Sponsored Links
Dangina Book 2Hausa Novels

Dangina Book 2 Page 11

Sponsored Links

๐Ÿ”ฑโšœ๏ธ๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆ *DANGINA*๐Ÿ‘จโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘งโ€๐Ÿ‘ฆโšœ๏ธ๐Ÿ”ฑ
*BOOK 2*

*PAGE 11*

Tun safe Sarki ya k’ira d’aya daga cikin yaran shi dake can Lagos d’in ya bashi umarni akan su gyara mishi gidan kafin ya iso,
Domin dai dama koda ma ace matar gidan tana gidan idan yayi tafiyan daya dad’e baije Lagos din ba to kafin ya dawo su yake turawa su kintsa mishi gidan dan ita dai Teemah haka Allah yayi ta da rashin iya gyaran waje baya tunanin kuma zata iya canzawa,
ita dai barta a tsaftar jikin ta tsaftar muhalli ne dai bata da katabus, dan zata iya wanka sau goma a rana amma ba tareda damu da sharan d’aki ko sau d’aya a rana ba,

dan dama tun bayan barin shi Lagos da aka maida shi KD aiki ya zamana ta samu freedom dan haka tuni ta d’auki yar aikin dake mata komai daya shafi aikin gida sai in Sarki yazo garine shine mai aikin ke dena zuwa idan ya koma kuma saita dawo da ita, duk da yanda zuciyar shi ke azalzalan shi akan ya kirata domin ya shaida mata zuwan nashi k’iyawa yayi, dan tun bayan barin ta zaria dama yayi alwashin cewa bazai kirata ba har sai in itace ta kirashi da kanta tunda har ta iya tsallakewa tabar garin bada izinin shiba, yasan fushin rashin gaskiyar data sabayi a duk sanda suka samu sab’ani koda ko ace shine mai gaskiya ba itaba shi takeyi a yanzun d’in ma,
jira take ya kirata ya kaskantar dakai yana bata hak’uri kamar yanda ta saba ita kuma sai taji dad’in kafa mishi tarin sharud’an da baya iya tsallakewa a wancan lokacin yanzun kam ko kusa bayajin zai iya zubar da kanshi akan abunda yasan cewa koda ya aikata aiba haramun ya aikata ba, tunda ita yarinyar da take tunanin ya kwanta da ita d’in ai matar shice ta aure wanda ya biya sadaki kamar yanda ya biya nata sadakin itama,

Ana cewa mata na kishi amma gaskiya wani kishin yana zarce ka’ida dan kishin teemah akan shi in batayi wasa ba sai ta d’aura ma kanta lalurar da babu mai mata maganin shi,
Duk da yasan cewa a ayyukan da take aikatawa shima yana da nashi kason laifin domin shine tun farko ya sake mata, ta yanda ta samu damar aikata duk abunda take so batare daya takura taba,
Ya sani cewa yana son matar shi sosai domin shi din irin mutanen nan ne da basa iya cusa ma kansu son abunda baiyi dai dai da ra’ayin suba, Teemar shi itace mace ta farko daya fara so,
Yaso ta da dukkan zuciyar shi sai dai baiyi zaton cewa zatayi amfani da soyayyan da yake mata wajen juya akalar rayuwar shiba,bai sani ba ko soyayyar da yake nuna mata ne yayi yawan da take ganin kamar bazai tab’a iya rayuwa da ko wacce mace ba sai ita, ta manta cewar shi d’in namiji ne musulmi kuma wanda Allah ya halatta ma yin mace sama da biyu ma tunda yana da halin da zai auro su,
duk da cewa yana da tabbacin cewa ita ma d’in tana matuk’ar kaunar shi, koba komai ai duk inda kaga kishi tofa yana tafe ne a cike da soyayya, matsalarta d’aya da bata iya sarrafa kishinta a duk sanda ya motsa mata sai kuma daraja da matsayin da miji yake dashi a wajen matar shi wanda ita bata duba wannan darajar in ta tashi magana dashi kai tsaye takeyi babu wani girmamawa ko ladabi,

