Sponsored Links
KyalKyalin Kauna Hausa Novel

KyalKyalin Kauna 53

Sponsored Links

EPISODE

 

Wani kalan rawa jikin Hajiya keyi wlh kaganta zaka iya dauka da gasken gaske ta samu cutan farfadiya ne, ga iPad din dake hannunta data kunna da bama takanshi takeba tunda taji muryan Yasmeen, jikinta ko’ina na bari bar bar bar tana kallon wayan dayake kasa ya tsatsage, wani mugun kallo Maheer yamata kafin ya fito yazo har gabanta tsungunawa yayi kasa hannunshi yadauki wayan yakalli screen din sabon number shi yaga ta kira wayan dake hannun Yasmeen ga Yasmeen akan layin, ko dar Maheer baiji ba dan shi idan akwai abinda baidashi a duniyan nan shine tsoro yakai wayan kunnenshi daidai Yasmeen nakara cewa “Hello” ahankali, har cikin tsakiyan kirjinshi yaji muryanta baisan lokacin daya lumshe idanunsa ba, cikeda so da kulawa da kuma tattausan murya ta yanda kana gani kasan da abu mai mahimmanci yake magana yace “I’ll call you back” yazare wayan daga kunnenshi tareda katsewa sannan ya mike tsaye yajuyo yakalli Hajiya dake wani irin kallanshi jikinta na rawa, hannunshi yakai yakarbe iPad dinshi dake hannunta sannan ya juya yawuce closet abinshi Hajiya na binshi da idanu, duka hannayenta Hajiya tasa ta mammari kanta kafin ta wuce bayinshi da gudu tabude pampoo ta tara ruwa tana watsawa a fuskanta tana wani irin sauke ajiyan zuciya kaman wadda take shirin suma. Takai kusan 2mins tana haka sannan tajita tadawo daidai tafito daga bayin tai closet dinshi dagudu , bude kofan tayi tashiga daidai ya gama saka wando yana saka singlet kallo daya yamata yadauke kai yacigaba da abinda yake, cikeda tashin hankali Hajiya tace ” wacece wacce tadauki number nan Dana kira Pablo?” Shiru ya mata baice kalaba yadauki T-shirt dinshi fari yana sakawa, wani irin bakin kishi ne ya turnuketa tace “Pablo who is dat gurl daka kira around 5 na asuba yanzun nan kuma Kane cemata u will call her back, wacece?” Juyawa yayi yadauki turarukanshi yana fesawa one by one kaman bazaiyi magana ba sai kuma yajuya yadan kalleta kafin ya dauke kai yace “you don’t have to know wacece and this should be the last time da zaki kara taba min waya” karasa shigewa cikin closet din tayi tazo inda Maheer yake tsaye idanunta sunyi jazur tace “Pablo dawa kake magana haka? Koni baka 10min kana waya dani, wacece it’s?” Shiru yamata daidai yagama fesa turare juyawa yayi zuwa wajen takalman shi yaciro wani flat shoe yazuba akasa yasa zai wuce dasauri Hajiya tasha gabanshi yanda take jin kaman zata zare yasa ta wani kalan fashe da kuka gwanin ban tausayi tace “Pablo budurwa kayi eh? I thought nine komi baka, nine rayuwanka, Pablo kasan yanda na tsani naga any mace atare dakai that’s the reason har yau har gobe bamu taba daukan ma’aikata mata ba, ban isheka ba Pablo mezakayi da wata, babu wacce zata taba sonka kaman ni, Pablo dan ALLAH ka rufa min asiri my heart cannot take it naga kana magana da wata dan ALLAH, kaji tausayina wlh Maheer zan iya mutuwa idan kafara son wata sama dani aduniya kaji my baby” dan yatsina fuska Maheer yayi kaman wani abu ya shigeshi instead of yaji tausayin Hajiya yanda yakeji da idan tana kuka jiyayi he’s feeling irritated yatsina fuska yayi strictly yace “tashi agabana zan fits” yanda gaban Hajiya ke fadi zaka dauka zuciyanta is about to fail ne ganin yanda ko tausayinta ma Maheer baijiba kaman yanda yakeyi idan tana kuka ada, girgizamai kai tayi tace “kozan matsa saika fadamin wacece kake waya da ita” “is none of your business maryam! Allow me to live my life!” Maheer yayi maganan ranshi a bace, cikin bala’in zafin zuciya yace “tashi agabana” adan tsorace ta matsa daga gabanshi tana wani irin nishi wucewa yayi ya fice abinshi yay hangar kofa daidai yasa hannu zai bude kofan dakinshi yafita yaji karan faduwan abu dimmmm! Chak ya tsaya kafin ya juyo da sauri yakalli kofan dakin closet din Wanda half dinshi yakenan abude kafafun Hajiya ya hango kwance a kasa suna shaking sosai, dawani kalan sauri Maheer yay closet din yabude kofa ya shiga Hajiya ya gani kwance akasa idanunta sun kakkafe tana struggling tayi numfashi dawani kalan sauri yay wajenta tsugunawa yayi yadagota da sauri yama rasa mezaiyi ahankali ya jijjigata yace “maryam maryam” tashi yayi da sauri yawuce yafita daga dakin ruwa yadebo yazo ya kwara mata still taki dawowa she’s having heart attack idan baiyi rushing nata to hospital ba zata iya mutuwa, tashi yayi dasauri ya dauketa yasauka da ita kasa wajen motanta yaje sai lokacin yama tuna key, ajiyeta yayi kan kujera yawuce ya koma cikin gida zuwa dakinta key motanta yadauka yasauko yadauketa yasa ciki yakoma gaba yaja motan da mugun gudu, yana kaita asibitin su aka wuce da ita emergency tsayawa yayi tareda dafa kanshi kawai yayi shiru he don’t even know what to do again.

