kaÉ—ai bace,karta sakankance kamar da”
Har yakai bakin ƙofa yasake juyowa ya kalli Hajiya zeenah.
“Amma mommah shin indai yanda kuke faÉ—an haka take,bakya ganin cewar itama wannan bazata……..”
“Kaga ya isa haka kaje saida safe,sannan karka sa damuwar wannan auren cikin ranka,yanada dalilinsa daban wanda bai shafeka ba”
Akwai tambayoyi a cikin kansa kala kala,amma yasan koda yayi su bata lokacinsa kawai zayyi,dan haka yabarsu a zuciyarsa kawai ya fitah.
Jan numfashi Hajiya zeenah tayi bayan ya tafi,maida kallonta tayi kan Hilyaan wacce take zaune hankalin ta kwance akan kujera tana kallon abinda yake faruwa.
“Kiyi haÆ™uri fah nasan munyi tafiyah kun gaji,shi abokin tafiyar taki ankai shi masauÆ™in baÆ™i,ke kuma zaki iya kwana a É—akin Madeenah,ko kuma a baki É—aki daban”
“Ahah karki damu Hajiya,duk inda kika bani ma ya wadatar,na kwana ukune ai kawai kafin Anty maryam tazo,sannan ma ba zama mukazo yi ba ai,zamu fita kasuwa ne da khamis gobe”
“Medame kuke buÆ™ata haka,babu ba abinda zaku siyah na kayan gida,gyaran daza’ayiwa part É—in komai za’a saka shi”
“Eh dama ba wai kayan normal na gidaba,akwai abinda take buÆ™atar a saka na ra’ayinta ne,……
Uhm wannan shine Angon Antyn?”
Hilyaan tafaÉ—a,badan komai ba saidan ta kawar da zancen da ake a lokacin.
“Eh fah shine,amma bawani buÆ™atar ta sanshi ai ko ya santa,kafin tazo zanyimasa bayanin ainihin dalilin auren,karku damu da wannan”
Hmmm ba laifi kyakykyawane kam sosai,kaman yanda itama take mai kyau,ina gujemiki aikinki yajuye ba yanda kike so ba. A fili kuma tace
“Ahh babu wani abin damuwa sosai,naga shima bayada interesting akan auren,ko kallon inda nake bayyi ba,yayi zaton inaga nice amaryar”
Hilyaan tafaɗa ɗauke da ɗan ƙaramin murmushi akan fuskarta.
Kayan marmarin da Maleekah ta kawo ta ajiye tafara ci. Dan ita iyani mai aikace aikacen sashen a gajiye take saboda bidirin da suka sha.
“Hmmm da alama wannnan yarinyar da Hajiya ta auramin batada kunya ko kaÉ—an,wato tafi Æ™arfin gaisheda mutane ma,oh kodayake hakan ma yafiye mata,dan wahala zata sha idan tayi Æ™oÆ™arin shiga rayuwata”
Yana cikin zancen zuci bai sani ba yanayinsa a fili,har ya isa sashen Lubnah.
Bai sameta a falo ba,dan haka ya nufi ɗakinta,a tsaye take tana kallon window da Ƙaramin wando a jikinta,rigar ma iyah rabin cikinta,indai ba sannan tasaka kayan ba yasan dasu tayi yawon a falo babu abinda ya dameta.
Sallama yayi a bakin ƙofar,duk da a hankali yayi yasan tajishi sarai,shurun datayi kaman gunki bata amsa ba ya tabbatar masa da labari ya isa ga kunnenta kenan na auren.
Ajiyar zuciya yasake,zuciyarsa tana tsalle a cikin ƙirjinsa,shikansa yasan tsoron ta dayake bana lafiya bane,saidai babu yanda zayyi da hakan.
“Luban!!!”
Ya ƙira sunanta cikin sanyayyiyar muryah.
Bata amsa ba sannan bata juyo ta kalleshi,shikansa yasan bai isa misalta abinda yake cikin zuciyarta ba a yanzu.
