Arubuce Ta Ke 2
waiwayowa yayi yana dubanta bayan ficewarsu gaba daya,maficin da ummu ta tashi ta bari ne riqe a hannunta tana tsige adon jiki,fuskarta a dinke tsaf,yakanyi.mamakin yadda take masa,kamar wata qatuwar budurwa,ya rasa dalilin da sam bata son su zauna waje guda ko su hadu,saidai har yanzu zuciyarsa na bashi nutsuwar cewa quruciya ce kawai da rashin sanin ciwon kanta,da zarar ta sake hada hankalinta zata fuskanceshi?
“Amma sai yaushe?,lokaci qara quracewa fa yake” zuciyarsa ta gaya masa,sai ya dan gyada kai
“Soon in sha Allah” ya fada yana bawa kansa qwarin gwiwa,qwarin gwiwar da kusan kullum itace madogararsa
“Widad” ya kira sunanta
“Na’am” ta amsa a cunkushe ba tare data kalleshi ba,murmushi yayi
“To kidan kalleni mana?,ummm,ke da zaki zama matata?,so nake ki saki jiki da yayan naki” manyan fararen idanuwanta ta daga tana kallonsa,wani haushi da kuma tsanarsa suka saukar mata,lallai yaaya mahfood ta tabbata dan iska ne,ita yakewa zancen ta zama matarsa?.
Yadda ta zuba masa fararen idanuwan nata sai yaji dadi cikin ransa,don takan jima bata tsaya ta kalleshi ba,wannan ya bashi qwarin gwiwar janyo ledar daya shigo da ita wadda ke shaqe da kayan kwalliya,kasancewar ya santa da son kayan ado da gayu ya tura gabanta
“Ga kayan kwalliya nan ‘yammatan ummu,sai ayita shafawa ko?” Dauke idanunta tayi daga kansa ta mayar kan kayan,saita dalla wa kayan harara,ita zaiwa wayo?,ya dauka bata da hankali kenan,haka kawai,bayan ummu tasha gaya mata ko zama tayi kusa namiji ciki zatayi,shine zai wami bata kayan kwalliya?,to bai isa ba,tana gama wannan tunanin ta miqe abinta ta nufi qofa da saurinta.
“Zo mana widad…..widad”ya fara qwala mata kira,gudun kada latifa ko ummu dake daki su jiyo shi,su kuma sanyata dawowa dole saita fella da gudu ta qarasa ficewa,don ta lura shi kadai ne zaifi mata saurin barin sassan.
Bata tsaya ko ina ba sai sassan anty madina,taja birki tana zabga haki,dai dai lokacin da dukka yara yaran gidan da suke da shekaru irin nata ke zaune a falon anty madina,kaf cikin matan gidan ta fisu qarancin shekaru,tana da faran faran da son mutane,tana yawan jansu a jiki gami da biyewa shirmensu,wannan yasa kafatanin yaran gidan kowa ke sonta,yake kuma son zama a sassanta.
Dago kai tayi tana duban widad,muhassana ce kwance a cinyarta diya ga qanwar mahaifin widad tana mata tsifa
“Lafiyarki widad?,irin wannan cin burki haka?” Guri ta samu kusa da khalisa ta zauna tana maida numfashi,sai kuma ta bata rai, idanuwanta sukayi rau rau suka ciko da qwalla
“Yaya mahfood ne”
“Mahfood kuma?,biyoki yayi?” Kai ta girgiza tana turo baki gaba,ita sam sam ma batason maganarsa,yanzu su mahassana zasu fara tsokanarta
“Wai cemin yayi matarsa” tana fadin maganar qwalla na gangaro mata,qaramin murmushi anty madina ta saki,ta rasa wanne irin rashin haduwar jini ne haka tsakaninsu,duk wanda ya kwana ya tashi yasan yadda mahfood din ke qaunar widad,hakanan kowa yasan yadda take gudunsa,bata qaunar hada inuwa dashi
“To banda abinki mene ne don yace miki matarsa iyi widad?,bakiga su zahira ba aure za’ayi musu?,kuma daga su sai ku?” Kafin anty madina ta kammala bayaninta widad din ta saki kuka harda turje qafafu,baki anty madina ta sake tana kallonta gami da jan salati,yayin da su muhassana suma ke kallonta suna dariya
“Tsaya,bakya sonshi ne shi yayan naku?” Kai ta gyada
“Wallahi ni bana sonsa Allah”
“To ya isa,ki share hawayenki,an gama maganar,ba wanda zai baki shi” dif kukan ya tsaya,ta tashi ta zauna dai dai tana goge qwallarta tana kuma hararar su khalisa kan dariyar da suke mata
“In sha Allahu sai su abba sun baku dauda” dariya sosai anty madina ta tuntsire da ita,duk da quruciyarta wani lokaci idan tayi wani abun kamar babba,dauda shike wankin gidan,na kowanne sashe,daga qauye yazo a gidan aka riqeshi
“Bakinki ya sari danyen kashi” khalisa ta fada tana dariya
“Saidai naki bakin” widad ta fada tana sake harararta,dole anty madina ta shiga fadan ta raba,ta kuma janye musu hankalinsu da wani abu na daban.
