Bakar Ayah 4
Page 🖤04🖤
Ƙarar jiniyar motar asibiti ce tafara amsa kuwwa a gidan,wanda hakan ne ya shaida alamar shigowa da gawar Hafsa tareda jaririn yaronta cikin gidan.
Bayan motar asibitin ta shigo sai kuma motocin su Jabeer suma suka biyo bayanta.
Kowanne idan kaga fuskarsa kasan mutuwar ta shigeshi,yanda suke fitowa daga motar jiki a sanyaye.
Sashenta aka nufa da ita domin yi mata sallah a É—akinta,duk abinda ake Lubna bata fito ba,bare tazo wajen yin suturar.
Sai bayan an tafi da ita kafin tafito da jumbulelen hijabi a jikinta fari tana rarraba ido.
Babu abinda kakeji a wajen sai kukan Sayyada-tateen,wacce babu yanda ba’ayi da ita ba,amma taÆ™iyin shuru sam,kowa tausayinta ne ya kamashi,saboda babu wanda baisan shaÆ™uwar da sukayi ba da hafsan.
Bayan dawowa Daga binnetan aka cigaba da karbar gaisuwa,Saidai duk wanda yazo yiwa Jabeer gaisuwa sai a ce bayanan.
Abinne ya É—aurewa abokinsa kai Khaleel,wanda hakan yasashi shigowa cikin gidan nemansa.
Da madeena suka haÉ—u a hanyar shiga sashensu zata kaiwa Æ´an uwan Hajiya zeenah Abinci.
“Am Madeena ina kuwa JJ( Jabeer Jaan) banganshi ba,gashi ana ta zuwa yimasa gaisuwa a waje”
Alamar mamakine yaÉ—an hau kan fuskarta,dan itama batasan inda yake ba,sannan babu wanda yaga shigowarsa,sashensu ma mutanene a wajen sosai.
“Ahah Banganshi ba,bansan inda yayi ba,kuma ina kyautata zaton baya Sashensu ma,dan wajen akwai mutane sosai. Amma ka Æ™irashi mana kaji inda yake”
“Tun É—azu nake Æ™iran wayarsa switch off,tabbas mutuwar Hafsa ta girgizashi,amma bai taba yin haka ba ya kashe waya dukka,kuma a irin wannan yanayin da mutane zasu nemeshi sosai”
Dukkan shuru sukayi kowa yana tunanin shin a ina zasu ganshi,can bayan shurun nasu madeena tace.
“Uhm barina tambayi ummah kota san inda yake ”
Daga haka ta wuce tabar Khaleel a tsaye,yana jiran fitowarta.
Wasa wasa anyi sadakar uku amma babu Jabeer babu Alamarsa,kowa yayi ta mamakin ina yashiga,anyi zaton ma ko ya bar garin.
Sai washagarin kwana uku mutane sun fara raguwa sannan yashigo gidan da motarsa.
A hankali yafito daga motar yana jefa ƙafa kaman mai koyon tafiyah,idanuwansa sunyi luhu luhu sai lumshesu yake kaman wanda yayi maye,kallon mutanen da suka kewayeshi yayi,amma babu wanda yayi wa magana,har hajiya zeenah wacce ta kafeshi da ido,da alamar tambaya a kallonnata.
Hanyar sashensa yayi kansa a sunkuye,bai juyoba har ya shige ya turo ƙofar.
Bai cire takalman ƙafarsa kana bai fasa tafiya ba har ya shiga cikin ɗaki.
Kan luntsumammen gadonsa ya faÉ—a a haka yana jan gwauron numfashi,tareda fesar da iska mai zafi.
Runtse idanuwansa yayi na tsawon sakanni kafin yafara buɗesu yana sauƙesu akan farin POP ɗin ɗakin.
Hawayene sirara suke bin gefen idanuwansa suna zuba akan zanin gadon,bai damu daya share su ba,haka yabar su suka cigaba da zuba har na tsawon wani lokaci.