Sosai Yasmeen tayi baki yan anguwansu, some kawayen ya sa’a ne, dasu matan malam Sani da kawayenta dasauransu, sai wajajen 5:30 na yamma sannan last set of people suka tafi kaman karsu tafi koba komi sunsa tarage kewa sosai wayan hannunta takalla wlh bala’in so take Maheer yakirata back din dayace amman har yanzu shiru jin duniyan tamata zafi yasa tashiga saka number Ammi awayan tai dialing number kira daya biyu Ammi ta dauka dasauri Yasmeen tace “Ammi nine” wani irin murmushi Ammi tayi tace “iyye Yasmeen ya kike? Ina mijinki?” Ahankali Yasmeen tace “yafita Ammi inata baki yau yanzunnan wasu ma suka tafi” Ammi tace “ai haka amare keda farin jinin baki kidinga samu dai kina bacci kinji” ahankali tace “to Ammi ke yaushe zaki zo?” Dariya sosai Ammi tayi tace “gobe” dasauri Yasmeen tace “dagaske Ammi” “ke dadina dake shegen shiririta da shirme nacemiki zan zo gobe saiki yards nida nazo gidanki sai kin haihu” murmushi tayi kunya maganan ya bata hakan yasa tace “Ammi ina Nanah, da Farida, da yayah, da Hajjo, ina Baba?” Murmushi Ammi tayi tace “Babanki na wajen aiki kowa kuma na nan lpy, sannan Nanah da Farida dasauran yaran kema kin San babanki ya kadasu makaranta ba bata lokaci” murmushi tayi batace komai ba Ammi tace “kin cigaba da shan magungunan nan ko” ahankali tace “eh dazun ma nasha” Ammi tace “good suna da kyau zasu kama jikinki har sai bayan kin haihu kirike abinda na fada miki Yasmeen kinji, kin daiga yanda iya kirsa da hikima yasa duk taurin kan babanki nakan juyashi kuma haryau muna zaune, in har na iya nakama babanki haka kema zaki iya better than me kisa mijinki atafin hannunki kinji” ahankali Yasmeen tace “to Ammi” Ammi tace “dazu sa’a ta kirani tace number ki baya shiga” “Ammi banga wayata ko sama ko kasa ba ni bansan ko agida na barshi ba amman dai banzo da ita nan ba wannan ma tashi ce yabani narike dazu da zai fita” baki Ammi ta tabe tace “ai ko an riga an sace wayar kenan tunda take akashe Bari zan kara duba ko’ina gobe kije ki gaida Baban mijinki kinga makaho ne ki gyaramai inda yake zaune, ki kyautatamai ki dinga abincinki dasu, ki daukeshi kaman yanda kika dauki Baba kina jina, bana son koda wasa naji an kawo karanki, Yasmeen na cire kunya babu abinda ban koya miki ba dan haka ki rike abinda nafada miki keba yarinya bace koda ada baki San komiba Nina koyar dake dakaina dan haka kirike amanar mijinki kinji” gyadama Ammi kai tayi tace “to Ammi” murmushi Ammi ta yi tace “jeki karashan maganin kiyi wankan dare kafin mijinki ya dawo sai da safe” ahankali tace “toh” hawaye ya zubo mata daga ido tacire wayan daga kunnenta she really miss gidansu da Amminta sosai, tashi tayi tasake leka kitchen takarasa jera kayayyakin cefanan da Dan yakawo Wanda tana cikin jerawa baki sukazo, raguna biyu da aka yanka aka sa a freezer da kaji da spices babu Wanda bai sayo ba dasu irin kayayyakin salad, bai siyo shinkafa ba dan ranan yana gidan yaga an kakkawo mata dasu jarkunan mai but duk wani abu da vegetables yasayo bayan ta gama ta wuce sama.
Wuraren 7:00 na safe Yasmeen tasauko kasa idanunta sun kumbura sosai sabida kukan datasha da rashin bacci ita kenan kawai ya aureta ne yazo ya ijiye a gidan nan lallai ma wlh it’s time she will face mutumin nan in har ya tursasata ta aureshi sabida kar ya kashemata iyaye itama zata tursasashi ya gyara halinshi wlh kuwa in har Amminta ta iya tasa Baba dayafi kowa taurin kai a duniya da masifa shiga taitayinshi itama zata iya saita Pablo dudda bata da shekaru a inda yake , bayan hannunta tasa ta goge hawayenta Tass sannan ta tsaya gaban kitchen din addu’a tayi kaman yanda Ammi takoya mata sannan tashiga dan fara girki for the first time Saninn Baba tsoho ne shine zatama girki yasa tamai abincin