Sponsored Links
Dabi'ar Zuciya Hausa NovelHausa Novels

Dabi’ar Zuciya 33

Sponsored Links

Suna shiga masallacin ana shirin tada sallar,yau masallacin a cike yake saboda addu’ar ukun bilal,don haka basu samu sahun gaba ba,sai a can baya suka zauna.

Kamar ko yaushe aka idar da sallah,saidai yau mafi yawan mutane basu motsa ba aka fara gabatar da addu’o’i wa bilal,wanda aka dauki kusan minti talatin anayi kafin a kammala.

Niyyar tashi samir yayi,sai amiru ya danneshi,dubansa samir yayi

“Ka zauna malam,ai ba’a gama ba” kamar zaiyi magana saiya fasa,ya koma ya zauna,dai dai sanda malam amadu ya miqe

“Jama’a akwai wanda keda sha’awar auren diyata kaltume?,idan har babu zan bada ita yanzu ga dan uwanta auwalu” maganganu ne qasa qasa suka fara tashi,tsahon wani lokaci shuru sai qananun maganganu

“Akwai wanda ya shirya?” Malam amadu ya sake jefa tambayar ga mutane

“Akwai” babu zato bare tsammani muryar amiru ta sauka kunnen samir,da sauri ya waiwaya ya dubi amirun,suka hada ido,sai ya fuske masa,tsoron halin amiru daya sanshi dashi ya darsu a ransa,yasanshi sarai,komai yana daukarsa wasa ne koda gaske ne,hakanan yana iya fadar magana a cikin wasa ka ganta a zahiri a aikace

“To alhmdlh,yaro kaine zaka karba ko?” Malam amadu ya fada yana murmushin samun wanda zai baiwa kaltume din,kai amiru ya gyada

“Ni zan karba,nawa sadakin?”

“Aiko nawa kake dashi yaro ka bayar” mai gari ya amsa wannan karon.

Tun samir yana ganin abun a wasa,sai gashi ya tasamma zama gaske,mutane sun fara matsowa ana dai daita magana,har takai ana buqatar amiru ya miqo sadaki.

Aljihunsa ya shafa,bai fito da komai ba,amma kamar yaga samir yana zuba kudi a aljihunsa,wanda yace zai qarasa biyan ma’aikatan kudin gininsu,saboda a gobe yake son a bude makarantar

“Aramin dubu talatin mana”

“Baka da hankali amiru?” Ya tambayeshi qasa qasa yana zuba masa idanu a rikice

“Yaro miqo mana,ko ila ajalin za’ayi?” Mai gari ya tambaya amiru,bayan sun gama magana qasa qasa da malam amadu kan baqin fuska ne,shin ya aminta a daura auren diyarsu dasu yace ba komai,zai bincikesu daga baya.

“Gashi….shi ya karba min ne,za’a daura auren da sunan muhammad samir,shine waliyyi na” samier ya fada yana miqa kudin daya irgo.

Baki da hanci amiru ya sake,ya jima da sanin cewa samir ya fishi sanin takan tsiya,idan ya debo rigimarsa dama shi kadai ke iya solbata,wannan abun da samir yayi masa yasan da manufa a ciki,bai sake tabbatar da haka ba sai da suka hada idanu ya banka masa harara.

Cikin lokaci qanqani aka daura auren muhammad samir da ummu_kulsum kaltume,wanda ana gamawa mutane suka fara watsewa kowa ya tafi da lamarin a bakinsa,ta yaya malam amadu zai dauki diyarsa ya baiw baqo?,duk da an dan sanshi sakamakon aikin makarantar da sukeyi?.

Raguwar da jama’a sukayi ya basu damar ganawa da me gari,shi ya damu yadan yiwa su samir wasu tambayoyi,da suka shafi cikakken sunansa da kuma garinsu da sunan mahaifinsa,dukka ya gaya musu,saidai ta sigar da bazasu gane waye ba,me garin yadan masa nasiha kan ya riqe amana,shi kuma ya shaida masa an bashi umarnin gobe a bude aikin makarantar da aka gina daga mai gidansa,murnar wannan ya sanya zancan auren yadan lafa,har gari yayi haske suna tare da me gari,tuni samir yaji ya gaji,sai yace zashi gida akwai saqon da za’a kawo,a sannan ne malam amadu da shima ke shirin tafiya gida don ya shaida musu daurin auren kaltumen yace

