Bakar Ayah Book 2 Page 19-20
Page 🖤19••20🖤
“KindaÉ—e kina min magana akan auren Æ´arki to ranar tazo,inaso ki shiryata tsaff ranar gobe da daddare zan turo a dauketa.”
“Ammma shin shugaba zilliyah ina Zaki kaita kenan,dan Allah ki barmin Æ´ata a gabana,ita kaÉ—ai taragemin wacce nake da”
“Yimin shuru laari,har yanzu baki san dalilin dayasa bata samu miji ba ,saboda na hana kowa ya kalleta da fuskar so,ita É—in matar É—anace,tunda aka haifeta ya nuna yana sonta daya ga hotonta,itace tayi daidai da wacce zata haifamin jikan dazai gajeni,dan haka zaman ta cikin mutane da kuma a gari ya Æ™are,saina daji tareda aljanu,wanda nan gaba zasu kasance sune ahalinta”
Hawayene yake zubuwo a fuskar laari,lokacin dataji zilliyah tana zayyanomata Kaddarar data zabawa yar tata,wanda batada ikon magana akai ballantana kuma hanawa.
“Shikenan shugaba zanyi yanda kikace,indai ina tareda ke nasan bazan tagayyaraba,babban abin alfaharina ne na haÉ—a zuri’ah dake Shugaba,amma zan iya ganin surukinnawa ko a hoto,kwanaki naji kince bashida rabin fuska,sakamakon yanda wani aljani yakai masa farmaki”
“Eh bashida rabin fuska,shiyasa ma baya fitowa ga halittu suna kallonsa,ko kema bazaki ganshi ba,iyah matarsa ce zata ganshi idan an kaita gareshi,karki ji wai dan ya nakasa kiyi zagon bashida amfani,kasancewar bazai iya gadona ba yasan na yanke hukuncin samun jika wanda zai gajeni,dan haka ki yi gaggawar cika umarnin dana baki.
Ganan magani a cikin kasko,kiyi mata turare dashi,ta hakane idan na turo aljanun zasu samu damar ganinta a duniyar mutane su É—akkomin itah”
Tana gama fadin hakan ta bace batt a jikin madubin kaman bata wanzu ba a jiki.
A bangaren Innayi kuwa tana gama jin abinda Aljanar tace taja ƙafafunta batareda sun ji ta ba tabar wajen.
ÆŠakin Danejo ta nufah,tana zaune kamar kullum akan kujera ta saka gabanta gabas.
Tsugunnawa tayi a gabanta tareda kama hannayenta dukka biyun ta riƙe.
“Kiyi hakuri Inna Danejo,ki yafemin abinda nayi miki tsawon rayuwata,wlh dukka inna ce take sakani nayiwa Addah Bombee,nasan cewar itace tayimiki haka,kuma tayi sanadiyyar zaman Addah Bombee haka,amma banyi zaton abinnata har yakai haka ba.
Duk da cewar na kasance mai son kai,duk abinda take ban taba fitowa na sanarwa da kowa ba,saida a yau danaji tana da niyyar hallakani tukunna,amma duk da haka ki amincemin dama taƙarahe wajen gyara kuskurena,kodah kuwa zan mutu a hanyar hakan.
“Inna Danejo inason zan gudu daga gidan ubana,saboda abinda innata zata min,saidai bazan zama mai son zuciya ba a karo na biyu,inason na tafi tareda ke cikin duniyah na nemo Addah Bombee na kaiki gareta,daga nan saina nufi wani wajen daban.
Ta hakanne kawai zan iya gyara kaÉ—an daga abinda na aikata,Ki amincemin hakan kibini mutafi inna Danejo”
Innayi taƙarisa maganar tana sakin kuka tareda matse hannun Danejo a nata hannun.
Jijjiga mata kai tafarayi tareda ƙoƙarin zare hannunta daga nata,alamar bazata bita ba kenan.
“Shikenan tunda bazaki amince ki bini ba,tunda har bazaki tsallake taki wahalar ba meyasa zan tsallake tawa wanda bata ma zo ba,nayi alÆ™awarin bazan tafi batareda ke ba,dan haka zan zauna inna ta auramin É—an matsafiyarta,idan na mutu ta sanadiyyar hakan kiyafemin abinda nayimiki a baya”
Tashi tayi zata bar ɗakin Danejo ta riƙo hannun ta.
Tsayawa tayi tareda juyowa ta kalleta.