Qememe taqi komawa sassan ummun,duk da ummun ta aiko latifa har kusan sau uku amma taqi komawa,zatonta mahfood yana nan bai tafi ba,wayo ummun keso tayi mata don ta dawo,har abbanta yazo ya tafi bata koma din ba,son samunta ma tayi kwananta nan wajen anty madina cikinsu farisa,amma kuma tana tsoron kyankyaso,kada yayi mata irin yadda yayi mata daxun,har sai data fara barci sannan latifa tazo ta tafi da ita bayan ta tasheta ta sakata a gaba.
Tana shiga dakin ummu ta haye gadonta taja bargo ta duqunqune sosai harda cusa kanta cikin pillow,tun tana kasa kunne taji shigowar ummu har bacci yayi awon gaba da ita.
Washegari ummun bata ce komai da ita ba,saidai ta bata ledar kayan kwalliyar tace ta dauketa taje ta adanata,aifa kamar jira take,saita dire cup din da take shan tea dashi ta saki kuka
“Allah ni bana so,banaso ummu” tana turje qafarta a qasa
“Hukumullahu” ummun ta fada a ranta tana zuba mata idanu,wannan abun na widad din kuwa na qare ne?,kullum abu kamar ma sake ci gaba yakeyi?,kafin takai ga sake cewa komai akayi sallama falon,ta dauke kanta daga widad ta maida gareshi taba amsa sallamar.
Babban mutum ne ko ace magidanci,wanda kallo daya zaka masa kasan danta ne daga tsatsonta ya fito,a nutse ya qaraso falon yana kallon widad da fuskarta tayi sharkaf da hawaye
“Ke kuma da baki rabo da rigima me akayi miki?” Ya fadi yana neman wajen zama,baki ummu ta tabe tana girgiza kai
“Don anyi maganar mahfood ne” saita zarce da gaya masa abinda ya faru jiya.
Maida dubansa yayi gareta yana nazartarta na wasu daqiqu,shima kallon quruciyarta yakeyi,yasan ita ke dawainiya da ita,don idan a wani gidanne ko zancan aurar da yayunta da za’a aurar yanzu ba’a fara ba bare ita,to amma haka tsarin yake,a haka kuma dukka suke tafiya
“K’aniyarki” abba ya fada yana tsuke fuska
“Don gidanku mahfood ba babanki bane kike masa irin wannan?,maza tashi ki dauki kayan ki adana su” fuskarta jiqe da hawayen ta miqe ta dauki ledar,sai tayi hanyar fita da ita
“Ina zaki?,nan ne dakinki?” Cikin muryar kuka ta waiwayo
“Anty madina zan kaiwa….”
“Eh itace ke iya jurewa shirmensu ai” ummu ta karba zancan tana qarashewa abba bayani,sai baice komai ba,wannan ya bawa widad damar ficewa.
Tana tafe ita daya tana sharar qwalla,maimakon sassan anty madina,sai tabi siririyar hanyar da zata sadata da parking lot na gidan,tasan can ne babu kowa,don duka samarin gidan masu fita kasuwa kawo yanzu sun fita din,sai su ‘yan makarantar da suke shirin komawa ranar litinin,sune daliban da aka yaye daga primary school zasu wuce zuwa qaramar secondry jss one.