Wayarsa ya fitar daga cikin Aljihun wandonsa ya kunnata.
Kaman jira kuwa takeyi,tafara amayar da saƙon da aka zubo mata lokacin da take kashe.
Ƙuramusu ido yayi suna ta shigowa,saidai ko kaɗan bai nuna alamar ma zai buɗe ko ɗaya daga cikiba,shidai yana kallonsu kawai.
A jiyeta yayi a kan drawer gadon ya shiga banɗaki,har sannan wayar bata daina ƙarar shigar massage ba.
Ya daɗe a wankan kafin ya fito sanye da towel a ƙugunsa,ɗaya kuma akan sa yana tsane ruwan jikinsa.
Farine ba sosai ba,sannan yana ƙirar jiki,da alama ba haka aka bar jikin ba ana motsashi.
Yanada baƙin gashi sosai,amma daga ganin yanayinsa kasan bashida laushi a nature sa,ana amfani da manyan mayuka ne wajen bashi gyara na musamman.
Kallo É—aya yayi kansa a madubin dage gabansa yayi saurin É—auke kai.
Da alama bayason kallon ramar da take kwancene a kan fuskarsa,kana da kuma launin idanwansa wanda har yanzu basu dawo da haskensu ba.
Riga da wando yasaka marasa nauyi yafita daga ɗakin da sauri,jin alamun ana buga ƙofar falon da ya sakawa key shigowarsa.
Da Madeenah suka haɗa ido lokacin daya buɗe ƙofar itada Maleekah,ɗauke da kulolin abinci a hannunsu.
Ganin kallon tuhumar da sukewa idanuwansa ne yasashi saurin É—auke ido tareda komawa cikin falon ya barsu a tsaye.
Suma basu damu daya ce musu su shigoba suka biyo bayansa,dan sunsan ko za’ayi shekara bazai faÉ—a ba É—in ba.
A jiye kayan abincin sukayi a kan center table ɗin dake gabansu, Madeenah ce tayi ƙarfin halin faɗamasa saƙon da aka aikota dashi.
“Uhm ummah tace idan ka gama tana nemanka a sashen Abbah”
Bayyi magana ba duk da tasan yaji abinda tace,dan haka kowa ke fama da halinsa na rashin magana shida Maleekah.
Har takama handle ɗin ƙofar zata fita taji muryarsa ƙasa ƙasa,inda akwai surutu a wajen ba lallai taji mai yake faɗa ba.
“Lubna tana nan?”
Haushine ya turnuƙeta sosai,bayan kwana uku daya ɗauka bayanan,ana nemansa an damu dashi,amma yana dawowa bai tambayi kowa ba sai wata Lubna.
“Bansani ba”
Shine amsar da Madeenah ta bashi a daƙile,kafin tayi wuff tabar sashennasa,kar ya huce akanta.
Fitowa yayi daga sashen ya nufi hanyar na Lubna.
Ga hasashensa kuwa bata nan kaman yanda yayi zato,ina taje oho.
Tun halinta yana bashi mamaki yanzu abun har ya zame masa jiki,lokacin da ake wani abin daya girgiza kowa a gidan,ita sannan zata shirya tabar gidan,ko kunya ma da kuma bakin mutane bata ji.
Jawo ƙofar yayi ya nufi Apartment ɗin iyayennasa.
A zaune yake mahaifinnasa kaman kullum akan Wheelchair,shekararsa uku kenan akai tunda ya samu paralyse na Accident,a lokacinne Jabeer ya karbi kujerar CEO na Companyn.
Maganinsa Hajiya Zeenah ta balla ta miƙa masa,tareda kofin ruwa.
Sallama Jabeer yayi a hankali can Æ™asa Æ™asa yanda za’a jishi amma kuma bada sauti sosai ba.
Hajiya zeenah ce ta waigo ta kalleshi daga haka da maida kanta wajen mijinnata.