Hannunta ta miƙa a gefen Kujerar ta,tafito da wata farar takarda daga ciki. Hannun Innayin ta kama ta saka mata ita a ciki.
Mamaki ne ya cikata amma dai sai ta buÉ—e takardar.
“Addaress inda nake aure inna ,14 way JAAN ESTATE Abuja”
“Inna Danejo wannan address É—in na inda Bombee takene?”
Saurin jijjiga mata kai tayi alamar eh shine,dunÆ™uke takardar tayi tareda cewa,shikenan na fahimta inna,duk da cewar a bansan yanda zan kaiki ga garin abuja ba a yanzu,amma zanyi iyah Æ™oÆ™arina wajen kwatantawa. Barina ce wajen Alhaji labaran na aro kuÉ—i da sunan Inna,idan muka tafi nasan dole zata biya kuÉ—in.”
Jijjiga kai nan ma Danejo tayi tareda zaro wata jaka ta miƙawa Innayin.
KuÉ—ine a cikin sabbi masu dumbin yawa,wanda tana tabbacin Bombee ce ta bata su ba kowa ba.
“Da ban so karbar kuÉ—inki ba,amma tunda na kula bakyaso na ranto kuÉ—in wani to zamuyi amfani da wannan kuÉ—in na kaiki wajen ta Da yardar Allah,abin ya isa haka.
Yanzu bari naje na nemo motar daxata fita da sassafe,saimu buyah a daji, su samemu a wajen su É—aukemu”
Tana gama faÉ—in hakan tafita daga É—akin Inna Danejo zuwa waje.
A Lokacin ana ta kiran sallahr magariba.
Sai bayan isha tukunna ta dawo gidan,kicibis sukayi da Mlm Ahmadu ya dawo daga masallaci.
FaÉ—a yafarayi mata a kan ina taje bata dawo gida ba har dare yayi.
Inna laari tana tsaye da buta zatayi alwala suka shigo mlm Ahmadu yanata faÉ—a.
“Baba kayi haÆ™uri,dama na dawo daga islamiyya ne shine na tsayah gidan Addah Ramma yin hadda,to da tsayi sosai shiyasa bamu gama da wuri ba”
“To naji,koma dai menene ki daina kawai dare a wajen irin haka kinji?”
“Eh baba zan kiyaye”
Hakan da tayi shiya hana inna laari zarginta dajin abinda suke,wanda hakan yabata damar yin shirin ta a cikin dare batareda kowa yasani ba.
Bata É—ebi kayan su dayawa ba,kaya kala bibbiyu ta saka musu a jaka,sai kuma wanda yake jikinsu.
Wajen takai kayan wajen drivenr dayake shiga cikin Jalingo,su kuma zasu fita da daddare sai ya samesu a can gaba.
Can cikin dare da misalin ƙarfe 1:00am Innayi ta buɗe ɗakinta siƙaf ta shiga ɗakin inna Danejo.
Bubbuga kafaÉ—ar ta tayi ta tashi,dan har ta fara bacci ma.
Riketa tayi suka fito daga É—akin,suna tafiyah a hankali har suka samu damar fita daga cikin gidan.
Duk da Inna Danejo bata gani,amma a tare suka juya suka kalli gidan,ita gidan ubanta da aka haifeta a ciki,yayinda ita kuma yake gidan mijinta,wanda aka kawota tun batasan mai yake mata ciwo ba,gashi yau zata barshi bada an saketa ba,saidan neman mafita,dan tasan idan har tabi zabin zuciyarta taƙi fita kaman yanda tayi alƙawari,toh rayuwar innayi kuma zata shiga cikin hadari wannan dalilinne yasa ta amince zata bita.
Juyawa suka yi tareda barin gidan,dukkansu badan zuciyoyinsu na so ba,saidan fitinar da take gidan wato inna laari.
Tafiya suke Innayi tana haska musu hanya har saida suka fita daga cikin garin.
Kafin asuba tayi sunyi tafiya mai nisa har zuwa inda Sukayi da drivern zai samesu.
Ruwa suka É—iba a wani rafi dake wajen sukayi sallah,kafin gari yayi haske ma har drivern ya iso wajen,kasancewar dama fitar wuri yakeyi.
Fitowa yayi ya taimakawa inna Danejo ta shiga motar,saida ya tabbatar sun zauna kafin ya ja suka bar cikin garin tareda saita hanyar Jalingo,inda zasu samu motar Abujan su shiga.