“Zaka leqa kaga amaryar ne ko kuwa?” Kansa daya fara ciwo ya girgiza

“Zanzo baba daga baya”

“To…to saika shigo”

Baiko samu sararin amsa masa ba yayi gaba,amiru da bakinsa ke cike fal da tambayoyin da ya gaza samun amsarsu ya dafa masa baya…

Tunda suka fito yake jefa masa jerin gwanon tambayoyinsa amma bai kulashi ba,har sukayi nisa,suna haramar tadda gida

“Kace wani abu mana….waime ka shirya ne?” Ya sake tambayarsa wannan karon adan qage saboda yadda ya gaza samun amsar kowacce cikin tambayoyinsa.

Ba zato yaja cak ya tsaya,sannan ya waiwayo ya zubawa amirun idanu na wasu lokutta,har sai dashi amirun ya gaza daukar kallon samir din,gwani ne shi wajen iya hukunci da idanu,ya san da wannan tun ba yau ba

“Idan kai zaka dinga wasa da rayuwarka kana daukar hakan ba’a bakin komai ba….ni bazan dauki wannan ba,akanme zaka rakitowa kanka auren gangan amiru?,oh….da nufinka shine kayi yadda ka gayamin ko?,ka gama tsara hakan,me yasa?”

“Kai me yasa ka tare auren?,me yasa ka bari ya fada kanka?” Ya maida masa tashi tambayar cikin damuwa,don har ga Allah ya shiga damuwa,yace zai karba auren ne ba don wai yana nufin hakan ba har cikin ransa,ya fadi hakanne saboda yana ganin ba zasu bashi ba,kasancewarsa baqo kuma baquwar fuska a garesu,zasu qalubalanceshi akan hakan.

Ajiyar zuciya samir ya saki,shi dinma yace shi zai karba ne saboda shigen irin tunanun amiru,ta yaya zasu bawa mutumin da basusan waye ba auren diyarsu?,ashe wautarsu ta wuce duk inda yake tunani

“Na karba saboda na shirya sakinta ne da zarar kwadayin ubanta na aurar da ita ya fada,kuma hakan zai faru daga yanzu zuwa anjima,zuwa safiyar gobe da zan gama aikin daya kawoni garin na tattara na koma duniyata…..amma ka sani,kada ka sake gigin sake aikata wani kuskuren makamancin hakan,saboda idan kayi yanzu ka tsira,gaba zaka iya rasa wani abu da baka tsammata ba” daga wannan ya saki hannayensa da ada ya rungumesu a qirji ya soma takawa.

Sai amirun ya kasa cira qafarsa daga wajen,ya bishi da kallon mamaki,duka yayi wannan abun ne saboda shi,ya dauki wannaj risking ne saboda shi,saboda ya tunkudeshi daga fadawa wanan matsalar,shi yasa a rayuwa yayi amanna da qaunar da samir yake masa wadda babu na biyunta,baya ga qaunae mahaifiyarsa a gareshi,wannan tunaninnm ya bashi qwarin gwiwar cira qafarsa da hanzari yabi bayansa.

Yauma gidan akwai jama’a dake ta shigowa gaisuwar sadakar uku suna fita,sai kuma wasu daga cikin ‘yan uwa na kusa sosai da suke tare da ummanmu,kamar su yakumbo indo,da umma altine habi sa sauransu.

A filin tsakar gidan suke zaune saman tabarmi,a yanxun sai iya su isu,habiba da kaltumee na saman tabarma daya su biyu suna hirarsu qasa qasa,wanda su kadai sukasan me suke tattaunawa.

Sallama yayi ya shigo,suka amsa masa,masu masa sannu da zuwa sukayi masa,ya gaisa dana gaisawa,sannan ya dubi kaltume

“Ki kiramin babarku,kuzo keda ita” sai ya qara gaba yana bude dakinsa.

Jikinta a matuqar sanyayen da batasan musabbabinsa ba tun dazu ta miqe,ta shiga dakin ummanmu ta shaida mata.

Tare suka fito da ita suka nufi dakin nasa,zuciyar kaltum na wani irin bugawa da saurin da bata taba jin irin hakan ba,har kamar ana dan matsa zuciyar tata ne.