bata san inta aikata ba dai daiba ta duk’ar da kai ta nemi afuwa, ah ah a kullum ita gani take cewa ita dai itace akan dai dai.
Zaije Lagos da kuduri ne guda biyu,
na farko dan ya samu dai daito tsakanin shi da matar shi, dan a yanzun bayajin zai iya d’aukar wani sabon kalubalen da zata iya kawo mishi, dan haka zaiyi bakin kokarin shi wajen saita ta ta dawo kamar ko wacce macen kwaran da miji zaiyi alfahari da ita,
Miye matsalar ta?
Kud’i sune abunda tafi bawa mahimmanci fiye da auren ta, shima kuma Allah ya wadata shi yana da kud’in dan haka zai sakar mata su inhar zata dawo mishi kalar matar da yake fata, maganar aikin ta a can kuma duk yanda take son shi dole zata hak’ura ne ta dawo KD taci gaba da aikin zai nemar mata transfer in kuma tace a’ah tofa zai bata zab’ine yasan a yanda take son shi bazata yarda ta zab’i aikin ta akan shi ba, idan sun dawo nan Kaduna kuma zasuje suba uwar gida hak’uri ta dawo musu da yaran su a hannun su dan yana buk’atar had’e kan ahalin shi waje d’aya yana son yaran shi su taso da so da kaunar junar da yataso a cikin shi tsakanin shi da nashi k’annen,

Sai kudurin shi na biyu, dan zuwa yaga Moon yarinyar da tunda yayi tozali da hotunan ta suka kafe mishi a kahon zuciya,
Joseph ya Kira shi akan ya kammala duk wani binciken daya sashi yayi a kanta, yanzun sauran aikin nashi ne, shi dai a gefen shi ta mishi % percent bai san koshi d’in zai samu karb’uwa a wajen taba, sai dai kuma zaiyi iya bakin kokarin shi wajen shawo kanta harta amince dashi ba tareda ya nemi taimako daga wajen Meenal ba shi kadai zaiyi ma kanshi yak’i saboda ba iya farin cikin shi yason ya inganta ba harda na Mahaifiyar shi yasan cewa zataji dad’i kwarai inta samu labarin yana neman aure balle kuma idan taji cewa yarinyar tana da alaqa da Meenal,

ร—ร—ร—ร—ร—ร—

Alhamdulillah ya samu isa garin na Lagos lafiya, Joseph daya Kira tun kafin ya taso ya shaida mishi lokacin isowar shi,
Shi d’in ne ya d’auko shi daga Airport sai da suka tsaya a wani restaurant sukayi takeaway kafin suka k’arasa gidan shi,
Envelope d’in da yake kunshe da bayanan binciken da Joseph yayi mishi akan Moon ya gabatar mishi sama sama ya mishi bayani akan ta domin suna cikin tattaunawar ne shi Joseph din ya samu Kira na gaggawa akan an wuce da matar shi asibiti zata haihu, wannan kiran shiya katse komai duk da Joseph d’in yaso Sarki ya zauna dan ya huta shi yaje asibitin amma Sarki ya nuna mishi cewa babu komai su tafi taren kawai,
Dan haka suka rankaya zuwa asibitin, motar Joseph a gaba motar Sarki da d’aya daga cikin sojojin dake gadin gidan yake ja kuma suna binshi a baya a haka har suka isa asibitin, koda suka je sun samu an shiga da Matar Joseph din d’akin haihuwa sai iyayen matar dana Joseph din ne a wajen suna zaman jiran tsammani,
Basu yi tsayuwa na mintuna 20 a wajen ba ya farajin muryar d’an shi Abubakar da suke Kira da Boy yana kwala kiran sunan shi,

“Daddy! Daddy!! Daddy oyoyo ga dady”
Yaron yake fad’a da harshen turanci a yayin da ya k’araso da gudu cike da murna ya rungume uban nashi,
Wanda shima Sarki mamaki yake akan su kuma me sukazo yi a asibitin da daren nan, duk da mamakin da yake ciki hakan bai sa ya kasa nuna farin cikin shi na ganin sanyin idaniyar shi a dai dai wannan lokacin ba koba komai shima yayi kewar yaron nashi, dan haka sai yasa hannu ya d’ago shi yana jefa shi sama yana cafewa,

“Oh my Boy kaida waye kuka fito da daren nan daya kamata ace kana kan gado kaima kana bacci?”
Sarki ya tambaya, sai dai mai makon Boy ya bashi amsa sai shima ya jefo mishi tambaya kamar haka,

“Daddy kaima kazo duba Baby da Smole Mom tace Momy zata haifa ne koh”
Ya tambaya yana shafa fuskar baban cike da farin cikin ganin baban nashi da yayi a lokacin,

“Sabon Baby na Momyn ka kuma? Ita kuma Momyn naka tana ina?”

Ba tareda yaron ya damu ba ya amsa mishi da cewa,
“Ai tana ciki kuma kullum ma anan take kwana ko nace ta tashi mu koma gida bata zuwa”

Sosai kan sarki ya d’aure dan bai fahimci surutan da Boy ke mishi ba inya fahimta dai dai fa yaron yana nufin Teemah tana nan asibitin kuma wai anan take kwana bata komawa gida, ga sabon Baby da yaji Boy d’in ya ambata, to kenan Teemah nada ciki kenan?