A bangaren Mlm Ahmadu kuwa asuba tanayi ya nufi ɗakin Innayi domin ya kwanƙwasa mata tafito tayi sallah,jin yayi bugu har uku bata motsaba yasa yayi zaton ko tana Hutun wata ne,dan haka yayi tafiyarsa masallaci.
Har 10 tayi shuru innayi bata fito ba,inna laari harta haɗa abin karyawa,ga wanke wanke ƙudaje nata bi,kuma so take dama tayi mata turaren yanzu,kafin zuwa dare ya bi jikinta.
Hanyar É—akinnata ta nufa tana magana.
“Wai nikam innayi wanne irin bacci kikene haka,ai kamata zuwa yanzu kam kin tashi kin fito koh kuma ga………”
Maganar tace ta katse lokacin datayi arba da É—akin innayi tace É—aukeni a hankali,dan babu ita babu alamunta a É—akin,sai wata fara takarda a kan gadon.
Fitt ta fito daga É—akin tana salallami kaman an jeho ta,turakar mlm Ahmadu ta nufah tana ihu .
“Mlm maza fito innayi ta bata banganta ba,da alama bata kwana a gida ba,babu ita babu alamunta sai wannan takardar,yau ni laari naga takaina”
Duk ihun da inna laari take bayyi magana ba,saima takardar hannunta daya karba ya buÉ—e.
“Aslm baba kayi haÆ™uri ka bawa inna ma haÆ™uri.
Amma bazan iya zama ba saboda wani dalili wanda bazan faÉ—eshi a yanzu ba sai nan gaba idan har na rayu.
Na tafi nida inna Danejo zan kaita wajen Yar ta addah Bombee,ta hakanne kaÉ—ai zan rage laifin dana aikata”
Ninke takardar yayi tareda nufar É—akin danejon,wanda itama inna laari tabishi kaman jela.
Kaman yanda ta faÉ—a a takardar kam Danejo ma bata nan,ya tabbata sun tafi tare kenan.
Sauƙe ajiyar zuciya mlm Ahmadu yayi,yarasa ma mai zaice,banda Inna laari wanda tasaka hannu a ka tana ihu,yagagara cemata komai.
Fita waje yayi ko za’a samu mafita,domin zaman sa cikin gidan babu abinda zai haifar,tunani ne fall a ransa,musamman daya tuna shekaru dasuka wuce a baya,Lokacin da Æ´aÆ´an sa suke Æ™anana,yayi rayuwar farincikin da bai taba zaton zayyi ta ba,a yau kuma sai gashi ya rasa komai na farincikinsa. Tabbas yasan hakan jarrabawa ce daga Allah,shiyasa ma yake fatan Allah ya bashi ikon cin ta.
A wajen inna laari kuwa ba kukan Batan Æ´ata bane yafi damunta,kukan wanne irin tashin hankali zata fuskanta ne a wajen ZILIYYAH,sannan kuma ga Danejo ma ta tafi,idan Bombee tayi nasarar samunsu,tasan idan suka sake gamuwa saita Allah,wai Jaka a É—aki.
Saboda gudun da Drivern yake kuma ya kware sosai,da rana tsaka suka isa Tasha a cikin jalingo ina zasu hau motar taraba.
Masa innayi a siya musu a wajen da ruwa a cikin kuÉ—in suka ci.
Kana suka yi sallah tareda samun dan hutu,kafin a gama yin lodi a motar dazasu shigan.
“Inna Danejo kin gaji koh,kiyi hakuri yanzu zamu shiga mota,inshaaallah muna isa abuja sai mu bawa masu mota address É—in su kaimu,da sannu nasan zata nema miki magani ki warke inna”
Tana jin abinda innayi takecewa,amma batace komai ba,dan itama har ga allah tayi kewar Æ´ar tata sosai,abin tsorom shine bata san a wanne yanayi zata sameta ba ne.
Suna nan zaune sukaji ana ƙiran sunansu,innayi ce ta taimaka mata ta tashi suka nufo motar,dan tun ɗazu suka biya kuɗin motarsu dama.
Ƙara nausawa sukayi kan hanya,tareda kama niyyar barin nahiyar su ta taraba.
Tafiya ce aka farata kaman ta yada dan shege,sannan abinka da basabunba tuni bacci mai nauyi ya É—ebesu a motar.
Basu suka buÉ—e idanuwansu ba saida muryar yaron motar ta jiyarci kunnensu.
