Sponsored Links
Bakar Ayah Book 2Hausa Novels

Bakar Ayah Book 2 Page 45-46

Sponsored Links

Page 🖤 45••46🖤

 

Tsit taji falon lokacin da shiga babu kowa,saidai ta kasa kunne kafin tajiyo muryar maleekah inaga da Madeenah a É—akin su.
Hanyar wajen ta nufa harta fara jiyo muryar su.
“Waini kam maleekah meyasa kike min haka ne,sanin kankine rigar nan tunda na siyeta ban taba sakawa ba,shine kika É—aukemin”
“Kai wai ke babu dama a É—au kayanki ne saikin……”
Da bombee ta haɗa ido wacce take tsaye a bakin ƙofah.
“Uhm sannunku,yanaji gidan shuru,ko an sameta ne?”
“Ahah ba’a sameta ba anty maryam,suna sashen Iyah sayyada,barin rakaki can”
“Ahah ina shi Jabeer É—in yake?”
“Uhm yana É—akinsa na sashennan,muje na nuna miki”
Jefawa Madeenah rigarta tayi tareda yin gaba bombee tabita.
A bakin ƙofar ta tsaya tareda cewa.
“Gashinan maybe in yaganki ya yarda yaci abinci,amma babu abinda yaÆ™e Æ™ira sai sunan lubnah yana riÆ™e kai,ni wlh har na Æ™osa a ganta saboda halin dayake ciki”
Bombee bata ce mata komai ba,sai murɗa hannun ƙofar datayi ta shiga,a zaune yake a ƙasa yasaka kansa akan gadon.
A hankali take tafiya har ita isa inda yake ta zauna,hannu tasaka tana dafa bayansa.
“An sameta,ta dawo gida lubnah n?”
“Ahah bata dawo ba,saidai kasani tana cikin Æ™oshin lafiya,nasan inda take ma,idan har ka kwantar da hankalin ka zan kaika inda take”
Saurin É—agowa kansa yayi yana kallon bombee,wacce ta kawar da idonta,don bazata iya kallon yanda yakoma ba a yanzu,ya sanja kamanni yayi wani iri,ga tunanin sa ma yazama tamkar na yara.
Dan ma yanayin aikin yana ƙara kwanaki batareda yaganta ba abin kuma yana rabuwa dashi,dolene ya jure ya zauna a haka idan yanaso abin ya rabu dashi.
Cikin lallama da bi a sannu ta samu yaci abinci kaÉ—an yayi bacci,saida ta tabbatar babu matsala tukunna tafito daga É—akin zata tafi.
Karo suka ci da Hajiyah Zeenah zata nufi sashen alhj Aliyu,kallo É—aya tayi mata ta É—auke kanta.
“Uhm yanzu nafara share tantama ta,kenan kin kamu da soyayyarsa,tunda kika gagara haÆ™uri saida kikazo kika ganshi”
“Hmmm Hajiyah Zeenah kina bani mamaki,yanzu ki duba halin da É—anki yake ciki,amma duk a haka kike?.
Inkin san mai kike banice abokiyar hamayyarki ba yanzu.
Batun barinsa kuma basai kin faÉ—amin ba zan barshi,ai na bar nonon uwata ma kuma na rayu,kaman yanda na faÉ—a a farko to kuwa zan cika wannan alÆ™warin,sai hankalin ki ya kwanta”
Tana gama faÉ—in hakan cikeda bacin rai tabar cikin falon.
Madeenah da maleekah wanda suke tsaye akan idonsu hakan ta faru,harda su Abdulmaleek da abdulkareem da shigowarsu kenan sashen.
Kallo É—aÉ—É—aya bombee tayi musu kana ta rabe musu ta wuce.
Da kallo suma suka bita,ganin yanda tasamu ƙarfin halin gayawa uwar tasu magana kuma tayi tafiyarta cikin izzah.
Jan numfashi Hajiyah Zeenah tayi tareda barin wajen itama bayan bombee ta tafi.
“Wayyo shikenan mommah takai anty maryam bango tace zata tafi,nikam banaso ta tafi tabar ya Jabeer”
“Ke dallah rufemana baki,kaf gidannan kowa yasan rashin mutuncinta bandake,kullum kina mamuÆ™e da ita,bakya ganin akan idonki yadda ta gayawa Mahaifiyarki magana ido da ido,ke wacce irin Æ´a cd ne”
“Ehh nagani amma kaff cikinmu akwai wanda ya iya kwantarwa yah Jabeer hankali tunda abinnan yafaru,amma daga zuwanta gashi nan har yayi wanka yaci abinci yayi bacci.
Kafin aurensa da waÉ—ancan matan da gwanda babu su,itake kulada wankinsa,dukiyarsa,cinsa,shansa akan lokaci,sannan in an kawo masa hari kafin yasani ma tasan da abin.
Bazaki ganeba saboda bakisan mai yake faruwa ba,nima bansani ba sai ta sanadiyyar ta,amma yah Jabeer yana kewaye da mugayen mutane bila adadin,zamanta kusada shi wani taimakone da allah yayi masa.
Kodan kwai mutum yanada zafin hali kuma yana bayyana gaskiyar mai yake ransa sai ya zama azzulumi da tantiri,ina jiyemiki ranar dazaki gane mutanen dakika É—auka mutane ashe dabbobine masu fatar mutum”
Maleekah tana gama faÉ—awa Madeenah haka tabar falon cikin bacin rai.
Sukuwa su Abdulmaleek da basu san kan lamarin ba sai aka barsu da wasiwasi,dan ita kanta bombeen ganinsu na farko kenan da ita.