“Kai da waye kukazo nan?”

“Smole Momy” ya amsa yana nuna mishi inda Aziza ke can gefe tana amsa waya da alama bata san cewa Boy ya sulale a wajen ba, shi kuma sarki dama tunda yaji yaron ya ambaci smole Momy yasan ita yake nufi dan duka yaran haka suke kiranta,
Excusing kanshi yayi daga nan inda su Joseph suke ya kama hannun yaron suka k’arasa inda Aziza take,
Da gudu Boy ya k’arasa wajen yana fad’a mata cewa ga dadin shi yazo ganin Momy da baby,
Gaisuwa sukayi tsakanin ta da Sarki cike da girmamawa tana mishi barka da zuwa, bai iyace mata komai ba harta mishi jagora zuwa d’akin da Teemah take, wanda isar su yayi dai dai da fitowar Brigadier general Abubakar da matar shi Aunty Rahma daga d’akin na Teemah,
Dan haka babu b’ata lokaci Sarki ya zube zuwa k’asa domin nuna girmamawa ga sirikan nashi da suka rik’eshi tamkar d’ansu,

Anty ce kawai ta amsa gaisuwar nashi tana tambayar shi yanzun ya iso?
Shiko General k’arasawa yayi ya kamo hannun shi ya mik’ar dashi tsaye,

“Baban Junior bana hakana duk’amin irin haka ba,”

“Ayi hak’uri zan cigaba da kiyayewa mun same ku lafiya? Ya mai jikin ta k’araji?”

“Alhamdulillah mai jiki tana samun kulawa dan d’azun danayi magana da Dr yace min zuwa gaba kad’an zasu bamu ita mu koma gida har sai in lokacin haihuwar yazo gab sai mu dawo, ai jiki alhamdulillah taji sauk’i sosai fa, ya hanya da wajen aikin ka kuma?”

“Lafiya lau, ita kuma Allah ya bata lafiya,”

“Ameen” Brig ya amsa dashi kafin ya d’aura da cewa,

“Gashi kana zuwa mu kuma muna shirin tafiya, ko zamu jiraka idan ka dubata sai mu wuce gida gaba d’aya kaga sai ka samu kaci abunci dan nasan kila bakaci komai ba kayo nan, kasan sunan basa barin yan jinya na kwana”

“Ai babu damuwa kuyi gaba kawai Sir na riga naci abinci kafin in fito kuma bani kad’ai bane tare muke da Friend dina shima matar shi na d’akin haihuwa,”

“Oh Allah sarki to allah ya raba lafiya mu bari muyi gaba to sai da safe”

Juyawa yayi sai da ya raka su har mota kafin su wuce kuma sai da suka duba matar Joseph sai dai har lokacin bata sauka ba tana dai ta fama,
Duk yanda suka so Boy yabi su ko kuma yabi Aziza da mijinta Imran yazo d’aukarta k’iyawa yayi akan shi wajen Daddy zai tsaya dole haka suka hakura suka wuce shi kuma ya koma ciki rungume da Boy din dake ta bashi labarai,
Da sallama d’auke a bakin shi ya bud’e kofar d’akin ya shiga,

Kwance saman gadon da aka tanadar dan marasa lafiya take kwance tundaga kafafuwanta zuwa saman cikin ta rufe da farin lallausan bargo ita kuma kuma tana kwance ne amma fuskanta na kallon kofar shigowa,
Domin tun isowar shi wajen taji muryar shi, bata da k’arfin da zata yunk’ura ta fito wajen dan ta tabbatar ko shi d’inne shi yasa kawai taci gaba da kwanciya tana kallon kofar shigowar,
Bayan ta dena jin motsin su a wajen kuma sosai tsoro ya kamata Allah yasa dai ba juyawa yayi suka tafi tareda su Aunty ba, kenan har abunda ta aikata yakai matakin da Sarki zai shigo cikin asibitin amma ya kasa shigowa ya dubata shine ya juya ya koma?
Kenan bai damu da halin da take ciki ba komai yake shirin faruwa da ita?
Tunda ta dawo fa ko sau d’aya batayi sakacin da wayarta ta rasa caji ko kuma wayar tayi nisa da ita ba duk dai a tsammanin ta na ganin kiran shi, amma kullum haka Gari zai waye rana ta k’ara fad’uwa babu amo ba labari,
A sanda batun Sakin Meenal ya risketa a gadon asibitin nan duk da tana kwance ne cikin ciwo amma ta samu sauk’in nauyin da zuciyar ta ke mata na yawan tunanin da take cewa mijinta nacan tare da wata suna cin soyayya ita kuma gata nan a gadon asibiti ciwo ya hanata sakat,
Tayi zaton tunda akayi sakin zai tattaro ya dawo wajen tane sai kuma taji shiru, shine kuma yau d’in daya iso ya kasa shigowa dubata ya juya,

