Dabi’ar Zuciya 15
*_ka/ki gujeta!!!_*ππΎππΎππΎππΎππΎ
*_Dabi’ar da zata iya sanya ubangiji yayi maka kaca kaca!,RIQO QULLACI KO KWANA DA WANI DAN ADAM_*
*_Me yiwuwa wanna bawan da kake kwana dashi cikin ranka koka qullata,ubangiji na sonshi fiye dakai,ya fika matsayi a wajen ubangijinka,kaga qullatarshi ko gaba/ko kwana dashi a rai daidai yake da SHIRYA YIN YAQI DA UBANGIJI NE_*
*_Allah ya haskaka mana zukatanmu_*π€²π½π€²π½π€²π½
******Rana ce sosai akeyi a ranar ta lahadi,wadda tun safiya dama ta qwalle sosai da zafinta,kusan indai ba lalura ba da wadanda ta kama dole,kowa ya samu mafaka yana shan iska,tare da jiran ranar ta danyi sanyi kafin ya wuce yaci gaba da aikinsa.
Ita daya ce qwal a tsakar gidan nasu,tsit gidan yake,babu motsin kowa,sai waqe waqen baba laure dake tashi tsakanin babban tsakar gidan nasu zuwa sassanta,tana aikace aikacenta,da alama duniya tayi mata dadi.
A duqe kaltum take tana wanki kayan ummansu da nata dana bilal,ranar ce ke dukan gadon bayanta,duk da zafin da ranar keda ita hakan bai wani dadata da qasa ba,qunci ne fal zuciyarta,wadda babu abinda take mata sai zafi da quna,musamman idan ta tuna da irin tijarar da mahaifinta ya tsiyaye musu tas ita da mahaifiyarta a dazun kafin ya fita,a kullum idan yana irin wadan nan halayen mamaki kamata yakeyi,kai bazaka ce shine ya haifesu ba,ba zaka taba dauka mahaifinsu ne da suka fita ta tsatsonsa ba.
Ta gama matse wasu tana shanya ta soma jiyo dan qaramin kuka da nishi,saita dora sauran kayan dake hannunta saman igiyar tana waiwayawa bayanta da sauri,bilal ne ke shigowa yana dingishi,yayi futu futu dashi da qasa sai kace wanda yayi wanka da gari.
Sakin abinda takeyi din tayi,ta nufoshi da sauri tana kallonshi,fuskarsa daga gefe ta kuje,hancinsa kuma da alamun jini daa hade da qasa,dafashi tayi tana kallon fuskarsa cikin tashin hankali
“Kai….lafiya bilal…meye haka?,waye yayi maka haka?”
Cikin haki dake nuna zallar kukan da yasha yake magana
“Su musbahu ne….”sosai ranta ya baci fiye da tunaji,batasan me yasa suke masa haka ba,sun maidashi kamar wani jakinsu,ko yaya yayi musu abu saisu kamashi suyita duka,bayan duka duka ba wani girme masa sukayi ba,kusan sa’anninsa ne
“Me kayi musu?”ta fara da tambayarsa duk da fushin da take ji yana cinta
“Ban musu komai ba wallahi,wai don kawai am bamu kudin aikinmu yace na ranta masa zai siya sabuwar waya,saina hanashi,saboda wancan karanma da suka ranta basu biya ni ba” wani fushi taji ya taso mata,wannan ba shine karon farko da suka fara dukansa ba,kuma a yau din bata jin zata qyalesu,rashin gatan nasu da galihu baikai har haka ba,don haka tace dashi
“Ina zuwa”saita shige daki.
Ko zanin jikinta bata sauya ba,ta zaro hijabinta dake cikin kayan datti ta saqala,ta tabbatar ummansu bacci take,ba zataji fitar ta ko dawowarta ba,hakan kuma yayi mata,don haka ta warci hannun bilal suka fice daga gidan,tana jin kamar tayi tsuntsuwa ta isa wajen.
Sauri take falfalawa kamar zata tashi samq,cikin mintina qalilan suka isa wajen,ko ina ma’aikata ne birjik,sai tarin was ada duwatsu na aikin ginin makarantar,iya kayan aikin da aka zube kawai ya isa kasan cewa aikine za’ayo tuquru babu wasa,sai taja ta tsaya tana wulga idanunta inda zataga su musbahu.