Hilyan ce riƙeda kwanon abinci,saida ta sincewa lubnah hannu kafin ta tura mata abincin,kallon kwanon tayi kaman mai nazari kafin ta miƙa hannu ta ɗiba takai baki.
Yau kimanin sati biyu kenan,duk wata magiya babu wacce batayiwa bombee ba,amma taƙi sinceta,har yazamana yanzu ta daina magana ma sai bin hilyan da ido kawai idan zata bata abinci..
KuÉ—aÉ—e kuwa sun Æ™arbi akallah yakusa miliyan hamsin ko sama a wajen brr na’imah,amma har yanzu shuru tana jiran dawowar Æ´ar ta.
“Uhm yafimiki kam takika daina magana,dan tunda ta yanke miki saikinyi wata gudannan to babu fashi”
“Dan allah to idan bazata sakeni ba kice mata ta kawomin Jabeer na ganshi inyaso”
“Hhhhhh wannan kuma ki bari sai tazo inyaso saikiyi mata bayani.
Ni nayi zaton kin zama kurmiya,ashe kina magana sarai kenan”
Cigaba ta cusa abincin tayi tana hawaye da majina,a ranta tana fatan bombee ta yarda ta kawo mata shi.
Kaman yanda tafaɗamata babu duka babu zagi,wanda tasa su kulada ita suna bata abinci mai kyau da lafiya,saidai fargabar abinda zai sameta yasa ta ƙanjame ta rame,babu wannan ƙibar ta da duk ta tafi.
A bangaren Jabeer kuwa yanzu yafara dawowa daidai,saidai har yanzu bayayiwa kowa magana,yana dawowa daga aiki zai shiga sashen lubnah ya zauna. A cewarsa umarnin data bashi kenan,kuma yasan zata dawo da sameshi.
Kaff gidan hankalin su yayi mungun tashi da wannan É—abi’ar tasa,hakanne yasa ake tunanin Æ™arbar kujerar CEO daga hannunsa,wanda kuma duk Alhj Abdullahi ne mai Æ™arfafa maganar.
Itakuwa bombee duk abinda suke tana jinsu,kallonsu take kawai a baibai na gameda shirin dasuke,tsakanin Lailah da Alhj Abdullahi.