Gefan gadonsa suka cimmasa a zaune,ya baza babbar rigar jikinsa yana dakon isowarsu,gefe daya ummansu ta zauna,sai kaltun din ta bita ta zauna a jikinta tanajin jikinta yayi wani irin laushi.

Gyaran murya yayi kamar me shirin fara karatu,sannan ya dubesu,kanshi tsaye yace dasu

“Kamar yadda nace,na kuma alqawarta,to na bada auren kaltum” a tare maganar ta bugi kowannensu,kaltum da batayi shirin kallonsa ba,batasan sanda ta daga kai ta dubeshi ba.

Ya fahimci irin kallon da suke binsa dashi,a karon farko kuma yaji yadan daburce

“Eh,yau dai nima na sauke nauyin da yake kaina,na aurar da sauran ‘yata data ragemin,zanyi bacci kamar kowanne uba” mamaki mai girma ya kama umma,taci gaba da kallonsa kamar wani sakarai

“Waye ka aura mata?” Dubanta yayi yana matse fuska

“To meye na gaggawa?,koma waye na aura matan ai zaku ganshi,tunda kunqi auwalu ba shikenan ba an muku abinda kuke so?” Yayi maganar cikin fada fada,saboda baiso taci gaba da tambayarsa waye mijin?,don idan hakan ta faru bashi da amsar bata,shi kansa baisan waye ya aurawa kaltum din ba,amma koma waye yasan babu abinda zai faru bazai cinyeta ba,a iya nasa dan qaramin sanin da ya yiwa duniya kenan.

Can qasan ranta umman ta saki ajiyar zuciya,tana jin fiye da rabin tashin hankalinta na kwaranyewa,saidai kuma akwai sauran fargaba a tare da ita,don batasan waye ne ya dauko ya maqalawa kaltum din ba,taji ranta yana motsawa,tausayi da bacin rai suka cakude waje daya suna karafkiya cikin ranta,kamar ba zata tankashi ba saita kasa,duban fuskar kaltum kawai ya daga hankalinta

“A wannan zamanin?,a irin wannan lokacin zaka yiwa diyarka irin wannan auren na rashin siyar daraja da mutunci?”

Idanunsa ya bubbude sosai yana hura hanci,baya so kuma baya sha’awar tayi masa wata magana,kota kawo masa tarnaqi kan hukuncin daya yanke ko misqala zarratin,don baiga uban daya isa yasashi ya janye wannan hukuncin ba

“Ke zuwaira ki fita daga ido na,ita din uban wace da bazan zaba mata miji ba?,ina cewa yarinya budurwa uba ne dama yake da haqqin zaba mata miji,shine zaki hurewa yarinya kunne ki sakata ta bijiremin?,to wallahi ta gwada,bismillah,ga fili ga me doki nan,nida ku uban wanda ya fasa” da alamu jama’a yakeson tara mata,saita miqe tana riqe da hannun kaltum zuciyarta na quna

“Ko da wanne lokaci fa zan tattarata a miqa masa ita” ya bisu da kalmar sanda umman ta kama hannun kaltum da tuni hawaye ya jiqe mata fuska,tsantsar tashin hankali kuma ya cika zuciya har saman fuskarta.

Mamaki ya kuma kama umman,wanne irin abu ne kuma haka,a daura ma yarinyar aure ba tare da tasan mijin ba,sanna ace ta shirya kowanne lokaci zata iya barin gidansu?,babu wani shiri tanadi ko sakawa rai?,mema suke dashi da zasu kaita dashi?.

Kamar yasan tunanin da takeyi saiya fiddo sadakinta daga aljihunsa,wanda sai daga baya daya nutsu ya lissafa yaga dubu arba’in da daya harda dari biyar akai,yana da yaqinin zata yi ma yarinyar kayan daki,ya lissafa ya dauki dubu ashirin ya miqa mata

“Nasan dai tunanin da kike,gashinan ayi mata wani abu dasu wanda zata tafi dasu,daga baya aje ayi mata jere”

“Amma wannan wanne irin al’amarine fisabilillahi malam?,wannan abun fa kwata kwata baiyi dai dai ba,yadda kake da haqqi a wuyanta itama tana da nata haqqin…..” Saiya zaburo ya fara maganganu,maganganun da suka sanyata dole ta janye kaltum,suka fice ranta a mugun bace.