Daga can ta hangosu,sunata daukan kwababben sumunti cikin kwanon sarki zuwa cikin sabon foundation din makarantar da aka fitar aka kuma soma sanya bulo.
Tsaiwa tayi ganin isyaku na dosowa inda suke,shine abokin bilal da tasu tafi zuwa daya,ci gaba tayo da dakonsa har yazo gab dasu
“Isiyaku”ta kirasa ganin bai gansu ba,ya waiwayo sannan ya taho inda suke
“Isyaku…..me ya faru tsakanin bilal dasu musbahu?” Sak yadda bilal din ya gaya masa hala shima isyaku,sannan ya dora da cewa
“Saida nace ya daina bawa kowa bashi amma yaqi ji,ni ya gani aiba wanda nake bawa,shima kuma dukkansu babu wanda yake iya ranta masa naira biyar,amma shi duk wanda yace bilalu aramin kaza,ko ragowar kudinsa duka saiya dauka ya basu,kuma yawansu ba biyansa suke ba,idan sukaci sunci kenan” Duban bilal tayi,kamar ta mangareshi haka takeji,saidai yanayin yadda yaji jiki a hannunsu musbahu yasa ta daga masa qafa,kuma tunda Allah yasa taji zata yiwa tufakr hanci,maida dubanta tayi ga isyaku
“Yanzu dawa dawa yake bin bashi a wajen nan” Dukansu isyaku ya lissafa mata,daga inda take tana iya hangosu da idanu,sai daya gama sannan tace
“Muje wajen nasu” tayi gana cike da qarfin hali da qwarin gwiwa,duk da cewa musbahu ya girmesu bama su ba har ita,amma batajin koda tazarar shekara nawa ya bata zata qyaleshi.
Tun kafin su qarasa musbahun yaga tahowarsu,saiya tsaya da abinda yakeyi ya riqe qugu yana jiran isowarsu.
A gabansa ta tsaya tana kallonsa ido cikin ido
“Kudin bilalu nazo karba”
“Na qarfi ne,idan kina dashi saiki amsar masa”
“Bana qarfi bane,kuma nwzan qwata ba,kuma dole ka bashi”
“Bazan bayar ba,duk wanda zaki kira ya karbar masa ki kira” sosai ranta ya baci,hakan ya tunzurata ta fara magana cikin daga murya,cikin masifa da tada jijiyar wuya tana nuna musbahun tare da jaddada masa ba zata bar wajen ba sai ya bada wannan kudin.
Daga can gefe daya dukka cikin sansanin da ake gabatar da ginin makarantar,qarqashin wata qaramar rumfa da akayi da ciyawar bunu,zaune yake saman wata kujera mahadi da teburin dake gabansa,saman teburin lemo ne da cup sai ruwan roba,gefe daya kuma kwamfutar tafi da gidanka ce ta laptop,duk da haka jarida ce a hannunsa yake dubawa shafi bayan shafi,jikinsa na sanye da jeans da shirt wadanda sukayi qura saboda qasar dake wajen,sai rigar ma’aikatan kamfaninsu mai kama da apron daya dora saman kayan nashi.
Hutun minti talatin ya tafi a yanzu yanzu daga filin da ma’aikata suke,wanda kusan duk wani aiki da ale gabatarwa a kowanne qauye indai yana nan yalan shiga yaga yadda yanayin aikin nasu yake,daga irin nashi experience din ya musu gyara a inda yake ganin yana da buqatar gyaran,ya dauki jaridar kasuwanci ne yana duba yanayin hawa da saukan hannuwan jari dollar da sauransu.
Kadan kadan hayaniya daga can gefansa ta soma shiga kunnuwansa,tana kuma rarraba masa tunani,saiya cira kansa a hankali ya waiwaya gefan nasa.
Tana tsaye tsakiyar ma’aikatan maza,sanye da duqunqunen nan hijabi wanda habarda ta koma gefen kuncinta,tsingilallen zani wanda ya tsaya iya qaurinta,da wasu sudaddun silifas,fuskarta sai shining take cikin hasken rana,sakamakon baqar fatarta da kuma gumin da take saboda zafin rana.