Gaisawa sukayi da mahaifinnasa kafin daga bisani ya tambayeshi jikinsa.
“Jiki Alhamdulillah Jabiru,Naji ummanka tace kwana uku baka gida sai yau ka dawo?”
“Eh Abba dama……dama….”
“Bakomai nasan yanda kakeji a ranka,rashin mata da kuma É—a,musamman a yanayinka abune da yakamata ayi maka uzuri,sannan kuma a jajanta maka.
Allah yabaka ikon yin haÆ™uri da kuma tawakkali,sannan kuma ka dage da addu’a da miÆ™a lamarinka ga Allah,watarana zai wuce sai labari”
“Inshaaallah,nagode Abba”
“Tabbas ansan anyi maka mutuwa,amma bai kamata ka kashe wayarka sannan kuma tafi batareda ka sanar da inda kake ba,Abokan kasuwancinka jiya suka zo daga india yimaka gaisuwa,sai tafiya sukayi basu sameka ba……..”
Shuru Jabeer yayi yana jinta,yanda take faÉ—an baya nan,badan ta damu dashi ba sai dan ta damu da yanda aka zo ba’a sameshi ba,shikansa wani lokacin yana zama yayi ta tunanin shin Hajiya zeenah ce ta haifeshi,saidai ga sauran Æ´aÆ´an ma haka takeyi,wanda yake nuna zai fiddata kunyah yayi kuÉ—i shine a gaban goshinta,gaba É—aya batasan nuna soyayya ga É—anta tsakani da Allah ba,saidan wani abun duniyar.
Haka ta horar dasu tun suna yara,burinta su zamo sunfi kowa,indai har wani ya fisu to anan zasuga bacin ranta a fili.
Shiyasa takeji da Jabeer saboda yana matakin farko a compayn nasu,abu ɗaya ne yake cimata tuwo a ƙwaryah,shine mata marar arziƙi da Allah ya haɗashi da ita,saikuma rashin haihuwa da bai samuba.
Lokacin daya auri hafsa ta samu ciki,tafi kowa farinciki,itama zata samu jika a daina yimata habaici,saidai kash Yanda taso bai yiyuba. Wannan dalilinne yasa ta ƙunshe vaƙin cikin Lubna a cikin zuciyarta.
“Haba Zeenatu wai meyasa kike hakane,yaronnan fah Matarsa ce ta rasu da kuma É—ansa,kuma kinfi kowa sanin yanda waÆ´annan mutane suke a wajensa,dan yatafi yabar gida,daga dawowarsa ki fara wai abokan kasuwancinsa sunzo bayanan basuji daÉ—i ba?”
Jumburo baki tayi tareda hararar Jabeer ɗin ta ƙasa ƙasa,
“Haba Alhj yanzu kai baka ga maganata akan gaskiya,yanzu daya tafi da wani muhimmin aiki ya taso fah,yakake ganin za’ayi,kuma dazakace haka duk waye ya jawo komai idan bashi ba,da bai auro waccar masifarba aida komai bai faruba. Hmmm ai bari ayi sadakar Arba’in,takardarta zai bata ya auri Æ´ar mutunci wacce zata haihu,ba ita ba juya”
“In kina so ma kice yasaketa yanzu,ai duk É—aya ne tunda kin faÉ—i Abinda ke bakinki,ki dunga sararawa zuciyarki dai,kina yayyafa mata ruwan sanyi,dan yanzu girma yafara kamaki,inba so kike ciwon zamani ya kama ki ba”
Shuru sukayi dukkan su babu wanda yasake cewa komai,kana ganin Hajiya zeenah kasan da maganganu a ranta fal,ganin idon mijinnata ne yasata yin shuru badan ta haƙura ba.
Shikuwa dama Jabeer duk maganar da suke a iya zuciyarsa yake saƙasu,ko ɗago da kansa bayyi ba.