Kasa riqe kukanta kaltum tayi sanda suka koma daki,su yakumbo suna tambayar lafiya?,ganin yadda yanayin fuskarsu ya nuna zallar tashin hankali.

A karon farko bayan dukka abindanya faru,qwalla ta subuce daga idanun umman sanda take gaya musu abinda ya faru,ran yakumbo a bace ta miqe

“Haba,wannan abun yayi yawa,bari naje na sameshi,yarinyar yar tsana ce ita da za’a bada ita sadaka?,batasan miji ba miji bai santa ba?,sannan ace a shirya kowanne lokaci za’a kaita?” Harta sanya kai kawu ado ya shigo gidan,ta dubi qofar dakin amadu a kulle,da alama ya fice abinsa

“Ke kuma lafiya kamar wadda aka koro” kawu ado ya fada yana kallon fuskar yakumbo indo data cika da bacin rai

“Shigo daga ciki yaya” ta fadi tana juyawa dakin umma,saiya sanya kai shima,ya samu kujera yaja ya zauna.

A taqaice yakumbo ta labarta masa komai,sai yayi shuru yana jinjina kai,tabbas lamarin ya bugeshi ya kuma bashi mamaki,hakanan tun a hanya daya taho aka bashi labarin,saidai bai gasgata ba,ganin labarin yayi kama dana qanzan kurege.

“Da farko mu soma aiki da hankali tukunna,dukkaninmu nan amadu ya fimu iko da diyarsa kattume,hakanan a cikinmu babu wanda ya isa yaja da hukuncin daya yanke akan diyarsa koda gaban alqali akaje kuwa….saidai idan ita yarinyar taja da kanta,idan akwai abinda zamu iya cikin wannan lamarin bai wuce mu bashi shawara,mu kuma nusashe da shi ba,idan ya dauka haka mukafi so,idan bai dauka ba kuma,mataki daya zamu dauka,mu binciki halayyar yaron sana’a gami da nasabarsa,idan muka tabbatar da bashi da matsala a dukka wadan nan,sai muyi haquri,mu bi auren da addu’ar sanyawar albarkar ubangiji” a hankali zukata suka soma sauka daga bayanan da kawu ado yayi,ga duk me nisan hankali a cikinsu idan ya yiwa kalaman kallo na tsanaki,zai hango ya kuma shanshano gaskiyar zancan kawu ado,saidai ko daya zuciyar kaltum bata rusuna ba,saima tashin hankali data sake shiga dajin zancan kawu adon,yana nufin kenan a haqura a miqata ga duk wanda baban nata ya bata aurensa?,saita sake fashewa da kuka cikin tashin hankali.

*******A nutse yake shiryawa duk da cewa yayi nisa a tunanin da yakeyi,har ya gama shirinsa tsaf,ya dawo a hankali ya zauna gefam katifa yana jan kayan breakfast dake saman wani babban tray da niyyar yin break aamiru na zaune saman wani stool yana dubanshi,hannayensa goye a qirijinsa.

Hannayen nasa ya saki yana sauke ajiyar zuciya,fuskarsa da alamun damuwa yace

“Am asking you since yesterday…..ya zakayi da auren nan,bakace min komai ba” kamar ko yaushe harara ya watsa masa yana hada tea din,sai daya kammala ya riqe kofin a hannunsa zaikai baki sannan yace cikin wani irin soft voice

“Da zaka dameni duk ba kaine ka jawo komai ba?,dana sani ma na qyaleka,idan yaso in ka koma hajiya qarama tayi banda da namanka” duk da tasirin damuwar dake tattare dashi amma sai daya daara,kana ya koma ya daidata zamansa sosai,cikin seriousness yace

“Am bother to ask you ne saboda hajiya qaraman da kuma boss professor,but u are feeling bossy,sai wani jamin aji kakeyi”

“An ja makan,idan kaji haushi ka barni da matsalata” kafada amirun ya dage

“Kome zakace zan dauka,saboda bamu saba hadiye damuwoyinmu mu kadai ba” qaramin murmushi ya subucewa saraki,saiya aje cup din a gabansa,ya hade yatsunsa waje guda yana kallon amirun