Dan bencin da ake ajewa a wajen lokaci lokaci ta haye ta zauna a kai,sai a sannan ta buda ledar tana duba abinda yake ciki,kayan makeup ne sosai irin wadanda takeso,batayi mamaki ba,don uncle mahfood din ya jima da sanin zabinta da kuma duk wani abu da takeso.
Sai data fiddosu tsaf ta qare musu kallo,sai kuma ta tabe baki,motsin da taji daga parking space din ya sanyata fara tattara kayan cikin hanzari,tana gudun ko abba ne ya fito zaya tafi,ta tabbatar idan ya ganta a wajen fada zata sha.
Wanda ta gani a wajen yana niyyar fitowa daga motar tasa ya sanyata sauke ajiyar zuciya,tasan cewa kome zatayi ba kulata zaiyi ba bare ya hanata,don kuwa tsahon tasowarta ta sanshi amma ba zata iya tuna rana daya da magana ta taba shiga tsakaninsu ba.
Kamar yadda ta zata din kuwa,ko a yanzun ma dauke kansa yayi ya soma rufe motarsa sanna ya jefa key din a aljihu ya kuma soma takawa yabar wajen.
Da kallo ta bishi tana tabe baki gami da jifansa da harara,har sai da ya bacewa ganinta sannan ta dauke dubanta daga wajen,a hankali take tattare kayan tana maidawa cikin ledar,qasa qasa take magana ita daya
“Wallahi banaso,bayarwa zanyi,ni ba wani aurensa da zanyi,dan iska kawai” dif maganar tata ta yanke,sai kuma tahau zaro idanu cikin tsoron kada wani ya jita,sai data tabbatar babu motsin kowa sannan ta qarasa kwashe kayanta ta kuma fito.
Isowarta farfajiyar gidan yayi dai dai da budewar gate din gidan,qaramar motar qirar 406 ta danno kai ciki,sai ta dakata daga yunqurin isa sassan anty madinan tabi motar da kallo,sai kuma ta saki murmushi har dimple din dake kwance saman kumatunta hagu da dama ya lotsa,saita cilla da gudu gudu sauri sauri zuw wajen motar,cike da zumudi da kuma murna.
Sanda ta isa daura da motar tuni mamallakiyar motar ta kasheta tana yunqurin fitowa
“Anty dina sannu da zuwa” waiwayawa tayi sashen da widad din take tana niyyar dauko jakarta daga back seat na motar
“Widad rigimammiyar ummu,ya na ganki a gida kuma?” Murmushi tayi tana leqen cikin motar da alama akwai abinda take nema
“Anty secondry zamu tafi fa,muma mun zama manya kin manta?”
“Au anyi haka fa,kice zamu sake samun qarin ‘yammata cikin gidan namu…..”
“Anty wai ina aysar ne?” Ta tambayeta cikin katsar numfashinta
“Gashi nan a daure” ta fada tana nuna mata shi a kujerar dake kusa da tata cikin baby car seat,zagayawa tayi da hanzari
“Don Allah anty kwantomin shi”
“A’ah widad……ke kanki yaushe ummu ta daina goyaki?, barshi yanzu zan fito na kunceshi” bata rai tayi,wai me yasa kullum suke maidata baya,bayan ita kanta tasan girma take?,to idan ma har yanzu yarinyace ita a wajensu me yasa suke mata zancan uncle mahfood?,dole daga bisani anty dina ta ciro yaron ta miqawa widad shi,sannan suka nufi sassan mahaifiyarta tana ankare da widad din.
“Ke kuma wanne tsautsayin ne ya sanyaki daukar yaronki ki bawa wannan yarinyar?” Cewa momma mahaifiyar anty dina bayan shigarsu babban falon sassan nasu.
Kafin anty dina tace komai widad din ta rigata magana
“Momma Allah na iya fa,gash.i nan ma ni na daukoshi tuyn daga parking space” ta fada tana turo baki,wanda ke sake nuni da zallar quruciyarta,abinda ya sake batawa momma rai,taja tsaki tana miqa hannu gami da yunqurin karbar yaron
“Miqomin shi nan,me kika iya?,yarinyar da ko pant dinta har yanzu batasan ta wanke ba” momma din ta fada tana jifanta da harara,zallar quruciya ya hana widad fahimtar kuma,bugu da qari kuma,akwai wata irin wankakkiyar zuciya da take da ita,ba kasafai ta fiya damuwa da abubuwan da suke faruwa cikin gidan ba,duk da ta soma girma,hankalinta ya fara fahimtar wasu abubuwan
“Allah na fara koya momma”
“Naji,jeki da Allah” ta fada tana sake harararta kamar idanunta zasu fado,sai dauke dubanta daga fuskar momma din tana nufar hanyar kitchen dinta.