*** ***
Tun safe bombee suke kan inna Danejo,sai sanÆ™amewa take,sai anyi mata tofi da ruwan Addu’a Kafin take dawowa daidai kaÉ—an.
Innayi ce takalleta cikin muryar kuka tace.
“Dan allah addha bombee yanzu kam mu kaita wajen mai magani,wlh abinnan nata Æ™ara tsauri yake,gashi kullum jikinta Æ™ara laushi yake saboda ciwon,ko bazaki iya ba nida su hilyan zamu kaita idan yaso,dukkanmu munsan uzurinki,kuma munga Æ™oÆ™arinki akan abubuwa da dama namu,wannan karon dakika gaza ki barmu muyi Addah bombee”
Hannun inna Danejo ta riƙe gam tanajin abinda innayi take faɗa,duk dauriyarta da kuma jajircewarta tagagara kaiwa Mahaifiyarta magani,wannan wacce irin ƙaddara ce.
Tashi innayi tayi ta É—auko hijabinta tasaka,inna Danejo ma ta sakamata nata.
Hilyan ce ta inaya suka kinkime ta zuwa cikin motar bombee,har suka kaita tana nan zaune a inda suka barta bata motsaba.
Hilyan ce tashigo É—akin ta dafa ta.
“Karki takurawa kanki dayawa harki samu matsala anty maryam,idan bazaki iyaba ki kawo makullin nakaisu,ai nasan gidan malamin,kuma dama kin biyashi kuÉ—in aikin tun wancan karon,wannan karbo maganin bazai yiyuba dole sai ya ganta tukunna”
“Uhm uhm hilyan zan iya zuwa,bazan zama mai tsoro ba,haka suke so bazan basu dama ba”
Tashi tayi ta ɗauki key ɗim motar,yayinda itakuma hilyan ta riƙo Haidar a hannunta suka fito daga gidan.Basuyi tafiya mai nisa ba cikin ikon Allah suka isa gidan,dan ma bombee tana tafiyah a hankali kaman bataso,kowane gudu kaɗan ji take kaman ana zare mata laka,amma taƙudura a ranta dolene taje yau a yita ta ƙare.
Wani yaronsa ne yayi musu iso zuwa cikin falonsa inda yake ganin marasa lafiyah,har sannan inna Danejo batasan inda kanta yake ba,ta sanƙare kaman gawa.
Cikin gaggawa yafara da yimata Addu’a da kuma yayyafen ruwan magani wanda zai taimaka.
Yadaɗe tana yi kafin aka samu naman jikinta yasaki daga ƙanƙamewar dayayi.
Duk abinda yake bombee tana gefe guda tariƙe kai bata sanma mai suke ba,kowacce kalma idan ya furta ji take kaman kanta zai fice daga gangar jikinta,ita kaɗai tasan mai takeji a lokacin.
Yanayima inna Danejo karatu,amma ta gefe ɗaya kuma yana kulada da yanayin da bombee take shiga,duk da tana iya ƙoƙarinta wajen bata nuna mai yake damunta a fili ba.
Wasu mata guda biyu ya ƙira suke shigo wajen,tashin Danejo sukayi tsaye Wacce jikinta yayi sanyi kaman babu laka..
“Kukaita É—akin turare,ku tabbatar kusaka a kowacce Æ™usurwa”
“To mallam”
Daga nan suka bar wajen sai iya bombee dasu innayi,gyaran murya yayi tareda gyara zama yana kallonsu.
“To Alhamdulillah an samu nasarar shawo kan matsalar,saidai fah gaskiya jikinta yadaÉ—e tana jure abin,a kowanne lokaci komai zai iya faruwa wanda ba,a fata,dan haka tana buÆ™atar magani gaggawa.”
“Uhm malm kaman ya kenan?”
“Maganin dazamuyi mata zai É—auki lokaci,sannan ita,kuma jikinta yana buÆ™atar maganin akan lokaci ne,to maslaha É—ayace saidai itakuma ba lallai a yita ba”
“Waccece faÉ—amin ita naji”
Shuru naÉ—an lokaci batareda yace komai ba,yayinda dukkan wajen kuma suke jiran dakon abinda zai faÉ—a.