Sosai ya zuba mata idanu yana kallon yadda take wulwulga hannu,gamida motsa bakinta da sauri da sauri,duk da baya iya jin muryarta sosai amma ya tabbatar rashin kunya take,dubda da yadda na bayanta keta mata magana,amma batajin me suke fada ma bare tabar abinda takeyi din.
Ranshi yadam baci,donshi mutum ne da baison rashin kunya ko qanqan,shi yasa yake respecting duk mutumin dake sama dashi a shekaru,koda kuwa qasa yake dashi a muqami,daya daga cikin abinda yasa ya tsani SIYASA kenan,saboda yadda dan qanqanin yaro zai iya tsaiwa gaban sa’an kakanshi bama babansa ba,ya danna masa zagi,rashin mutunci ko cin fuska yadda zuciyarsa ta raya masa,saboda kawai ya fishi wani abun duniya,muqami ko matsayi ko kuma kudi ko fada aji.
Ajjiye jaridar hannunsa yayi,saiya kiqe tsaye yana sanya hannayensa cikin aljihun wandonsa,kana ya taka zuwa bakin rumfar ya tsaya yana ci gaba da kallon abinda ke faruwa.
Tsahon wasu mintuna ya hangi umar na nufo rumfar da yake tsaye din,sai yasa hannu ya fitoshi,ya qaraso wajen cikin girmamawa
“Me yake faruwa a can wajen?” Yayi masa nuni da idanuwansa,saida umar din ya kalla wajen sannan ya dawo da kansa wajen samir din
“Nima dai naxo na tadda abun na faruwa….dana tambaya sai yaron yacemin,kudin aikin da aka basu ne babu canji ba’a bawa yaron nashi ba,shine yaje yacewa yayar tasa an hanashi,shine tazo karbar masa,tanata zaginsa yana qoqarin yi mata bayani amma taqi saurarsa” Tsaki yaja yaa ci gaba da sauraren umar
“To nidai ban mata magana ba,saboda kasan halin wasu yaran qauyen nan ba tarbiyya garesu ba,yanzu ‘yar cikinka saita qunduma maka ashar” komawa yayi da baya ya zauna kujerar daya tashi din,ya zura hannunsa aljihun wandonsa ya fiddo kudi,’yan dari biyar biyar ne sababbi guda shida,ya miqawa umar
“Ka kai mata,tayi qoqari tabar wajen nan yanzun nan,banason hayaniya” karbar kudin umar yayi,har yayi gaba samir dake murza goshinsa yace
“Ka gaya mata,indai taci gaba da zuwa wajen nan,to qaninta zaibar aikin da yakeyi a wajen,saboda ba wajen zuwansu bane”
“Ok sir” umar ya fada yanayin gaba.
“Kinga madam,kiyi haquri,karbi kudin aikinku da Allah” umar ya fada yana shan gabanta,saida ta yima umar din wani irin kallo sannan ta saka hannu ta karbi kudin,ta kallesu sosai ganinsu sababbi a miqe,idanun musbahu qur akan kudin,ji yake a ransa dama shi aka baiwasu,saboda yana ganin yawansu yasan sun wuce adadin da aka basu din na ainihi,daya sani ma ya biyashi kudinsa,da bai samu wannan garabasar ba,ga mamakinsa saita maidawa umar kudin
“Da irin kudin da aka biya kowanne ma’aikaci za’a biyashi haqqinsa,bama huqatar sabon kudi ko wani abu daban” duban mamaki umar yayi mata,ganin kamar tazo da sabuwar tsirfa,amma kuma daya tuna nau’in muhallin da take rayuwa,sai mamakin nasa ya ragu,ya kuma danganta hakan da qila zallar qaunyanci ne ya sanyata aikata hakan,akwai wasu kudaden a aljihunsa,don haka ya laluba ya irgo ‘yan dari biyar biyar guda shida kamar yadda suke a sababbin.
Karba tayi ta irga,saita dubi bilal
“Nawane kudin aikin naku?’