Tana cikin wannan bak’in cikin ne ta k’ara jiyo muryoyin su shida Boy sai kuma gasu sun shigo d’in, ashe dai har yanzun mijinta na sonta,
Hakan kuma yana nufin cewa ita dai Fateemah itace kad’ai zata dauwama a matsayin matar mijin ta, lallai idan taji sauk’i ziyara na musamman zata kaima OBA dan tasan wannan aikin nashi ne, ashe bai manta da ita ba duk da dad’ewar da tayi bata ziyarce shiba gashi kuma shi baya rik’e waya balle ta kirashi.

*****
A gefen Meelat ko tun washe garin ranar da ta amshi key din gidan Sarki a wajen Hajiya suka isa gidan ita da Maryam kamar yanda suka tsara,
Zama sukayi suka ware suturun na Meenal tsaf suka musu screening suka ware mata wad’anda sukafi buk’atar tayi amfani dasu,
sauran kuma suka kimtsa mata su a gefe, duk wani abunda suka san zata buk’ata saida suka d’aukar mata tundaga kan gyale, takalma da jakun kuna, dan sai da suka mak’are manyan akwatuna biyu da kaya, da suka kuma kawo mata kayan harta da kayan ta na nan gidan Hajiyar suma sai da suka tantance su, basu huta ba haka washe gari suka k’ara shiga kasuwa suka sissiyo abubuwan da suke buk’ata,
Badai su sarara ba sai da suka kaddamar da shirin su akanta na ganin ta canza tsarin shigar ta itama ta fito a yanda suke so, tako fito d’in domin dama tun tuni Meenal ba baya bace wajen iya d’aukar wanka matsalarta d’aya dai ita ba ruwan ta da shafe shafe da dangwale dangwalen su jambaki, dasu bar bad’a kumatu k’ure kwalliyan ta shine ta goga kwali sai mascaran da take amfani da ita dan daidaita tsayuwar gashin idon ta, a tsarin ta ko jagira bata ja dan girarta a tsare take,
To dai itama tunda suka dage akan ganin canjin nata da kuma goyon bayan Hajiya hakan yasa itama ta canza d’in ta koma fiyema da Meenal din da kuka sani a baya wajen iya d’aukar wanka,
Sai gashi hakan ya zama kamar wani makulline na bud’e kofar farin jinin ta, dan kusan kullum ne in sun fita sai sun samu wanda zai taya domin dukan su yanzun basa zama suna ta faman shirin biki ne yawon raba kati da anko,
Kamar yanda kuma Hajiya ta fad’a a cikin satin ita da kanta ta jagoranci zuwa gidan Sarki da masu siyan kaya dan tace bata buk’atar kayan su iso gidan ta kona Malam dan haka duk wani abu mai daraja wanda ya had’a daga kan gadaje kujeru duk ta had’a ta siyar wadanda kuma tasan bazasuyi d’araja ba da wad’anda suka tsufa duk rabasu tayi wa mabuk’ata wasu kayan kuma ta aika dasu gidan Malam, kuma tass tama gidan ko tsinke basu barma Sarki ba dan ita cewa ma tayi ya gode Allah da Allah yasa shine ya zuba kayan Sashen shi da kud’in shi inba haka ba da duka harda na Sashen nashi zata kwashe wallahi,

Duk wannan budurin rabon kayan da kwashe kayan Malam yana da labarin komai ido kawai ya kawo ya zuba batareda yace komai ba dan ya lura magana kawai Hajiya take nema shi kuma bazai biye mata ba,
Ita ko Hajiya kan kud’in kayan ta had’a da kud’in da Sarki yaba Meenal wanda tuni Hajiyar tasa aka canzo mata ta tura su can Saudiya wajen Amina Mahaifiyar Mai Jama’a ta siyo mata dank’ara dank’aran qwalaqwalai ta aiko mata dasu ita kuma ta adana ma Meenal d’in a cewar Hajiyar wai in Meenal ta samu sabon Miji su za’a siyar a mata wasu kayan d’akin.

 

*UMMIEE ZARIA*โœ๐Ÿผ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button