Takawa ya farayi a hankali zuwa inda take tsaye a jikin windown,duk da shareshin datayi baiji daÉ—iba,amma yasan rabin abinda ya faru larfinsa ne dana mahaifiyar sa,ko mace mai sanyin rai ba kowace zata yarda da irin auren da akayi masa ba,miji bai sanar dakai zayyi aure ba,saidai kawai kaji a bakin masu aiki. Mai yafi haka ciwo,musamman idan aka danganta da zafin kishi irinnata?.
Hannunsa ya saƙala ta ƙasan tumbinta,duk da bawani mai yawa bane amma zaka jishi,saboda ƴar ƙibar datake da itah.
Kansa ya kwantar a kafaÉ—arta,sunkai kusan minti biyar amma har sannnan yagagara cewa komai .
“Dagaskene kayi aure yau”
“Kinga ba…….”
“Kawai tambaya nayi,shin dagaskene yau an daura maka aure ko ahah?”
“Eh da gaskene,amma ba yanda kike tu…….”
Buge hannun Jabeer tayi daga jikinta tareda fuskantarsa cikin bacin rai.
“Bana son jin komai bayan gaskiyar danaji,duk Æ™oÆ™arina a koyaushe baka gani sai kayi ta kawomin mata cikin gidana koh,bayan kasan babu abinda na tsana kaman na buÉ—i ido naga wata halitta wai ita mace a gefen mijina”
“Oh gosh wai lubna yaushe zaki daina irin wannan abinne,eh aure da gaskene an É—auramin aure yau,amma ki tsaya kiji ni nawa bayanin mana,Nifah banine naje dakaina nayi aurennan ba,Mommah ce ta yimin aurennan ki fuskanta mana”
“Wacce fuskantar zanyi,koma wanene yayi maka auren aidai kai akayi wa,mijina akayiwa ni akayiwa kishiyah,ni wannan kawai nasani ba wai wanda yayi aurenba,akan me akayi shi nasan bazai wuce ace dan ka samu É—a ba,koba dan haka bane. Ko kace baka santa kaman yanda kayi sauran,kana ganin ta samu ciki shikenan saidai na ganka kana lailayata kaman ka samu Æ™wai,koba haka bane?”
“Kaiiii lubna bafah haka bane”
“To idan ba haka bane,yanzunnan kaje ka bata takardarta basai gobeba,shine zan yarda dakai toh nasan babu hannunka a ciki”
“Mee naje na bata takardarta,yakikeso kenan na fuskanci Mommah idan na aikata hakan”
“Ni wannan bai dameni ba,kaita shafah”
“Dan kinsamu ina lallabaki shine kika faÉ—amin abinda kika ga dama koh,ni bazan iya aikata abinda kike so a yanzu ba,idan har abinda na faÉ—amiki baki yarda ba shikenan”
“Haka ma zakace aikuwa gidanmu zan tafi bazan zauna ba,inka fitarta daga cikin gidannan saikaje kayi min bayani”
“Fine ga kofa nan,dama konayimiki shamaki da ita bakya daina tsallakata,yanzu ma kuma Æ™ofarki a buÉ—e take ki tafi,sanda kika ga dama saiki dawo,dama ba yau kika fara ba ai”
“Zan tafi amma karka damu dakanka zakaxo kana rokona kafin na dawo,itakuma matarka ka faÉ—amata tashirya dawowa ta bazai mata daÉ—i ba,saita fuskanci abinda bata taba ganiba a faÉ—in rayuwarta”
Tana gama faÉ—in hakan tafara tattara kayanta cikin zuciya,tsayawa yayi yana kallonta,dan shi yanzu ta daina bashi ma mamaki.
Jin ana shirin shiga sallah ne yasashi faÉ—awa banÉ—akin dakinnata domin yin alwala.
Lokacin daya fito bata nan itada akwatinta,jan ajiyar zuciya yayi kafin yace.
“Jeki na samu na huta naji da wani abun kafin ki dawo”
A zaune take ta dafe kai tana kallon Haidar yanata yimata kuka,tun yamma take fama dashi yaƙi shan nono kuma yaƙi yin bacci,gashi ta duba jikinsa babu zazzabi.