Wata tsawa ta kwatsa mata,wadda sai data sanyata ta kusa tuntube da kujerar dake gefanta
“Ina kuma zaki?” Ta fada tana fidda idanu
“Wajen Aafiya zani”
“Kiyi mata me?” Ledar hannunta ta daga tana nuna mata
“Kayan kwalliya na kawo mata ta zaba”
“Uhnnnn,salon kije kisa ta bata aikin dana sakata,to zauna nan har sai ta fito,kada ki shiga ku hadu ayimin shirme” narkewa tayi tana duban momma din,da alama tanason ta roqeta ne ta barta ta shiga,tana kuma tsoron tsawarta,don ba abinda ta tsana sama da tsawa da kuma fada.
“Ki barta mana momma,idan yaso tana shiga saita fito kada ta zauna” dina ke fada qasa qasa,saboda tausayi da widad ta bata,waiwayowa momma tayi ta kalleta tana dan juya aysar a hannu kamar zata masa rawa
“Wannan yarinyar?,tsab zasu iya barnatar min da guri,kuma baka da damar yi maya fada balle duka,tunda tana da uwa a bakin murhu”
“Kiyi haquri momma,yanzu zata fito”
“Naji,amma indai ta shiga din duk barnar da tayimin ke zaki biya”
“Na yarda” sai.anty dina din ta daga kai ta dubeta
“Shiga kikai mata kizo na aikeki sassan anty madina”
“Tohm” ta amsa da zumudinta tana shigewa,deena ta bita da kallo,bata fiya yin fushi ba don mutum ya bata mata ko ya tsangwameta,bata sani ba ko tsabar quruciya ce?,ko sai nan gaba zata fahimta komai idan hankali ya gameta?.
*KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*
*KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*
Littafi daya—400
Biyu—600
Uku—-800
Hudu—–1k
Biyar din duka—-1200
*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*π₯π₯π₯π₯π₯
0022419171
Maryam sani
Access bank
*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*
09166221261
π³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺ
*Ina yan uwa ‘yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*
+227 90 16 59 91
Littafi daya—450CFA
biyu—650CFA
uku—-850CFA
hudu—-1050 CFA
Biyar—-1250CFA
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*
*Thanks for choosing us*π₯
[1/23, 6:13 PM] It’s Queen MeenaliπΈπ»: *_A RUBUCE TAKE!!!_*
(k’addara ta)
Page 03
*MAAB LUXURY HOME*
*_idan kaji gangami akwai labari_*
*_SABUWAR DUNIYA CE_*
*ALFAHARIN UWAR GIDA*
*FARINCIKIN AMARYA*
*MAIDA TSOHON GIDA SABO*
*DUNIYAR QYALE QYALE*
*KAYA NA ALFAHARI DA TAQAMA*
*_Ba iya kyawun idanu suka tsaya ba,harma da ingancinsu da kuma qwarkonsu,ka dade kana mora kana kece tsara a tsakanin tsararraku da sauran mutane_*
*nasan zaku tambaya ina ne nan?*
*MAAB LUXURY HOME*
π *Kai daga jin sunan ma babu tambaya*
*_duniyar qawata muku gidajenku ku ganku kamar a wata nahiya ko wata duniyar_*
*Suna kawo kayan kitchen rankatakaf manya da qananu*
*Kayan gado dana parlor*
*Kai…suna kawo kowanne nau’in kayan ado na cikin gida*
*Karkiyi qasa a gwiwa kuma kada kiyi sake ma dafe,maza garzaya ki nemesu a*
_adress dinsu dake No 22 Ahmadu bello way,kano state_
*Ko kuma kuyi order din kayanku kuna daga gida ta shafinsu na instagram*
@maabluxuryhome
*Facebook*
@maabluxuryhome
*Ko ku nemesu ta lambar wayarsu kamar haka*
08034631010
*Kyau inganci da rahusa shine takenmu*πππ€π€π€π€
____________________________