“Dubu biyu ne” ya bata amsa,ta sake waiwayawa ga kudin,ta irga dunu biyun,ta linke dubu daya ta miqawa umar
“Mun dauka iya kudinsa,ga canjinku”
“Ku riqe gaba daya”kaita kada
“Bamaso,haka aka biya sauran abokan aikinsa,shima haka za’a biyashi” sosai umar ya cika da mamakinta,ya tsammaci tun a karon farko zata karbi kudin cikin murna da farinciki,ba tare data tsaya neman musaya da tsaffin kudi ba,bare ta tsaya ta irga iya haqqinsu.
Kafin ya ankara tuni ta juya taja hannun bilal sun fara barin wajen
“Oga yace a gaya muku….idan kika ci gaba da zuwa nan wajen,to qaninkin xai rasa aikinsa” cak ta tsaya sannan ta waiwayo,sai data watsa masa wani kallo sannan tace
“Ko da baka fada bama bilal bazai sake aiki a nan wajen ba,tunda babu amfani yin aiki qarqashin mutanen da basa da adalci” daga haka taci gaba da jan hannun bilal suka bar wajen,yayin da tabar umar yana binta da kallo,cike taf da mamakin daya cika masa zuciya.
“Ka gani ko mai gida,dama bata da kunya,duka ‘yan gidansu ma,ana xargin qanin nata ma barawo ne” musbahu ya fadi haka,cike da fatan bilal din ya sake nisa gaba daya da wajen aikin,ta yadda shi zai samu ya dinga aikin mutum biyu yana karbar kudin,kallonsa kawai umar yayi,saboda ya shiga shakku ga zaton da suke mata,saiya jiya ba tare da yace komai ba ya koma wajen da saraki ke zaune.
Dakatar da umar din yayi yayi kafin ya gama bashi labarin abinda ya faru,yace yaje kawa yaci gaba da duba abinda za’a qara saman kayan aikin dake wajen.
Suna isa gida ta tattara sauran kararen dake ajjiye kusa da bayan gidansu ta kunna wuta ta dora ruwan zafi,tas ta gasawa bilal jikinsa,tana yi tana baqin rai ita kadai tana mita harta gama sannan ta dubeshi
“Idan na sake ganinka wajen daga yau nida kaine wallahi,tunda kai bakasan dadin jikinka ba bare ciwon kanka,kuma zan koma,duk wanda kake vi bashi a cikinsu saisun hada maka kudinka” hada masa sauran ruwan ya shiga bayan gida yin wanka,daidai sanda umma ta fito daga dakinta,tashinta kenan a bacci,tana dabarun yadda zata miqe saboda yanayin qafarta ta jiyo mitar kaltum din
“Wai lafiyarki kuwa….ke kaltum keda waye?,ga wankin ma har yanzu baki gamashi ba,garin yaya?” Tas ta gayawa umman komai,shuru tayi umman ta sanya buta a gabanta zata daura alwala,shurun na umman ya tabbatarwa kaltum akwai inda tayi kuskure kenan,duk da ita bataga wajen da tayi ba dai dai ba
“Yanzun kin kyauta kenan kaltume?,ki tafi cikin maza kina fada kina babatu?,tarbiyyar dana baki kenan?ina kunyar dana sanki da ita?,shine har kike cewa zaki koma?,to idan kece da kanki ki koma din” daga haka umman taja butar da kaltum din ta xuba mata ruwa taha daura alwala.
Sosai jikinta yayi sanyi,sai a sanna ta gane rashin kyautawarta,saidai ranta ne ya riga daya baci a sannan din,takai maqura kan abinda akewa bilal din,tunda ba yaune na farko ba da hakan take faruwa ba.
A sanyaye taci gaba da aikinta,da zummar idan umman tasu ta huce zata je ta lallabata ta bata haquri.
Bayan sallar isha’i sanda tasan umman nata na zama su danyi hira,tayi amfani da wannan damar ta bata haquri,kamar kowanne lokaci umman na yawan mata uzuri,wannan karonma uzurin tayi mata,tayi mata nasiha
“Kiyi koyi da haquri kaltum,babu abinda yafi haquri riba,duk wanda kikaga yayi haquri baici ribarsa ba,to ba shakka ba ainihin haqurin yayi ba” kai ta jinjinawa umman tasu,saidai cikin ranta tana juya kalmar umman ta haquri,wa shin wanne haqurin umman takeso tayi baya ga wanda sukeyi a yanxu?,ko so take a daga hannu a dagesu,a zagesu,a dalla musu mari su tsugunna su baiwa mutum haquri harda tukuici ma?,to idan ba irin wannan haqurin ba batasan wanne umman takeso suyi ba.