Sakashi tayi a gaba tana kallonsa har wuntsilawa yake yana shiÉ—ewa saboda kuka.
Ƙarar wayarta ne yasaka ta dauke kanta daga kansa ta mayar kan wayar.
Sunan Hilyaan ne ya bayyana akan screen din,hakanne yasa takai hannunta ta É—auka a kasalance.
“Hello Hilyaan yaya kun isa koh”
“Eh mun isa anty,yanzunnan ma aka kawoni dakin dazan zauna kafin ki taho”
“Toh ya gidan tsarinsa yayi yanda nakeso,kunga inda zan zauna a gidan”
“Ehh komai yayi sosai,gobe zamuje da khamis muyi order duk abinda kike so a saka…É—azu naga Mijinnaki gaskiya ya haÉ—u sosai,saidai da alama fah shima yana ji dakansa,daya shigo wajen mahaifiyar sa ko kallona bayyi ba,yayi zaton nice amaryar”
“Kinga niba damuwa ta ji da kansa ba,inyana so ma yaji da cikinsa ba kansa ba,bai dameni ba danshi zanje garinba daga shi har uwartasa,to ya matar tasa taji labarin auren ko kuwa”
“Eh kaman taji,dan muna zuwa Hajiya zeenah tasaka a shaida mata mun dawo,kaman yadda ta faÉ—a dagaske bata son ta kam”
“Wannan kuma tsakaninsu,nidai bazan yadda su yimin abinda banaso ba kaff gidan,ita kanta matar tasa ba yanzu zanyi maganinta ba sainazo tafiyah a Æ™arshe tukunna,abinda yake raina shizan fara”
“To shikenan Allah yabaki sa’a,yadai naji Haidar sai kuka yake lafiya”
“Hmmm ai Hilyaan kina Æ™oÆ™ari sosai da yaronnan,wlh iya yau duk narasa yadda zanyi dashi,ko fita zuwa training na gagara zuwa fah yau,gashi khmis ma bayanan,waÉ—ancan direbobin sai signarsu nake gani a cikin jeji”
“Hhhhhh gwanda ki saba ai,karki manta fah ke uwace, yakamata ki saba da É—awainiyar danki”
Hilyaan ta karisa maganar cikin dariya.
“Zanyi wanda nayi,in yagaji ai zayyi shuru,gobe zan shiga cikin gari wajen mutanen gidan can,ki tabbatar fah ki tafiyar da komai yanda ya kamata”
“Karki damu anty zamuyi miki yanda angonki yakeso,ni ina ganin ma kina ganinsa ki faÉ—a soyayyar sa”
Zaro ido tayi jin maganar takaicin da Hilyaan take yi mata,tun kafin tayi magana taji ta ƙatse ƙiran ƙitt,da alama dama tsokanarta tayi.
Duba wayar tayi taga ƙiran ya katse,cije baki tayi tareda cewa.
“Lallai kinga gadon baccina dayawa,na faÉ—a soyayyar sa,wannan maganar kuwa zata barni nayi bacci yau?”
Bombee tafaɗa cikin cije baki tana dunƙule hannu.
Da safe data tashi har mai aiki tayiwa haidar wanka ta dafa abinci. Wanka ta shiga,bata daÉ—eba tafito tana tsane ruwan dayake jikinta.
Riga da wando tasaka kaman na pakistan baƙaƙe,da alama irin shigar yana burgeta,kuma yana daukar jikinta dakuma dirinta ba kaɗan ba.
Zama tayi tashi abinci sosai,dan ma yanzu tarage yawan jin yunwar datake kwanaki..
ÆŠaure dogon gashinta mai walwali tayi da ribbon,kafin ta yane kanta da mayafin kayan.
Wani baƙin glass ƙato ta toshe dashi a fuskarta. Kallon madubin dake gabanta tayi na dan wasu mintuna,itada kanta tasakawa kanta dariyah ganin shigar datayi.
Belt ta ɗauka na goyon gaba ta ɗaura,kana tasaka haidar a ciki,wanda yake ta daga ƙafa akan gado,shima yasha baƙaƙen kaya masu tsada.