datasan tsofaffi naso tuwon shinkafa miyan taushe dayaji kan rago gidan gabadaya yadauki kamshin abincin Yasmeen, tahada zobo dayawa tadauko wani babban jug tazuba tasaka kankara sannan tai wrapping tuwon a Leda ta dauko lafiyayyun kuloli masu bala’in kyau ta fito da komi parlor ta ijiye sannan ta wuce sama fuskanta ta wanke tacire riganta tadauko wani sabon atampa tasaka da babban mayafi sannan ta tasauko parlor kaganta sak amarya, kulan daya data zuba ma maigadin gidan ta dauka fitowa tayi tafara tafiya har zuwa wajen gate mai gadin na ganinta dasauri yace “sannu Hajiya” bashi kulan tayi zokaga addu’a murmushi tayi tace “dan ALLAH zoka tayani daukan abu” gyadamata kai yayi yace “bari na ajiye adaki Nazi” wucewa tayi shima yana ijiyewa yafito yabiyo bayanta kulolin tabashi yarike mata itakuma tadauki jug na zobon suka fito har zuwa bangaren Baba sallama tayi tare da knocking bude kofan Hamad yayi ganin Yasmeen yasa akunyace yace “sis in-law, let me help you” yasa hannu ya karbi jug na hannunta yace “Ku shigo” shigowa tayi ahankali mai gadi biye da ita har inda Baba yake zaune kan kujera yana murmushi yana kallon kofan kaman yana gani har gabanshi tazo ahankali tace “Baba ina kwana” hannu Baba yashiga mikawa hakan yasa Yasmeen ta matso kusadashi dasauri yasauko hannunshi akanta cike da so yace “fateemah na” murmushi Yasmeen tayi ahankali tace ” Babana kaga yau da sassafe natashi nadaura abinci nace Baba yau girki na zaici bana kowaba” dasauri Hamad yazo kusa da Baba yazauna yana Nuna kanshi yace “ohh Baba kadai kika Sani ko nifa” sandarshi Baba yadauka zai rafka mai yace “tashi anan diyarka ce dazata maka” tashi Hamad yayi dagudu hakan yasa Yasmeen ta kyalkyale da dariya kaman ba ita tagama kuka ba ta tashi da sauri tace “bari na dauko plate na zuba maka Baba” tayi maganan tana yin hanyar dinning tafito da plate guda biyu dawani roba na bowl din ruwan wanke hannunta, sama Baba tuwon tayi tasa miya tamai arranging a tray ta mike tajawo kujera ta daura mai akai, ahankali takama hannun Baba cikeda so dan hakanan taji tanason mutumin tace “Baba wanke hannu” tai maganan tana wanke hannunshi sosai Baba ke murmushi dashi kanshi Hamad dake kallonsu ba karamin burgeshi Yasmeen tayi ba, Ciro hannun Baba tayi tace “yauwa Baba ci kaji ka koshi baraka kara cin abinsu ya Hamad ba” dariya Baba yayi a hankali yace “ALLAH ya miki albarka Fateemah” wlh har cikin zuciyanta taji sanyi sabida addu’an daya mata, juyawa tayi ta kalli Hamad dan hararanta yayi kadan shi adole yayi fushi murmushi tayi tazuba mai zobo ta wuce har gabanshi taja kujera tadaura ahankali tace “kaima kayi breakfast ya Hamad” murmushi yayi yama kasa magana sabida yanda abincin ke kamshi yasa hannu dasauri yafara ci ya ALLAH! Hamad jiyayi kanshi zai sauka shima yazauna akan kujera sabida dadi, komawa wajen Baba Yasmeen tayi tana kallon yanda yakecin abincin yama kusa cinyewa tace ” Baba nakara maka?” Murmushi yayi yace “eh amman rabi zaki samin, Fateema na Dade banci abincin daya tunamin mahaifiyata ba kaman yau, kin dafa naman yayi luguf daidai yanda tsoho Irina daba hakora zai iyaci” murmushi Yasmeen ta yi karamai yaci Hamad har wajen yazo yace “nima akaramin” sake samai tayi tana murmushi yanda taga sunyi appreciating abincin Tass suka cinye babu Wanda ta bari yayi wani abun kwashe plates din tayi dudda Hamad yaso yahanata taki takai kitchen ta wanketa bama kitchen din lafiyayyen gyara kusan 1hr tayi cikin shi ko’ina yahau kyalli sannan ta fito, wajen Baba taje fuskanta ya shafa yace “ALLAH miki Albarka Yasmeen” ahankali tace “Aameen Baba” anatse Baba yace ” jeki huta kinji kada ki kara wani aiki kuma yau dan ALLAH”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button