“Uhm mafitar itace a kashe bokan dayayi wannan aikin,idan an sanshi kenan. Ta hakane aikin daya kulla a rayuwarsa zasu bar kan wanda yayiwa sukoma kan wanda yasaka a yimasa,zance anan kenan ba iya bokane zai mutuba harda wanda yayi aikin shikuma abinda wancan yake fama dashi to kansa zai koma”
“Indai ta wannan ne angama,da banyi niyyar kasheta yanzu ba,amma tunda ya taba kan innata to banida zabi,dolene kuma mataki yabiyo baya,yanzu inaso ka faÉ—amin tsawon wanne lokaci zata iya kaiwa a wannan halin da take ciki?”
“Tsawon kwana ukune,saidai kina abin zaikai harga kisa kuwa?”
“Kisan wanda yayi kashkashe ladane,saidai kafin akai gayin hakan akwai abinda nakeson aiwatarwa,dan Allah ka kulamin da ita kafin lokacin,ni barina tafi”
Tana gama faɗin hakan tabar falon da sauri,su Inayah sai tsinkayota sukayi a mota,dan ji take kaman akan ƙaya take.
Bayan sun fara tafiya a mota kallon innayi tayi ta glass,wacce ta rungume Haidar da cinyarta tana kallon window,saidai kana gani kasan hankalin ta yana wani waje daban.
“Innayi kinji abinda mlm yace,sannan kuma idan na aikata hakan dole,zai shafi inna laari!! Am sorry i have no choice but to do it”
“Karki ce haka addah bombee,duk da cewa uwa uwace kam zanji babu daÉ—i,amma a yanxun ma ba daÉ—in rayuwar takejiba ai,tana girbar abinda ta shuka,a yanzu ni kaina nafison samun lafiyar inna Danejo,saboda ita nake gani a matsayin inna ta ba inna laari.
Duk abinda tayimin na yafemata a matsayinta na wacce ta haifeni,saidai babu wanda zan tursasa a waÉ—anda ta zalunta su yafemata,dolene ta tone abinda ta shuka”
Daga haka kaff cikin motar har suka isa gida babu wanda yace wani abu.
Waya bombee ta ɗauka taƙira khmees,wanda yau shikadaine a wajen lubnah,inshine kuwa dama bata magana,ta koma tamkar karya saboda ɗaurin dayake jikinta.
“Hello khmees ya wanann matar take?”
“Gata nan taci abinci yanzu”
“Okay a yau akwai gagarumin aiki da kuma gobe,inaso ka Æ™ira brr Na’imah kace mata na shiryah haÉ—uwa da ita a yau da yamma a bayan gari,kaje kai da yaranka ku satomin ammar ma É—anta,domin inaso kada tayi min gardamar abinda zan tambaya. Ka tura mata hotunansu dukka kace ta fanshesu da share companyn jaan data mallaka da mummunar hanya,idan kuma ba haka ba to kace tayi bankwana dasu”
“Angama shikenan,yanzu ma kuwa zamu danÆ™oshi,GPS É—insa yana nuna hotel ne,da alama yana can yana kashe arna da ranar nan,scamp message zamu turamasa kada ki damu”
“Shikenan duk yadda kukayi,ganan hilyan ma zata zo,idan kuka gama tsarawa ku yimin text da yamma”
Tana kashe wayar ta karbi É—anga tanufi gida,dukka tareda su inaya,wacce zata sauÆ™eta anguwar su brr na’imah wajen aikinta na spy.
Tana isa gida abinci ta ɗora marar wahala,ta zubawa innayi taci,saboda kowa yaganta yasan tana buƙatar a zauna tareda ita,saida ta tabbatar taci abincin tashiga wanka,kafin ta nufi ɗakinta na study.
Wajen wasu computer taje guda biyu da akayi musu connecting da CCTV camera,a ƙalla kusan guda shida,dukka kuma na bangaren Jawaheer ne da Jaleelah.
Dariya tayi mai É—auke da takaici bayan tagama ganin abinda yayi record a ranar,kaman yanda tayi tsammani harma yafi haka,yanzu tariga tagama sanin mai yake wakana a gidan.
Sending vedion tayi ta email É—inta,kafin ta rufe É—akin ta fito.