Baƙar motarta tashiga tayi mata key,bayan ta bata wuta yanda ya kamata ta ƙujeta sai cikin gari.
“To mutanen gida dana gari harda maÆ™wanta,ganinan zuwa muku bankwana kafin na tafi……..”
Ta faÉ—a cikin sautin dariyah mai É—auke da nishaÉ—i.
Kaman kullum inna laari ce kawai a tsakar gidan sai innayi tana tayata Gyara ganyen shayi,suna cikin taɗinsu na uwa da ƴa sai ganin Bombee sukayi a kansu carr ta saƙala hannunta na hagun a jikin igiyar belt din abin goyon,dayan hannun kuma tana kakkaɗa key din hannunta,dan jijjiga take da alama tana lallaba ɗanta wanda yake ɗaure a kan ƙirjinsa,hankalinsa kwance bamu mai iya tabashi saidai abinda ido baya iya gani.
“Sannunku iyalan Mlm Ahmadu,nagaban goshinsa abin alfaharinsa,ga baÆ™uwa tashigo gaisheku”
A tare suka sauke idonsu a kanta,tambayar su daya mai takeyi a wajennan bayan an É—aura aurenta jiyah.
“Mamakin ganina kuke koh,to ban tafiba bare kusaka ruwa a kasa kusha dan daÉ—i,uwata nazo gani shin zan samu ganin ta ko ahah banida ikon hakan”
Cikin izzah ta alamar babu wasa take maganar.
Innayi ce ta tashi tareda kallon Bombee tana murmushi.
“Ahh Addah Bombee kawoshi”
Yar dariya Bombee tayi tareda cewa.
“Haka aka koyamiki ki faÉ—a kuma yanzu,kiyin sakin fuska nabaki É—ana shima ku kasheshi a tsaye koh?”
“Kee wai menene Burinki ne haka,kishigo gida babu sallama babu komai ki hau yiwa mutane tujara,bada sa’nninki ba komai ba,na miki shamaki da cikin gidannan amma kin Æ™iji,ki faÉ—amana mai kikeso ne wai a wajenmu,duk abinda kikayi ta jawo mana a gari na tsawon shekaru bai isheki ba ne”
“Bai isheni ba laari,sai ranar danaci ribar abinda nake,sannan kuma kowa ya tone abinda ya shuka kafin zai saurara,banyi komai bama tukunna,ina jiran lokacin dayafi daidai ne,yanzu gargaÉ—i kawai nake aikawa kafin sakamakon ya iso.
Bombee zata bar garin gembu amma ba wai ta tafi bane shikenan,kai tsaye zata dawo tasake bayyana,domin akwai aikin data bari bata ida kammalashi,aikin dazanyi a can shine akan layi hakan shikaÉ—aine sa’arki,kafin sannan ki gama shiri iyah shirin dakike bukata”
Duk wannan maganganun a daidai fuskar laari take faÉ—ansu tana kallonta ido cikin ido.
Wani kallon inna laari tayi mata mai cikeda yarinya baki san komai ba,yayinda itama tayi mata kallon kin sake wuyana yayi kauri yafi ƙarfin yanka.
Muryar mlm Ahmadu sukaji yana cewa.
“Mai kuma wannan halittar takeyimin a gida,duk yanda na kai da Æ™in korarki saida kika tilastani na aikata hakan,yanxu kuma mai kike min a gida”
Maimakon Bombee taji haushin abinda ya faÉ—a,saima murmushi da ta zabga mai armashi da nishaÉ—i.
Toh mu hadu a page na gaba……
_*SADI-SAKHNA CEH*_
____****🖤🖤****_____
🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤
🖤 _BOOK 2_ 🖤
Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]
Anshiga Sashen na KuÉ—i,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka É—au hakkina bisa kanka tamm!!!
Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin
https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31
Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.
3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150
Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU
Mutanen niger kuma zaku biyah kuÉ—inku tanan
300f
Shaida tanan
+227 97 21 16 15
______________****_______________