“Ke Æ´an mata,iya maza tashi zamu kai mota wajen ajiya mu kulleta”
Firgit innayi tayi takalli yanda gari yayi duhu,ga babban titi motoci suna ta wucewa sun haska danjar su.
“Mlm ina ne nan kuma,mun iso abujanne”
“Yo wannan kuma na nawa,har fasinja kowa yakama hanyar gabansa,bakusan inda zaku bane kome?”
Saurin tashi tayi ta duba jakar kuÉ—insu dake kunkuminta,amma babu ita babu alamarta.
Kallon yaron motar tayi ido a zare tace.
“Mlm ina jakar kuÉ—ina toh,bangata ba ina ta kayanmu ma?”
“Haba Hajiya ni da nake gaba ina zansan inda jakar kuÉ—inku take,kayanku gashinan na saka muku a gefenku,dan Allah ku tashi zamu rufe mota”
Hawayene ya jirarowa Innayi lokacin data gano cewar wani ya É—auke musu jakar kuÉ—insu,gashi suna wajen da basusan kowa ba,takardar da inna Danejo ta bata tafara lalumawa domin ta nunawa yaron drivern,ita taji wayam babu ta fadi.
Innalillahi wa inna ilaihi raji’un.
Shine abinda bakinta kaÉ—ai yasamu damar furtawa,dan tasan sun shiga tsaka mai wuyah.
“Shugaba Zilliyah ki taimakeni kiyimin rai n roÆ™eÆ™i,wlh bansan cewar zata tafiba kinsanni kinfi kowa sanin halina,bazan barta ta tafi ba inda na sani”
“Kiyimin shuru,banza marar amfani,taya kika bari har tasan dashirin mu ta gudu,lokacin da burina yake dabba da cika komai ya watse,idan har itama waccar yarinyar tasan cewar Uwarta bata hannunmu,kina ganin zata zuba ido tayi shuru ne iyeee.
Dolene kisan abunyi,na baki nan da sati guda ki nemo,idan kuma ba haka ba……sainayi miki abinda bantaba yiwa wani yashi muniba.
Koda yake bata lokacina kawai zanyi,idan na barki babu abinda zaki iya akai,dan inaji a jikina sunyi nisa,gashi bakiyi mata turaren ba tun dare dana baki,saboda kinaso Æ´ar ki ta gudu koh.
Naaa tsinemiki laaarrii bazaki tana ganin daidai ba daga yau.
Nida kaina zanje na nemo su,dakaina zan je inda suke na É—auko suruka ta,ita din mallakina ce,dukka su ukun nawa ne,nafara aiki akan su to kuwa bazan taba ja da baya ba.”
Tana gama ƙarajin da ihun ta bace bata daga jikin madubin,bayan ta fesawa inna laari wani abu a jikinta.
Ihu inna laari tafara tana roƙon Zilliyah agazi,amma maimakon tajita,saima madubin dayayi fass ya fashe gida dayawa ya tarwatse.
Yana tarwatsewa kuwa inna laari tasaka ƙara tareda bingirewa tafara burburwa a wajen.
Zaune yake a personal gidansa ya rike kofin ruwa a hannunsa,da kuma magani,shibai sha ba shikuma bai ajiye ba.
Tunani biyu ne a cikin ransa,na farko shine na amaryartasa da Hajiya zeenah ta auramasa,duk yadda yaso ya fahimci ita wacece abin ya ci tura.
A yanda yaganta rannan zai ya rantsewa cewar bata haɗa hanya da hausawa ba inba dayaji tayi hausarba,sannnan a yanda ya karanci jikinta macece mai ƙarfi kuma jaruma.
Shikansa bazai yiwa kansa ƙarya ba yasan kyakykyawa ce fiyeda sauran mata daya taba haɗuwa dasu,a duk lokacin da idonsu ya haɗu dana juna sai yaji wani abu ya tsirga masa,ko dan saboda idanuwanta wasu iri ne shiyasa yakejin wani yarr idan ya kallesu.
“Hmmm kuma ma wai hadda yarone da itah,haba mommah meyasa kike min haka,taya zaki auramin matar da take É—a hakan ma É—an karami,bazawara ce ko kuma shegene É—an bansani ba. Shin haka na koma kowa ma sai a auramin ita,”
Cikeda takaici yake maganar shikaÉ—ai batareda mai sauraro ba.
Tunani na biyu kuma Jaleelah,iyah haÉ—uwa dakuma hada abinda ake so a wajen mace tagari dukka tana dashi,tunanin sa É—aya shine auren,mata uku taya zai iya fuskantarsu ma tukunna.