Alhj Aliyu ne yakalleshi cikin tausayawa tareda cewa.
“Tashi ka tafi Jabeer Allah yayi maka albarka,sannan yakamata ka É—au hutun Aikin kaje wani waje nesa da gidan kaÉ—an huta na wani lokaci”
“Toh Abbah”
Alhaj Abdullahi ne ya fito daga mota ransa a bace ya nufi bangarensu.
Sauri yake zubawa kaman zai tashi sama,dan dama irin mutanennnan ne masu firitt jiki da kuma sauri.
Bai samu kowa a falon ba, dan haka ÆŠakin lylah ya nufah.
A zaune take tana bawa Haneef Abinci a baki,wuyansa sai gilu gilu yake da ƙyar yake karban abincin.
Tsayawa yayi bakin ƙofa batareda yayi ƙyakykyawan motsi ba yana kallonsu.
Tunani yatafi yanda rayuwar su take kasancewa shida matar tasa,shekararsu sha shida kenan da aure,babban É—ansu haneef mai shekara Sha biyar,Allah ya jarabceshi a Lalura,ko kansa baya iya tsayarwa bare yayi wa kansa wani abun.
Saurna yaransu kuma huÉ—u dukka matane,shikaÉ—aine dansu namiji saidai dashi gwara babu a wajensu.
Yanada shekara É—aya a duniyah yakoma haka,har yau babu wanda yasan meyasa ya koma haka,anyi na gargajiya anyi na asibiti amma abu yaci tura.
Haneef É—inne ya juyo yakalli mahaifinnasa dake bayansu,aikuwa ya wangale bakinsa yawu yana zuba,alamar yana masa dariya.
Itama lylah juyowa tayi ta kalleshi tareda cewa.
“Ahh yaushe ka shigo,amma lafiya na ganka da wuri haka ka dawo,É—azu fah kake cemin yau sai dare ka dawo”
“Hmmm kedai bari laylah,ni narasa yanda zanyi da wannan yaron,nine nafara sanin companynnan kafin yasani,amma dan tsabar babu wanda yake ganina da daraja a gidannan,wai aka É—au kujera mafi matsayi aka damÆ™a masa.
Project É—in danacemiki zan jagoranci aikinsa,saida suka zo yau da suka ga Jabeer baya nan wai bazasu yadda na jagoranci aikin ba,tunda hutu yatafi kuma ya kusa dawowa to zasu jirashi ya dawo”
“Kutt to miye dalilin daya saka bazasu baka ba,ba kaine Defuty CEO ba,duk wani aiki dayake ai kai yakamata kayi in bayanan.
Hmmm dama na daÉ—e da faÉ—amaka ai cewar duk gidannan Æ´an baÆ™incikine,babu wanda yadamu da rayuwarmu a cikinsu,in ina faÉ—amaka kana ganin banason yan uwanka,yanzu ai gashi ka gani da idonka”
“Nagani kam,duk wani aiki danayi a companynnan banida daraja a cikinsa,yau inna faÉ—i na mutu babu abinda iyalina zasu tsira dashi,dolene na É—au mataki akai”
“Hmm hakane kam,yanzu inka yarda a É—au mataki to kabar komai a hannuna,nikuma zan saita komai yanda ya kamata,buÉ—ar idonka kawai zakayi ka tsinci kanka a matakin CEO na JAAN company”
“Na baki dama kiyi komai ma yanzu,nima yanzu bazan saurara ba,dole na Æ™waci haƙƙina a ciki”
Wata dariyah gefen baki laylah tayi tareda kanne ido guda É—aya.
“Ka zuba ido kaga aikin laylah masoyina,bazan baka kunya ba”
🖤 Sadi-Sakhna ce🖤
Æ´ar mutan jama’are
____****🖤🖤****_____
🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤
🖤 _BOOK1_ 🖤
Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]
*WATTPAD*
Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03
*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna
______________****_______________