Suna nan zaune umman tana basu labarqi na rayuwa da zai amfanesu,ya kuma zame musu izina saiga sallamar suwaiba,sosai kaltum tayi mamakin hakan,saboda ta manta rabon da suwaiban tazo gidansu,harda bikin habiba,wanda har akaci aka cinye babu ita babu dalilinta,duk kuwa da takawar da tayi taje gidansu,ta kuma sake roqarta tazo din,tun daga wannan lokacin itama kaltum din taji haushin hakan,ta kuma janye jikinta daga suwaiban,dama ita ba gwanar tara qawaye bace,gaisuwa dai ta mutunci tana yi da sauran sa’anninta,an kuma san junq,amma ba qawance irin nata da suwaiba ba.
Wannan dalilin bai sanya kaltum sakar mata fuska ba,ta kuma bata wajen zama.
Daga gefan tabarmar ta zauna kamar wadda take a darare,ta gaida umman,sai umma ta tashi ta basu waje,sai bayan barin umman sannan suwaiba ta kalli kaltum
“Kwana da yawa” murmushi kadan kaltum din tayi
“Ke za’a cewa haka,harna zaci ma ko batan kai kikayi,ba gidan nan kikayi niyyar shigowa ba” murmusawa ta danyi kadan sannan ta tabe baki
“Nikam ai ana ganina,kece dai,daga ke jar nasuru kunyi batan dabo”
“To me zan fita nayi a waje suwaiba” kaita jinjina
“Nasiru fa?”sai data kalli suwaiban sannan tace
“Baya nan,yana cikin gari,yacemin jarrabawa sukeyi a makaranta,sai kuma sun gama zai dawo” yanayin fuskar suwaiban ne ya canza,sai tace
“Allah sarki,Allah ya bada sa’a…..”tayi furucin tana miqewa tsaye
“Bari na wuce”
“Da wuri haka?”kaltum ta fada tana dubanta,baki ta sake tabewa
“Eh….dandali zani,kuma nasan ke ba zuwa zakiyi ba”
“Gaskiya kam”ta amsa a gajarce,cikin nuna halin ko in kula tace
“Su lantana ma sun bani saqo,sunce suna jiran sabuwar waqar dandali da kika musu alqawari….naga sai wani kulawa take da lamarin,ban sani ba ko sabom qawance kuka qulla ba” Murmushi kaltum tayi,lantana tana da kirki,hakanan duk wani abu daya shafeta tana shiga ciki,saidai ita qawance bata daukeshi wani abu ba,ummanta a yanzu itace babbar qawarta
“Koda yake idama hakanne ba laifi,sai anjima” Cewar suwaiba tanayin gaba,sai kaltum din ta bita da kallo kawai,kullum mamaki ke qara kamata kan silar canzawar halaye da dabi’un suwaiban,wanda batasan daga inda ya samo tushe ko kuma asali ba.
Tana tsaka da wannan tunanin ummansu ta fito daga daki
“Harta tafi kenan suwaiban” tana gyara zama ta bata amsa
“Eh umma,tace wai dandali zata” kan kujera ‘yar tsuguno ta zauna tana miqe qafarta yadda zatafi jin dadin zaman
“Bansan me yasa sam yanzu bakison fita kiga mata ‘yan uwanki ba,ba hanaki fita nayi ba kaltume,kawai dare ne banaso kinayi sosai a can” dan murmusawa tayi
“Inason zuwa ummanmu,zan leqa wani lokaci”.
Umman bata sake bi takan wancan zancan ba ta sako mata wani
“Kinga daxu fatsima tazo,lokacin bacci ya daukeki bata tasheki ba,inna bata jin dadi,ni kuma ga yanayin qafata data matsamin,gobe idan kin gama abinda kikeyi ki shirya kije ki dubomin ita”
“Toh” ta amsa qasa qasa alamun batason zuwa dai,sai umman ta share bata bi takan sauyawar yanayinta ba.