“Wani abun mamaki,ban dauki wannan abun daya faru a bakin komai ba,but amma sai naketa jin nauyinsa a kaina tun jiyan?” Shuru ya ratsa tsakani,amiru ya saki ajiyar zuciya,muryarsa tayi sanyi fiye da dazu

“Ni kaina gaba daya tunani na ya qare akan yadda wannan al’amarin zai warware….ni inaga…..me zai hana ka qara ko one week ne,ka more sadakinka kawai,daga nan ka rubuta masa takardarta kawai ka maidata gida?” Wanu banzan kallo ya jefa masa

“Kana tunanin zan iya hada jiki da wannan yarinyar?,kai anaka tunanin yarinyar ma dukanta ta isa wani moro ne?” Kai ya kada
“Ba haka nakeson matata ta kasance ba,baya ga haka ta yaya zan cutar musu yarinya?,na karbe mata darajarta kuma na rabu da ita alhalin bata yimin komai ba?”

Gira amiru ya dage
“Ok,kawai ka gama bude school din muyi tafiyarmu,dole idan suka gaji da nemanka su warware abinsu su ba wani” fuska saraki ya matse yana dubansa

“Ya kakeson canzawa daga amirun dana sani ne?,ka manta who iam?” Shuru ya sake biyo baya,idanunsa ya janye ya dauki cup dinsa ya sake kurban tea sannan yace

“Zanje kawai na basu haquri kan ban shirya ba na karbi aurenta,zan rubuta mata takardarta na bata kawai shikenan an wuce gurin,ba wani yaudara ko kwana kwana” kai amiru yake jinjinawa,yasan halin samir,dama ba zaya dauki shawararsa ba,yana tarar komai gaba da gaba ne,bai iya boye boye ko qumbiya qumbiya ba,idan kuwa har kaga yayi hakan,to ba qaramin abu bane.

Sanin cewa koda ya sake cewa wani abun,hakan bazaisa samir ya sauka daga ra’ayinsa ba,saiya miqe yaci gaba da shiryawa,dai dai sannan umar yayi sallama ya shigo

“Ka dauki kayanmu duka ka saka a booth,get ready….ana gama bukin bude makarantar gida zamu wuce direct,ya kamata nayi facing my agendas”

“Ok sir” umar ya fada yana jan babbar jakarsa daya zuba komai nasa a ciki yayi waje da ita.

Taro akayi sosai na bude babbar makarantar primary da secondary ta me tafasa,wadda aka canzawa suna,kamar yadda samir din yakeyi a duk sanda yayi wani aiki.

Bangaren primary daban,na secondary daban,ga bandakuna da offices na malamai,abun dai masha Allah gwanin sha’awa,za’a iya gabatar da karatun boko da kuma islamiya duka a ciki.

Duk wani motsinsa yaro daya ya tsaye masa a rai wato bilal,ya dinga kallon guraben dayafi yin aiki a guraren,a irin wannan ranar yayi masa tanadin abubuwa masu yawa da zasu inganta masa rayuwa,saboda yadda ya karanci yana da buri kan yayarsa da mahaifiyarsa,saidai tsarin ubangijinya danne,ya kuma shafe tsarun dukkan wani me tsari.

Farincikin daya gani saman fuskar al’ummar mabuqata,talakawa bayin Allah shi ya dasa nasa farincikin da walwala kan tasa fuskar,har cikin zuciyarsa ya dinga jin farinciki da nishadi,he believes a rayuwa babu abinda yafi ka farantawa wanda yake da buqata ta hanyar biya masa tasa buqatar,yana jin abu daya ne a yanzu ya rageshi a duniya,RASHIN UWA MAHAIFIYA DAURA DASHI,KO TANA INA???,itace tambayar da yake yawan yiwa kansa,yana da tabbacin tana raye,saboda karo na barkatai da yasha yin mafarkinta tana gaya masa cewa tana raye,amma wani SHAMAKI data sanyawa zuciyarsa yasa ya kasa yunqurin komai wajen isa gareta.

*_WAIWAYE……ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau’in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

*_SANIN HALI…..yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*

*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*

*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*

*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*

*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*

*_ƊABI’AR ZUCIYA👉🏾huguma_*

*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR…ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*

2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000

*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*

09134848107

*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button