Wata zuciyarce tace masa,kawai ka aureta,ai an auramaka mai É—an ma a wani wajen dabaka san wacece ba ka rayu,sai wannan ne zai gagareka.
Ajiye maganin yayi da ruwan ya tashi ya saka kayansa,baiso komawa gidan yau ba,dan yau É—inne Lubnah takoma sashenta sabo,wanda yasan shima an kaimasa kayansa can É—in,ko sha’awar wajen bayason kalla bare kuma zama a cikinsa,idan yaki komawa kuma yasan bai dace ba ace matansa na wani waje daban shima yana wani waje daban.
Lallai Hajiya zeenah tagama tsara taswirar rayuwarsa a hannunta,wannan karon zai gwada ƙwatar ƴancinsa koda kuwa kadanne.
Tafiya kaÉ—ance takaishi gidannansu,direct sashen iyayennasa ya nufah,baisani ba shin abban nasa zai amince ko kuwa ahah,dan karyace ai bai daÉ—e dayin sabon aure ba.
Su biyune a falon,daga Hajiya zeenah sai shi,da alama zance suke akan wani abun.
Ita kuma Hajiya zeenah da saƙa ta ulu a hannunta tanayi domin samun abinyi.
Bayan ya gaishesu zama yayi yai shuru,shibai tafiba shikuma bai ce komai ba.
Dariyar dattako Alhj Aliyu yayi kafin yace.
“Babban mutum yadai naga kayi shuru,kuma alamu sun nuna akwai abinda yake cikin ranka,mai nene a haka ka faÉ—a min ko mai nene.
Kobaka so faÉ—ane a gaban mahaifiyar taka kanajin kunya”
“Ahhh nizaiji kunyah,saidai ko nauyi tayi masa kai a baki,idan kunyace kuma to barina baku waje ku tattauna,idan tayi wari ai zanji”
Hajiya zeenah tafaÉ—a tana dariyah zata bar É—akin.
Saurin dakatar da itah Jabeer yayi tareda cewa.
“Ahah mommah ki zauna kawai,dama……dama inaso na faÉ—amuku ne cewar zan Æ™ara aure,akwai yarinyar danake so to kuma mahaifinta yace na turo ayi babbar magana”
Ɗan taƙaitacce bayanin Jaleelah Jabeer yabawa su Hajiya zeenah.
Jimm sukayi dukkansu kafin Hajiya zeenah tafara magana,wanda dama tunda yafara maganar ta tsaya da abinda take.
“Aure kuma yanzu,habadai aure ina kuma Auren shi……..”
“Kinga kinga Momyn yara,kada ma ki É—akko wannan zancennaku da kuke ta maimaitawa shekara da shekaru,bazan hanaki yabi umarninki ba,saboda ke kika haifeshi,amma kuma wanann karon bazanyi shuri ki tauye masa haƙƙinsa ba.
Duk tsawon lokaci ke kike aura masa wacce kika ga dama,wannan karon yazo miki da wacce yake so,dan haka bincike yakamata a ayi,idan har gidan mutuncine nizan saka ayi bincike akan hakan.
Godiyah sosai Jabeer yayiwa abbannasu,dan bayyi tsammanin zai amince tashi É—aya ba.
Duk da cewar Abbannasa ya tari bakin Hajiya zeenah,amma yasan bazatayi shuru iyah hakanan ba.
Dole saita yi wani abun akai,shi hakan bai dameshi ba tunda mai nemo masa auren ya amince.
Bayan Jabeer ya tafi nasiha Alhj Aliyu ya zaunarta yayi mata akan lamarin da take tafiyar da rayuwar É—anna ta,amma hakan bayyi mata ba.
Tana shiga dakinta tace “chabÉ—ijan aure,yar uban wanne matsiyacin ce,daga yanda yabada labarin É—iyar talakawa ce,waton sunganshi da alrziÆ™i da matsayi zasu mallakeshi koh…..hmmm dani kuke zancen.”
Wayarta da É—auka tana neman Number Hajiya rabi,domin susan abinyi.
_*SADI-SAKHNA CEH*_
____****🖤🖤****_____
🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤
🖤 _BOOK 2_ 🖤
Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]
Anshiga Sashen na KuÉ—i,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka É—au hakkina bisa kanka tamm!!!
Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin
https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31
Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.
3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150
Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU
Mutanen niger kuma zaku biyah kuÉ—inku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150
______________****_______________