********

“Me kake faÉ—a kaikuma yanzu haka inspecter,yanzu an tafi kusan sati uku kenan da batan Æ´a ta,har yau kuma ba’a sameta ba,kuma yanzu kasake Æ™irana kace wai É—a na ma an É—aukeshi,kunsamu motarsa baya ciki?”
Maganar take kaman zatayi kuka,tama rasa yazatayi da gashin hankalin dayake zagaye da ita.
Katse ƙidan insectern tayi jin message yashigo wayarta,hotunan ammar ne shida lubnah,dukka an ɗaɗɗauresu tamau kaman awaki.
Zare glass É—in idonta tayi tana sake kallonsu,yaraf takoma dabaya ta jube akan kujera jikinta sai rawa yake.
Gen abdu manga ne yashigo gidan da waya a hannunsa da sauri,da alama shima yaga abinda tagani,samun waje yayi ya zauna a kusada ita.
“Dear ki kwantar da hankalin ki,ki daina saka damuwar nan,inshaallah za’a gansu dukka batareda wata matsala ba.
Bama sai ankai da basu takardun dasuka buÆ™ata ba,Æ´an bincike zasu nemo su”
“Ƴan binciken mai suka tsinana har iyanzu,kai kanka baka fini rashin son bada abinda suka buÆ™ata ba,saidai ka bari kawai,tunda har suka tambayi takardun share na JAAN,to na tabbata a cikin gidannane wani yasan mai muke aikatawa,musamman ma Lailah da mijinta,idan na karbo Æ´aÆ´ana saina É—aiÉ—ai ta rayuwarsu.
Kaje ka kawomin takardun nan yanzunnan”
“Waikina nufin basu zamuyi,bakya fa son rabuwa da takardunnan?”
“Dallah kaje ka kawomin su,idan banason rabuwa dasuma yazanyi,a tunanin ka shikenan na nahaÆ™ura daman,ammar dazai hau kujerar yana hannun su,itakuma lubnah banason takai wata guda a wajensu itama,domin akwai gagarumar matsala idan hakan ta faru”
“Wacce irin matsala kuma?”
“Bai shafeka ba,ka É—au takardun kakai musu inda suka buÆ™ata bayan kayi sign,kace musu basai na haÉ—u dasu ba,domin basuda wannan matsayin a wajena.Sunce sai gobe zasu sakesu,kada ka basu takardun harsai ka tabbatar sun sakesu É—in tukunna,haÉ—uwata da ita kuma kace basai na haÉ—u da ita ba,saboda nasan bazata wuce Lailah ba”
Maida glass É—inta tayi tabar falon,saidai kana ganin jan idonta kasan tashin hankali ne kwance a cikinsu.
Kaman yanda tafaɗa,gen abdu manga ƙiran khmees yayi domin ya faɗamasa inda zai ajiye takardun,da kuma inda zai ɗau yayansa.

**** ****

Kasancewar da daddare zasuyi musanyen,tunda farkon dare tawagar gen abdu manga sukayi likimo a wajen ƙarbar su lubnah.
Sai can wajen shabiyun dare kafin suka ji ƙarar waya,tun kafin khmees yayi magana gen abdu manga yace.
“Yah ka kawosu,gani nan a wajen daka kwatanta É—auke da takardun”
Saida khmees yasheqe da dariya kafin yace.
“Hhhhhh akwai wata motar katako zatazo wucewa yanzunnan,ka jefa a cikin motar,ina kallonku daga nan,idan har wani yayi yunÆ™urin bin motar kafin ta bace,to zan harbe kan namijin a take.
Kuna jefawa in motar tatafi,to zakaji address É—in inda Æ´aÆ´an ka suke a wayarka ya shigo.”
Hakan kuwa akayi,tun kafin khmees ya rufe baki motar tazo wucewa,kasancewar a hankali take tafiya,har yasamu damar jefa takardun a bodin.
Tana bacewa ganinsa kuwa yaga message É—in yashigo.
Signa yayiwa wasu mutanensa kansu bimotar,yayinda shikuma yanufi inda su lubnah suke.
Kaman yanda yafaÉ—a kuwa suna É—aure damau a wajen,jikinsu duk yayi ja saboda É—auri.
Yana farinciki yasamesu,saidai kuma ƙira yasameshi kan cewar sun samu motar,amma kuma babu takardun a ciki,shikuma drivern da alama bai ma san mai yake faruwa ba,kawai plan suka haɗa dashi a ciki.

Mashallah sai ku tara damu a give kuma domin jin mai zai faru a dokar daji tsakanin bombee da kuma Zilliyyah……..
Shin asirin zai karye ko ahah.
Taku sadi-sakhna…..

 

 

 

 

 

_*SADI-SAKHNA CEH*_

 

____****🖤🖤****_____

🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤

🖤 _BOOK 2_ 🖤

 

Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

 

Anshiga Sashen na KuÉ—i,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka É—au hakkina bisa kanka tamm!!!

Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin

https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31

Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150

Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU

Mutanen niger kuma zaku biyah kuÉ—inku tanan
300f
+227 97 21 16 15
Shaida tanan
09035784150

______________****_______________

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button